Sashe 30
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawai ta kafe sai tabi su Aunty hassana gida wai zata dawo" Salis yaci abincin kawai ne amma hankalinsa a tashe yake komawa gidan da muhasim tayi ya Kara tabbatar masa da akwai abinda yayi wa muhasim din kila baa hayyacinsa ba abinda zai iya tunawa kawai yasan yacemin tazo ya Kuma kankame mutum baisani ba lubar ce ko ita sai ya cije lebbensa Yana tsinewa Luba albarka yarinya da take tamkar Yar cikin sa ta jawo masa ya zubar da mutuncinsa a wajenta. Washegari haka ya shirya ya tafi office zuciyarsa cike da damuwa Aisha ma ta d'auka duk zazzabin da yace yana yi ne. Sosai ya shirya irin rashin mutunci da zai yiwa Luba idan tazo office dinsa dan yasan sai tazo din. Sai dai har aka kwana biyu bai ga kafar Luba a office dinsa ba. Sati biyu a tsakani ganin muhasim bata dawo gidan ba ga Khadija yayarta na nan yasa ya shirya ya nufi gidan su Yayan Aisha sai yake zargin Kamar akwai abinda yayi wa muhasim din bai sani ba wanan wane irin zubar da mutuncine. Kafin ya isa gidan ya dan yi siyayyar da ya saba idan zaije. Gidan ba bakon sa bane ba hakane yasa ya Shiga gidan kai tsaye da sallama a bakinsa. Hada ido yayi da muhasim dake wanke wanke a tsakar gidan tayi daurin kirji. Yanda tayi saurin sunkuyar da kai yasa Salisu yaji kirjinsa sake bugawa kasa kasa yaji tana "uncle sannu da zuwa" Bai amsa ba ya ciki yana "Ina Aunty take"? "Taje suna" "Abdulrahman fa"? "Sunje ball" "Ke kadai ce a gida kenan" "Eee " Duk maganar da suke bata dago kanta ba wai kunyarsa take ji yarinyar da tana ganinsa da gudu take zuwa ta rungume shi tamkar ya ya d'auketa Luba ta jawo mai zubar da mutuncinsa a wajenta wanan wane irin abin kunya ne. Cikin palon ya Shiga ya zauna ba dadewa sai gashi ta shigo Tana shigowa yaganta sanye da hijabi idan a da ne ma ko a jikinta da haka zata zo ta hau masa surutu duk da wani zubin miskila ce wani zubin magana bata dameta ba Sai da ta ajiye masa ruwa ganin tana k'ok'arin yin waje yasa ya tsayar da ita yana zo ki zauna tambayarki zanyi" Kanta a sunkuye ta samu gu ta zauna "Mai yasa Kika dawo gida"? "Ba komai" "Kamar ya ba komai haka kawai zaki dawo bayan hutunku bai Kare ba"? "Ba komai uncle na dawo ne kawai" "Muhasim" Naam Ruwan nan da kika kawo min na sha waye ya baki ki kawo min"? "Aunty Luba ce ta d'auko ta bani akan na kawo ma" Salis shiru ya dan yi na Yan mintuna Yana Jin wani sabon b'acin rai zarginsa ya tabbata Luba magani ta sa mai a ruwa da a yanzu ranar Aisha a dakinsa ta kwana da duk haka bata faru ba Kamar an fusgo maganar daga bakinsa yace "Na miki wani abune muhasim"? Sai ta dago ta kalleshi ta Kara maida kanta kasa Yana kallon yanda take ta murza hannunta ko batayi magana ba zarginsa ya tabbata akan ya mata wani abu Inda yake godewa Allah da baiyi mai gabadaya ba. Bai ma san yanda akayi ya nemi luban ba Sai da suka dau tsawon mintuna a haka Salis kunyar ce ta hana shi Kara magana tamkar yanda Muhasim ta tsinci kanta itama da Jin kunyarsa sabida har yanzu ta kasa manta yanda ya mata ta Kuma yarda Aljanu ne dashi amma tana tsoron ta cigaba da zama ya Kara Mata hakan dan har ga Allah tsoronsa ma take ji. "Kiyi hakuri bansan na miki wani abu ba kinji ki hakan bazata sake faruwa ba gobe ki hada kayanki ki koma kinji" Sai ta gyada masa Kai Salis ya mike Yana ta gayawa Aunty mamy yazo ya gaishe su basa Nan. A takaice yanda Muhasim ta sake komawa gidan kenan tun tana dari dari har ta dawo ta saki jikinta har suka kamalla hutun su Suka koma makaranta da yake duk makaranta daya ma suke zuwa dasu Afrah Salis shi yake biya musu. LUBA. Tana sane ta d'auke kafarta daga zuwa wajen Salis burinta taga ta samu ciki kafin ta neme shi yanda bashida yanda zaiyi a dolensa ya aureta. Sai dai burin nata bai cika ba da wata ya kama taga period dinta kamar tayi kuka. A yanzu Kuma batasan ta hanyar da zata Salis ya yarda ya aureta ba tasan yanzu Kara tsanarta zaiyi tunda tasan dole ya gane cewar magani aka sa Masa a ruwa. Dabarar da ya fado mata akan ta gwada saarta na zuwa office dinsa taga ko Allah zai dorata akansa yasa ta shirya ta nufi office din nasa koda taje bata same shi a office dinsa ba haka ta zauna zaman jiransa har ya dawo daga kallon da yake mata tasan rashin mutunci da ya Saba Mata zai mata. Bata bari yayi magana ba ta tare shi da "Ina d'auke da juna biyu" "Idan kina d'auke da juna biyu Ina ruwana,"? "Ai cikin naka ne" "Ok a lokacin da Kika saka min magani a ruwa na Sha na miki cikin ko to ba damuwa idan kin haihu ki kawomin abinda kika Haifa". Naceba Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195 Call:08064532391 Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida tested nd trusted Natural /organic *WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN* *+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA* *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *PAGE 17* Luba sakin baki tayi tana kallonsa Salis kuwa fuska a had'e ya nuna mata k'ofar waje Yana "Ki tashi ki bar min office Daga yau Kar ki sake zuwa office dina duk abinan da kikeyi wlh Kara tsanarki nake bazan tab'a aurenki ba Koda ba Mata a duniya ace ke kadai kika rage wlh bazan tab'a iya aurenki ba dan ke din munafika ce mai fuska biyu idan har Zaki iya cin Amanar Aisha ta hanyar saka min magani a ruwa wai dan na kwanta dake nasan zaki ma iya kasheta naso tasan wacce ke sai dai bata yarda na fada mata wacce ke duk iya k'ok'arin ta na ta kareki ne batasan ke din shaidaniya bace yanzu banda Allah ya rufamin asiri da kin cuceni kin sa na aikata abin kunya ta hanyar neman muhasim Luba kifita a harkata idan ba haka ba wlh zan baki mamaki a ranar da zan ganki a gidana zan tona miki asiri a gaban Aisha tashi kifita ki daina mafarki zan aureki wlh ba abinda zanyi dake duk ranar da kika Kuma zuwa office dina sai na saka security sun miki duka gidana ma ki rage zuwa dan banasan ganin wanan mumunan fuskar Taki" Luba na k'ok'arin Magana yayi kanta a fusace dan wlh wani irin tsanarta yake ji har Yana Jin Kamar ya rabata da ranta. Yanda ya harzuko yasa Luba yin waje da gudun. Tana tafe tana sharar kwalla wahala kawai take Sha bata ga alamar Salisu zai tab'a aurenta ko ya saurareta ba Koda taje gida ji take Kamar ma ta hakura ta nemi wani mai kudin amma idan ta tuna irin d'aular da Aisha ke ciki da yanda kowa ke san rabar Aishan sabida tana da abin duniya sai taji ina bazata tab'a iya hakura ba kodan wulakancin Nan da Salis yake mata zata san duk yanda zatayi ta Aureshi hanyar da zata bi din ne bata sani ba Asabe kawar da ta hadu da ita a biki ce ta fado mata itama bazawara ce idonta a bud'e yake tamkar ita. Da yamma ta sake shiryawa ta nufi gidansu Asaben tana zuwa ta tadata a k'ofar gida tana zance da wani kana ganinsa ma kasan mai kudine. Shigar ma da Asabe take yi na kece raini ne da alama itama masu kudin sun tsaya Mata. Sai da ta sallami saurayinta suka shiga gidan a tare sai da suka ci abinci Luba ta fada mata abinda ke tafe da ita da shawarar ta da take nema ko akwai hanyar da zata iya taimaka mata. Budar bakin Asaben sai cewa tayi "Mai zai hana muje ki asirce dan banza ya aureki Ina da wani mallami ya iya aiki sosai" "Bana san harkar mallamai dinan Asabe yanzu idan na asirce shi ya aureni ai dole watarana asirin zai karye" "Kafin asirin ya karye ba kinsamu abinda kika Samu ba balle sabunta aiki kawai za'ayi tayi" "Banasan asirin Asabe idan akwai wani hanya da kike ganin zan bi ya aureni ya Kuma daidaita ni da Aisha ki fadamin kawai wlh burina naga ya aureni" "Ai daga labarin da kika bani ba wata hanya da zaki bi sama da ki asirce shi ba ke kika gama bani labarin irin tsanar da ya miki ba" "Tom shikenan mu gwada zuwa din mu ga idan mai yuwa ne" Koda suka je luba ce duk ta fada masa abinda take so na auren Alhaji Salis da take so tayi,tana Kuma so ta mallakeshi sai yanda tayi dashi idan Aisha ma zata bata ciwon kai ko ta kawo Mata matsala a rabata da Salisun ta zauna dashi ita kadai. Sai da mallamin ya gama dube dubensa yace Mata aikin da zai mata sai