Sashe 2
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Luba ta rakashi har wajen motarsa sai da ya fice daga gidan ta koma ciki. *AISHA* Mace ce da ta koyi hakuri ta karfi da yaji ta koyawa kanta k'au da kai,a duk abinda mijinta Salisu keyi,ta kulle zuciyarta dake neman kamuwa da hawan jinin da mijinta ke k'ok'arin dora mata ta fahimci wani zubin namiji bai cancanci ki kashe kanki a kansa ba wani zubin Kuma basu San kunya ba sau tari takan zauna tayi nadamar sakin jikin da tayi da kawarta da ta Mata mumunan tabon da har ta koma ga Allah batajin zai gogu a zuciyarta a yanzu zaman 'ya'yanta kawai take da Kuma Neman Aljannarta ba dan wai akwai burbushin kaunar mijinta a ranta ba tasan Kuma koman daren dadewa Allah zai mata sakayyar cin amanar da ya mata yanzu suna da shekara Ashirin da biyar da Aure yaranta biyar Ashraf,Afrah,Abubakar Aliyu da Ummi. *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* *BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM* *Page 2* LUBA Mutane da dama suna ganin na aikata abin kunya nayi abin fade naci amana Wanda ni banga aibun abinda nayi ba tunda a musulunce ba haramun na aikata ba so so ne amma san Kai yafi,Ina san Jin dadi a rayuwata Ina san duk abinda nake so a rayuwata ya zama na samu,kina mace Ina mace ba abinda zaki gaya min Ina so naga na Zama mowa a wajen mijina ya zama ba matar data isa ta hada kafada dani Zan iya kashe ko nawa ne,Zan iya zuwa Ko'ina Ina dan na samu cikar burina. Waiwaye Aisha Zuciyata cike take da farinciki dawowar da uban yayana zaiyi. Ya shafe shekara biyar a waje dan ya Karo karatun da yana dawowa zai zama cikakken likita Allah yasan nayi kewarsa Kamar na mutu Ashraf da Afrah ma sai murna suke Abbansu zai dawo,nasan ashraf da wayonsa a lokacin da ya tafi yasani Afrah ce dai take da shekara biyu lokacin daya tafi. Salisu bashida komai a lokacin da mu kayi Aure dan zan iya cewa auren gata aka masa nima da yake a wajen yayana nake Yana kuma da dan rufin asiri Ina gama secondary school ya nemi salis daya fito da a lokacin ba wani aiki yake ba sai wani karamin chemist da yake dashi,da taimakon iyayen sa dai ya turo kudin aure gidanmu aka sa mana Rana wata shidda masu zuwa. A lokacin cikin tsananin farinciki salis ya bugo katin engagement na raba wa kawayena,a lokacin banida aminiya sama da Luba da a lokacin makaranta daya muka yi jinin mu ya hadu da ita sosai ba Wanda baisan kawancen mu ba, har ana mamakin yanda akayi tamu tazo daya da ita dan ni Sam bana San hayaniya ita kuwa akwai zuciya da fada gata masifafiya masifarta yasa lokacin samari ma basu fiye zuwa wajenta ba. A ranar da na bata labarin salis ya kawo kudin aurena mamaki ta ringayi tana mai salis yake dashi da zan aureshi ita har yanzu bata ga kalar Wanda zata aura ba. Dariya na sa mata ina nidai Ina sansa luba ni dama nafiso na auri Wanda bashida komai idan munyi aure mayi arzikin tare. Anan ta hade rai Wai taso muyi aure rana daya bazata so na rigata aure ba cikin dariya nace ta bada himma nan da wata shidda ta samo mijin aure ta tab'e baki tana ita dai taga Kamar nayi gaggawa. A kwana a tashi ba wuya sai gashi mun fara kirga sattikan Aurena,duk wani shiri da Luba muke yi dan itace gaba wajen fito da anko duk da ba wani shiri take da salis ba amma da ta ga dai shi zan aura ta fara sakar masa fuska a haka har aka sha shagalin bikina Luba tayi k'ok'ari sosai dan ba karamin gudunmawa tayi min ba haka ma a gidansu anyi min gudumawa na Kuma ji dadi matuka. Duk da na rigata aure ban canza mata ba, wai dan ganin yanzu ni inada aure hasali kawancen mu kara karfi yayi,dan ba abinda nake b'oye mata game da rayuwar Aurena itama ba abinda take b'oyemin ba ta ma fiye zuwa gidana ba amma idan dai tazo zata wuni a gidana ko da salis ya dawo ma haka zamu hadu mu uku muyi ta hira duk abokanan Salis da suke Santa duk tak'i su a fadarta tafisan ta samu mai rufin asiri sosai,a haka na samu cikin Ashraf har na haihu nan ma sai da ta hidimanta min na ringa addua Allah ya gwada min aurenta nima na rama abinda tamin. Na tafi shekara biyu da Aure na, aka kawo kudin luba murna kamar nayita rawa har salis na tsokanata akan ko a bikinmu banyi murna haka ba,daga yanda naga luba na shiri tana kuma facaka da kudi nasan ta samu irin wanda take so ta aura wato mai kudi,tamkar dai lokacin bikina nima haka na dage muka ringa shirya bikinta,har asusu na ringayi dan inaso naga na mata fiye da abinda tamin. A wajenta nake jin labarin Wanda zata Aura Hamza a wani company Yan China yake aiki Kuma babba ne acan. idan har sunyi Aure zata Masa magana ko zai iya samawa Salis aiki a companynsu. Har a zuciyata naji dadi dan zanso Salis ya ringa aikin da zai na shigo Masa da kudi,dan a chemist din ma ba wani kudi yake samu ba,amma Yana iya k'ok'arinsa wajen kula damu duk da yayana bai barni haka ba yana yawan yimin aike. A cikin irin aiken da yake min na yiwa luba gudunmawa sosai har da zannuwan gadona wajen biyu masu dan tsada da ban taba amfani dasu ba. Gidan Luba yayi kyau sosai Iyayenta Kuma sunyi k'ok'ari wajen yi mata jere Luba an samu abinda ake so sai falli take,har tana cemin ita dai taga nayi gaggawa da ace banyi gaggawa ba da sai na samu mijin dayafi salis,nidai inasan salis Kamar yanda yake kaunata duk da gidan haya muke ban damu ba dan indai da rai da rabo Yana Kuma iya k'ok'arinsa wajen kyautata min. A haka muka Sha bikin luba, kawancen mu ya Kara k'arfi fiye da baya. Watan ta hud'u da Aure watarana tazo gidana naganta a firgice daga yanda na ganta nasan ba kalau ba Salis ma ko fita baiyi ba. Tana zama ta rushe da kuka hankalina ya tashi anan na hau tambayarta mai ya faru dak'yar ta tsagaita Kukan da take take labarta min wai ta gano Hamza karya yayi mata Ashe mai gadi ne da kudin ajiya duk yayi facaka ya aureta yanzu haka jiya Yan sanda suka zo suka tafi dashi akan Mai company ya dage sai ya biyashi duk kudinsa ta Kara da "wlh ban taba tunanin Hamza makaryaci bane Aisha mai gadi fa kinsan kuwa gidan ma ashe hayane ba nasa bane" Nidai sallati kawai na ringa yi ita kuwa ta cigaba da rusa kuka dak'yar na bata baki tayi shiru ta ringa rantsuwar sai Hamza ya saketa ita bazata zauna da mai gadi ba,a haka Salis ya fito ya same mu ganin yanda mukayi cirko cirko yasa ya hau tambayar mu mai ke faruwa Shiru nayi dan Ina tunanin kamar sirrinta ne bai dace na fada masa ba,ita kuwa ganin banida niyyar magana yasa ta hau bashi labarin duk abinda ya faru,Salis kuwa ya hau sallati yana Yanzu Hamza na kulle shine tazo ta zauna ai Kamata yayi asan yanda zaayi a fito dashi a takaice a ranar salis bai fita shago ba haka aka ringa cuku cukun yanda za'a fito da Hamza dan Salis har wajen mai gidan sa yaje dak'yar dak'yar ya yarda akan a saki Hamza zai nemi rabin kudin ya biya shi inyaso ya cigaba da biya a hankali. Duk salis ke bamu labarin yanda sukayi dan luba na gidana tace ita bazata ma koma masa ba so take ya bata takardar ta ta tafi gidansu kamar ba mijinta ba ta ringa auna masa zagi. Luba sai da ta samu sati guda a gidana wulakanci kuwa haka ta ringa yiwa Hamza Kamar ba mijinta ba,sai da Salis ya samu Iyayenta suka saka baki ta yarda zata koma gidansu hamzan kafin ya samu wajen zama. Ni tausayinta ma na koma ji dan ta saka damuwa a ranta sosai gashi tana d'auke da ciki. Ba'a kwana biyu bata zo gidana ba,idan tazo haka zatayi ta mita tana tsinewa Hamza akan ya cuceta a irin wanan halin Nima na samu cikin a lokacin Ashraf ya tafi shekara uku. Nidai zan iya cewa banida matsala komai dan Asirina kam a rufe yake dan banida wani matsala a gidan aurena daidai gwargwado salis na kyauta ta min. Cikina wata biyar Luba ta haihu Sanin halin da suke ciki yasa na zage sosai wajen hidimanta mata Salis ma baa barshi a baya ba duk da bashida kudi. Nidai nasiha da shawara ke rabani da luba da ta balain raina Hamza ni nasan da baya Santa da tuni ya saketa dan Abubuwan da ya mata ma duk sai da ta raina burinta ma kawai ta kashe auren. A haka nima Allah ya saukeni lafiya na haifi Afrah a haihuwan nan Salis ya min hidima ba kad'an ba,tunda na haihu Luba bata tab'a d'auke kafarta daga gidana ba tun safe idan tazo sai dare take tafiya,kayan fitar sunan da salis ya siyamin take ta juyawa a hannunta tana "Kinsan kuwa tsadar atamfar nan Ina Salis ya samu kudi haka"? "Kice atamfar nada tsada wai Ashe tunda nasamu ciki ya Shiga adashe shine fa Ina haihuwa ya karbi Adashen ni Ina nasan ma zanin nada tsada" "Aikuwa da tsada yayi k'ok'ari gaskiya ni Ina naga arzikin Rabin atamfar nan ma wlh Hamza ya cuceni gashi yak'i sakina" Zama nayi a gefenta Ina "kiyi hakuri Luba mai nema Yana tare da samu ai da ace baya nema sai ki fida rai amma tunda har Yana nema watarana za'a dace insha Allahu Kuma zakiji dadi tunda Yana kaunarki" "Hmmm kinsan ko Napkin baya iya siyawa Sultan wlh ba irin rayuwar nan na tsarawa kaina ba" Kwalla ya zubo mata ta share a daidai lokacin da Salis ya daga labule suka gaisa daga bakin k'ofa ya mikomin ledar daya shigo dashi ya fita. Da zan ajiye ledar sai Kuma na bud'e ledar naga Kayan jarirai