Sashe 51
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Salis rawar da jikinsa keyi gumi na karyo masa yasa shi zama a gefen gadon ya dafe kansa har Ashraf ya idda maganarsa yaji ya kasa ma bud'e baki yayi magana taya zai kalli fuskar dansa ya fada masa hanyar da yake bi kudade ke shigo masa,a baya idonsa ya rufe da san ya zama hamshakin mai kudi hakane yasa da Zainab ta nuna masa hanyar bai yi wani dogon tunani ba ya amsa tayin dan kudadene ke shigo musu da yawa zainab kuwa Allah kadai yasan kadarorinta takunsa da ya iya ne yasa ba mai tab'a zarginsa. A shekarar nan ya fara tunanin barin harkar dan akaran kansa yasan watarana asirinsu zai iya tonuwa. Muryar Ashraf daya zauna gefensa ya katse masa tunanin da ya ke ya dago yana kallonsa da jajjayen idon sa da suka kada suka yi ja har lokacin wayarsa sai ringing yake da haka Ke Kara daga masa hankali "Abba dan Allah ka fada min menene b'oyayyen sirrin ka da kasan idan har ya tonu zaka shiga matsala muma mu Shiga tashin hankali"? "Ka tayani da Addu'a kawai Ashraf Allah ya fiddani fada ma masifar da na jefa kaina ba abinda zai kareka dashi sama da tashin hankali tashi ka tafi inasan na kadaice na samu nutsuwa" "Abba dan Allah"!!! "Ashraf ka fita nace ko"? Ashraf mik'ewa yayi a hankali ya fice daga d'akin yana jin hankalinsa na Kara tashi ba abinda yake darsuwa a ransa sama da mahaifinsa kila Dan yankan kai ne ko Kuma kidnapping yakeyi ya zama dole ya sa mai ido ya Kuma fara bin didiginsa ko zai gano wani abu" Ashraf na fita ya d'auko wayarsa dake yashe a kasa,sai yaji tashin hankalin daya Shiga a baya nafila ne akan wanan daya tunkaro shi. Kamar uje jira yake ya d'auki wayar kiransa ya kara shigowa, baya so ya daga yaji wani sabon tashin hankali kila duk an kamo su,bai san sanda ya mik'e tsaye ya fara safa da marwa a d'akin ba tunanin daya dar su a zuciyarsa yasa shi nemo lambar da yayi Saving da L worker dan duk wayanda suke harkar da worker ya musu saving, har Kiran ya kusa tsinkewa kafin yaji ta d'auki wayar da "Alhajin Allah" "Jidda kinji labarin an Kama John a hanya zaizo wajenki" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun wlh banji labari ba a Ina aka kamasu?ya akayi aka kamasu" "Dazun nan uje ya kirani yake fada min yanzu abinda nake so da ke ki sallami yaran nan gabad'aya ki basu kudi mai dan yawa ki cire layinki ki Yar dashi idan da hali ma ki bar kasar duk abinda za'ayi kome za'ayi dan Allah karki Kira Sunana ki kira sunansu John ki kafe akan su kika sani" "Ni fata kake a kamani ne Alhaji taya zan bari ma a kamani ai insha Allahu idan har an rik'e alkawari bazasu tona ba nidai bari na fara Shiri" Kit yaji ta Yanke wayar Zazzabi da rawar da jikinsa keyi yasa shi koma Kan gado ya kwanta ya lumshe ido Yana tuno ranar da Zainab ta fara gabatar masa da harkar da Rabin kudinsa ta nan yake samu,sai yaji dama zai iya maida hannun agogo baya da sam bai amshi tayin da ta masa ba. "Ana samun mahaukatan kudi am telling you karka tsaya wani dogon tunani Salis,larabawan nan basuda hankali in ponds suke biya" "Zainab wanan abin is very risk wlh har yanzu jikina rawa yake da abinda nagani bazan iya ba gaskiya wane irin rayuwa ne wanan sai kace ta dabobbi" "Hahah nima da farko haka na ringa cewa amma bashi zaka duba ba kudin kasan mai za'ayi ni zan baka kudaden da zai fasa ma kwakwalwa Wanda duk ta haka na same su nifa badan Ina kaunarka ba wlh bazan koya ma harkar nan ba idan kana ganin dan albashin wata daya da bai Kai dubu dari Ba zai isheka kayi irin rayuwar da kake so to Shikenan sai na rabu da kai Ta mik'e ta jawo wani akwatinta sai data ta zura hannunta ta fara fito da bandir din dalolli Salis ya gwalo ido Yana kallonta sai da ta ajiye guda goma ta rufe akwatin tana "wanan ni na baka kyautarsa a cikin irin kudin da nake samu idan har zan iya baka irin wannan kudin kasan ba kananan kudi ake samu ba ka je ka sake tunani" A cikin irin kudin ya turo gida aka siya masa katon fili ya ringa yo aike ana masa gini. Daga lokacin ya tsunduma kansa a cikin wanan harka a yanzu zainab din ma baya jin labarinta duk ta Inda zai sameta babu,baisani ba ko an kamata ko baa Kamata ba yasan dai ta samu wani bature ta aura shekaru goma da suka wuce. Kiran dake shigowa wayarsa ya Kara katse masa tunanin da ya tafi ganin mai Kiran yasa yaji wani sanyi na ratsa zuciyarsa yasan tana kaunarsa fushi yasa ta bar gidan,a yanzu kuma mai haddasa masa fitina ta hana shi zaman lafiya ta bar gidan a yanzu idan Allah yasa asirinsa ya rufu a yanzu ne zai samu nutsuwar da yake so ya samu yasan tunda har Yaya mustapha ya fahimce shi zai tilastawa Aisha itama ta dawo gidansa. Koda ya d'auka a madadin yaji muryar Aneesa muryar Hajiya Binta yaji ta ratso wayar da sallama. Sai yaji ya kasa amsa sallamar Yana tsoron Kira tayi akan ya saki Aneesa ba dai Aneesa tana nufin ta shirya rabuwa dashi ba,sunansa da ta kira da "Salisu baka jina ne"? Can kasan murya yace "Ina wuni hajiya" "Yanzu haka na baka 'yata wata bakwai kawai yarinya duk ta fige ta lalace Ashe dama zuwa kayi ka hadeta cikin matan ka suke gana Mata azaba alkawarin daka d'aukar mana kenan"? Salis bai iya magana ba dan bai san mai zai ce ba tunda har Aneesa ta iya fadawa Hajiya Binta karya da gaskiya yasan ta hakura da auren ne so take kawai su rabu tunda ya tafi watani bai bata hakkin ta ba Wanda har hakan yasa ta d'auko cucumber tana so ta gamsar da kanta. "Ka Aiko min da takardar ta dan ta gama aurenka na Dade Ina hango Mata irin wanan ranar ta kafe ta dage ai ga irinta nan da taji wuya ta dawo Salisu ka aiko min da takardar yata nace kaji ko baka ji ba"? "Hajiya kuyi hakuri karku yanke hukunci cikin b'acin rai inasan Aneesa itama tana sona" "Ai bani zan raba ku ba ita da kan ta ta nemi na kiraka akan ka saketa ka saketa ta je ta nemi daidai saanta ta aura Kai Kuma kaje kaji da matan ka na baka nan da kwana uku ka Aiko min da takardar ta idan baka aiko ba idan mun had'u a kotu sai ka bata takardar ta" Kafin yayi magana ta Yanke wayar,ya ajiye wayar a hankali yana "Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha" Kansa kamar ya fashe sabida ciwo ya rasa ma tunanin da zai yi bai san da wan zai ji ba da asirinsa dake neman tonuwa da barin Aisha gidansa ko da sakin Aneesa ta nema a wajensa. Mik'ewa yayi daga kwancen da yake dan a yanda yake jinsa dole sai ya sha maganin bacci a bakin k'ofa suka yi karo da Hindatu taci ado sai walwali take hannunta d'auke da faranti. "Alhaji tun dazu Ina jiran ka fito naji shiru shiyasa nace bari na biyo ka da abinci ka samu kaci ko kad'an ne" Matsar da ita yayi gefe ya nufi dakinsa dan ko magana a yanzu Kuma baya so yayi burinsa kawai ya sha maganin da zai mantar dashi damuwar da ya tsinci kansa Yana bukatar nutsuwa kafin yasan abinda ya dace yayi babban burinsa yanzu asirinsa ya rufu gani yake komai kuma zai zo masa da sauki. Koda ya Shiga d'akin drawer dinsa ya jawo ya deb'o magangunan ya watsa a bakinsa ya d'auki ruwa ya kora yana k'ok'arin kwanciya Hindatu da ta biyo shi har d'akin tana k'ok'arin zuba abinci ta dakatar da zuba abincin tana "Alhaji dan Allah ka sasautawa kan ka Wanan damuwar da ka sa kanka ka kwantar da hankalin ka ni nasan idan aka kwana biyu a lokacin zuciyar ta tayi sanyi ai bawa bai isa ya wuce kaddararsa ba hakuri zata yi nima so nake gobe naje na bata baki,ai yanzu matsalar ka ta kau tunda har ka rabu da luba dama itace take haddasa komai" "Hindatu dan Allah kifita so nake nayi bacci na samu nutsuwa idan na tashi zanci abincin" "Bari na maka tausa sai kaji dadin baccin" "Hindatu dan Allah ki fita nace" Hindatu harara ta watsa masa tayi waje tana "Kamar ni na aike shi yaje yayi wa Yar mutane fyade" Taja tsaki tare da rufo masa k'ofar. Aisha "Yaya kai yanzu duk ka yarda da maganar da ya fada maka wlh Allah karya yake duk yanda zai Kare kansa kawai yake nema,idan har da gaske Luba na bibiyar sa mai yasa bai tab'a fada min tana bibiyarsa ba" "Idan ya fada miki tana bibiyarsa ai ba yarda zaki yi ba sau nawa yana ce miki ki rabu da ita ko ni nan sau nawa na miki fada akan ki rabu da ita ba matuniyar arziki bace daga lokacin da mamy tace min tana zuwa aron sababin kayan ki,taya duk zai zauna ya tsaramin wanan zancen idan ba'ayi haka ba,ke naga alama bakida zurfin tunani da wayo a yanzu ma baki yarda ta saka mishi magani a ruwa ba a ranar da kuka tare"? "Yaya duk rashin hankalina dai da yace min ta tab'a cewa tana san shi wlh dole na rabu da ita,ni a lokacin cemin kawai yake na rabu da ita baya santa bai tab'a fada min dalilinsa ba,ni Kuma a lokacin abinda yasa ban rabu da ita ba sabida ba abinda tamin, bansan ta yanda lokaci guda zance mata mu rabu ba,ni yanzu duk ba wanan ba ba maganar Luba na bibiyarsa da yanda ya aureta muke ba ya aka yi ya karkatawa muhasim wuya"? "Daga labarin daya bani bashi ya karkata mata wuya ba dan har Qur'ani naga Yana k'ok'arin daukowa akan zai dafa na hana shi,a duk zargin da muke yanzu Luba tana da