← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 71

Sashe 67

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dama duk ita ta shirya abinda ya faru ba har tasan komai sabida ta samu ya aureta,dan haka Ina rokon kotu da ta taimaka tabi wa muhasim hakkinta Luba ita tayi silar da aka yiwa muhasim fyade ta Kuma karkata mata wuya sabida Kar ta samu bakin da zata Fadi gaskiyar abinda ya faru muna rokon kotu da ta taimaka wajen tilasta mata ta fada mana abinda tayi wa muhasim ta karkata Mata wuya" Alkali sai da ya gama rubuce rubuce ya tambayi Luba ko tana da lauyan da zai kareta ta girgiza kai akan Bata da lauya. Alkalin ya Kara rubuce rubuce ya dago yayi bayani akan zaa daga karar zuwa sati uku masu zuwa sabida itama wacce ake kara ta samo lauyanta Ashraf kuwa dama haka yafiso dan a zaman da za'ayi na biyu zai samo shaidar da dole asirin Luba ya tonu. Aisha kuwa kuka ta ringa yi wiwi tana nadamar rabuwar da batayi da Luba ba a lokacin da Salis ya dage mata akan ya rabu da ita,sai a yanzu ta tuna daga lokacin da Salis yaci abincin Luba ya canja ashe duk abinan da ya faru Luba ce ta haddasa komai ashe duk abinan daya faru tafi kowa laifi tunda da ace ta rabu da Luba da bata samu damar da zatayi wa Salis abinda tayi har ya nemi muhasim ba,ta riga kowa barin kotun dan kunyar ma hada ido take da salis dan sai take ganin kamar itace ma ta jefa shi a cikin wanan matsalar. Salis kuwa bai iya jan motar bama sai ASHRAF ne yaja motar dan bai tab'a sanin Ashe Luba ce tayi girkin dayaci har ya zama mabukaci ba,sai a yanzu ya Kara gane Luba ce ta jefa shi a wanan halin har ya nemi muhasim. Har suka isa gida bai iya ce komai ba sai da yazo sauka ya juya ya kalli ASHRAF yana "Mahaifiyar ku itace silar da ta jefani a cikin wanan masifar wlh Aisha bata min adalci ba,daace ta rabu da Luba da kila duk ban tsinci kaina a cikin wanan halin ba" "Abba godiya zaka yiwa Allah da gaskiya ta fara halinta nasan a yanzu hajiya umma dasu Yaya mustapha zasu gane cewar ba da gangan kayiwa muhasim fyade ba" Salis bai ce komai ba ya fito daga motar yayi cikin gidan dan ji yayi kansa na masa ciwo. Aisha kuwa Koda suka isa gida Yaya mustapha fada ya rufeta dashi yana duk abinan ma daya Faru ita ta jawo tafi kowa laifi dan da ace tayiwa mijinta biyayya ta rabu da luba da duk haka bata faru ba. Lauyan gwamnati aka samowa luba da Luba ta tsara masa karya gabad'aya ta maida laifin Kan Salis ta dage akan shi ya karkata wa muhasim baki ita batasan komai akai ba ASHRAF so kawai yake ya wanke mahaifinsa sabida shi lauya ne Luba ta ringa kuka akan ya taimaka mata barrister kabeer ya Mata alkawari akan zai taimaka mata. Ashraf shima sosai ya dage wajen Kara samo shaidu kafin ranar da zaa koma kotu. A ranar kuwa da zaa cigaba da Sharia kotun tafi koyaushe cika Alhaji Salis na daga gaba Aisha ma gaba ta zauna wanan karon har da muhasim Suka zo da aka turo a keke" Sai da akayi shariar mutane biyu kafin a kira shariarsu. Luba ta fito ta tsaya a wajen da ake tsayawa zuciyarta tana Jin kwarin gwiwa zatayi nassara har wani murmushi ta ringa sakarwa Aisha da Salis da ba abinda take hangowa a idonsa sai wuta,tasan da zaa bashi dama zai iya harbeta har lahira. Duk tambayoyin da Ashraf ya mata haka barrister kabeer ya ringa katse shi ya na kawo nasa hujojjin da "Ya mai girma mai Sharia lauyan Mai kara Yana so yayi iya k'ok'arinsa ne dan yaga ya wanke mahaifinsa ne amma babu tantama shi yayiwa yarinya fyade ya karkata mata baki sabida Kar ta samu bakin da zata tona masa asiri, wacce ake kara tasan sirrinsa ne sabida yawan sintirin da takeyi a office dinsa dan haka Ina rokon kotu da ta yiwa wacce ake kara adalci ta tilasta wa Alhaji Salis ya fadawa kotu gaskiyar abinda yayiwa muhasim ya karkata mata baki ngd ya mai girma mai Sharia Ya koma ya zauna Ashraf ya mik'e tsaye fuskarsa d'auke da murmushi Yana "Ya mai girma mai Sharia inaso kotu ta bani dama na gabatar da shaidar da kotu zata gamsu da cewa Wacce ake kara ita take da hannu a cikin abinda ya samu muhasim" "Kotu ta baka dama" Luba murmushi ta saki dan tasan ba wani shaidan da ASHRAF yake dashi. Bakin k'ofa taringa kallo Dan taga shaidar da Ashraf yace Yana dashi. Shigowar Asabe da mijinta Yusuf da ya ruko hannunta yasa Luba taja da baya kirjinta yayi wani irin bugawa Kamar ya fado taja da baya ta nuna Asabe da hannu tana "A!!S!!A!!B!!E ba kin mutu ba"?.......... Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b Mai bukata should Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Team glow *WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN* *+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA* *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *PAGE 37* "Ban mutu ba Luba Bakiso ganina ba ko?kin d'auka kin kin kasheni?toh ban mutu ba gani yau a kotu duk zan tona sirrinki da ba Wanda yasani sai ni a tunaninki tunda kin kasheni asirinki ya rufu ko? Toh gani da raina yau zan tona miki asiri asan ke wacece" Ashraf murmushi ya saki ya nuna mata wajen da zata tsaya yusuf ya saki hannunta ta shige wajen ta tsaya tana kallon Luba da ke wani irin karkarwa har lokacin nuna Asabe take da hannu Ashraf kuwa ya juya wajen alkali Yana "ya mai girma mai Sharia inaso kotu ta bani dama na yiwa Asabe tambayoyin kafin na mata tambayoyin inaso kotu tasan cewa ita wanan baiwar Allah da zata bada shaida akan Luba ita keda hannu a duk abinda ya samu muhasim kawarta ce Aminiyarta da tasan komai akan ta ko nace tare suke yin komai,daga lokacin da Suka fara samun sab'ani Asabe ta nuna zata tona Mata asiri shine ta caka mata wuka ta gudu, a tunaninta ta kasheta shiyasa da ta shigo ta mata tambayar dama bata mutu ba,?ko a yanzu zamu iya ganin yanayin jikin Asaben dak'yar ta samu tazo kotun dan har yanzu bata warke ba mijinta yazo mana da camera dake d'auke da yanda ta cakawa Asabe wukar ta tattara komai ta gudu iya wanan kawai ya isa kotu ta gane Luba ta wuce duk yanda ake tunani idan har zata iya kashe kawarta Aminiyarta toh ba abinda bazata iya yi ba amma inaso mu ji komai daga bakin Asaben dan ita zata warware mana komai" "Kotu ta baka dama kayi Mata tambayoyin" Alkali yace Yana gyara zaman gilashin fuskarsa dan a yanzu case din ya dau hankalinsa tamkar yanda Kowa na kotun ya zaku Asabe ta fara bada labari ciki kuwa har da Salis da Aisha da suke ji kamar suje kusa da wajen da Asabe ke tsaye "Nagode ya mai girma mai sharia" Sai da Asabe tayi rantsuwar zata Fadi gaskiya kafin Ashraf ya nufi wajen da Asabe ke tsaye Yace "Mallama Asabe ko zaki iya bamu takaitacen labarin yanda kuka fara kawance da Luba ya akayi kika san sirrikanta da ba kowa ya sani ba" "Luba dai kawata ce na hadu da ita a wani biki a lokacin auren ta ya mutu Nima a lokacin nawa auren ya mutu ganin dukan mu zawara ne yasa tamu tazo daya da ita, dan yanda nake son ado da kwalliya haka take so itama haka ma yanda nake so na samu miji mai kudi na aura dan na huta itama haka ra'ayinta. A wajenta nake yawan Jin labarin kawarta Aisha yanda take auren miji mai kudi,har take bani labarin Rabin kayan da take sakawa masu tsada na Aisha ne, ai Aishan sam bata dace da auren miji mai kudi ba dan bata da wayo ko kad'an har take fadamin yanda take rabata da abubuwa ta karfi da yaji Kuma ko nawa takeso idan har kudi ne zata d'auko ta bata,a haka tana ta kwadayin Auren mai kudi duk Kuma masu zuwa neman aurenta sai tace bataso tafison ta samu mai kudi irin mijin Aisha kawarta har take bani labarin haduwar gidan da yake ginawa da tsaruwarsa, nima nasan gidan a lokacin bansan na mijin Aisha bane ba, ita dai burinta a lokacin bataso Aisha tafita da komai, tafiso taga ma tafi Aisha ganin bata samu irin dai mijin Aishan ba rana tsaka tazo ta sameni akan ita a yanzu mijin ma Aishan takeso dan batajin zata samu miji mai kudi irinsa nayi matukar mamakin yanda take da Aisha ace zata iya cin Amanar ta amma ban nuna mata komai ba nace mata ba haramun bane zata iya aurensa,anan take fadamin irin wulakancin da yake mata har yanda ta samu magani ta saka Masa a ruwa dan ta samu yayi amfani da ita ko Allah zai saka ta samu ciki ma ya aureta sai dai a madadin ma ta samu cikar burinta dataje office dinsa duka ta sha a hannunsa ita bata san ya zata yi ta shawo kansa ba tace ko da yanda zan iya taimaka mata ta samu ya aureta" Shiru Asabe tayi ta saci kallon wajen da yusuf ke zaune dan fadar ta taimakawa Luba zuwa wajen mallami
Chapter 67 · 0% Book details