← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 71

Sashe 20

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuciyarta sai taji tana mugun kishin ma Alhaji Salis ya rabi sauran matan nasa ta d'auka tunda manya ne matan nasa ba wani rabon kwana da zaayi. Bata karyawa da wuri amma haka Alhaji Salis yasa taci abinci ta canja kayan jikinta zuwa doguwar riga Alhaji Salis yayi gaba tana binsa abaya dan so yake ya hadata da Aisha da Hindatu tunda Luba kadai ce tasanta. Kafin ya iso bangarensu yaji muryar Luba na tashi "Har ni Zaki sakawa fiya fiya a shayi Hindatu wlh sai nayi karar ki mai na Miki da kike so ki kasheni jiya ko bacci banyi ba sabida ciwon ciki wai ahaka ma ban sha ba da na Sha fa nasan da yanzu an fara shirye shiryen kaini" Hindatu na zaune ko daga kanta batayi ta kalleta ba bakin ciki fal zuciyarta sai tara iska a bakinta take tana sacewa dan dauriya kawai take bata tanka Luba ba wanan doka da Alhaji Salis yasa mata na daina biyewa Luba ya cutar da ita. Alhaji Salis farinciki da ya fito dashi yaji ya kau ya hade ransa a daidai lokacin da Aneesa ta labe a bayansa dan dagaske ta yarda tana da tabin hankali. Ya san yanzu idan yayiwa Luba magana dizga shi zata yi a gaban Aneesa ta d'auka bai isa da gidansa ba jawo hannun Aneesa yayi daga bayansa ya rike hannunta tare da nufar wajen da Hindatu ke zaune sai da ya zauna Aneesa itama ta zauna kamar zata shige jikinsa sabida tsoron Luba da ta zubo mata ido tana mata mugun kallo. Alhaji Salis kuwa yacewa Hindatu "Ga Aneesa nan kanwar ki Anjima za'a dawo da kayan ta wancan d'akin,ko ban fada ba kingan ta kinsan yarinya ce baza'a samu matsala da ita ba dafatan zaki d'auketa tamkar kanwarki "Hmmm" Kawai Hindatu tace tare da hararar Aneesa kasa kasa har ga Allah wani irin kishi ne ya rufeta da ta tsalleliyar yarinya mai jini a jiki da Alhaji Salis ya auro musu "Aneesa ga Auntynki ku gaisa" Aneesa ta sauko daga kujera tana "Aunty Ina kwana" "Lafiya" Hindatu tace tare da mik'ewa ta bar palon Ta kalli Luba da take balain tsoro tana "Aunty Ina kwana" "Yana gidanku kwanan ni zaki zo kina wani susunkuyar da kai bayan abinda nasani kema kinsani toh wlh bakizo gidanan ki huta ba wahala da bauta kawai kika zo sabida shegen kwadayi iyayenki Suka d'auko ki Suka bawa tsoho" Alhaji Salis rada yayi wa Aneesa a kunne akan haukarta ne ya motsa Kar ta kulata ya rike hannunta suka Mike tare da nufar d'akin Aisha Luba kuwa ta cigaba da masifa Da sallama suka shiga d'akin Aisha. Aisha da ke Shirin yafa mayafi akanta ta amsa dan tana Shirin tafiya wajen Aunty mamy zasu je wani gaisuwar mutuwa,ganin Alhaji Salis da Aneesa yasa ta saki fuskarta. Aneesa kuwa ta zube a kasa ta hau gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana ya bakunta ta sunkuya da kai tana Alhamdulillah Alhaji Salis tarbar da Aisha ta mata ba karamin faranta masa yayi ba inama iya su biyune matansa duk abinan Aisha bata kalli Inda yake ba Alhaji Salis yace "Aisha ga Aneesa kanwarki nan anjima zaa kawo kayanta d'akin dake can karshe zata zauna dafatan zaki riketa da Amana" "Ai wanan ba kanwata bace sai dai 'ya kanwarsu Luba ce tsakanin uwa da yarta ai sai mutunci da girmamawa insha Allahu diya na d'auketa sai dai na nace Allah ya kau da fitina" Sai Alhaji Salis yaji zuciyarsa ta sosu da abinda tace wato ita bata daukeshi ma a matsayin miji ballantana tayi kishinsa. Mayafin kanta ta kara gyarawa tana "Yata ni zanje wani gaisuwa sai na dawo" "A dawo lafiya Aunty" Allah yasa Daga haka tayi waje Salis ya juya yayi bayanta Yana cewa Aneesa ta fito ta koma dakinsu Afrah. Koda suka fito Luba na zaune a kujerar dake kallo k'ofar sai girgiza kafa take Ba wanda ya kalli Inda take Duk da kananan maganganu da take Aisha tayi waje Alhaji Salis yabi bayanta Aneesa Kuma tayi bangaren su Afrah. Aisha na fita wajen motarta ta nufa bata nuna ma tasan salis na bin bayanta ba sai da ta bude ta Shiga Salis ya sunkuyo ta wajen glass Yana "Aisha banji dadin maganar da Kika yiwa Aneesa ba bai dace kiringa nunawa a koina bakya kaunata ba bai dace kiringa nuna wa mutane irin zaman da muke dake ba haba Aisha" "Salisu kenan ni ba abinda nayi idan Kuma ba rigima kake nema ba zanje Aunty mamy na jirana" Daga haka ta rufe motar Salis yace adawo lafiya taja motar ta fice daga gidan. A takaice Yara na dawowa suka taya Afrah gyara d'akin da Aneesa zata zauna bisa umarnin Alhaji Salis Luba kuwa kamar tayi bindiga dan duk hauka Salis da Hindatu Suka manna mata har dukan Yara tayi dan suyi magana ba Wanda yabi ta kanta har suka gama Aneesa ta koma dakinta Inda ta kudurce a ranta ta ringa zaman daki tana kulle k'ofar ta tunda akwai komai na bukata a d'akin dan karamin d'akin ajiya Salis ya maida mata shi kitchen da komai na bukata har ga Allah ba yanda zatayi ne amma bataji dadin kawota da Salis yayi cikin matansa ba a wajen Aisha kawai ta samu sakin fuska. Luba burinta Aneesa ta Kara karbar girki ta jibga mata aikin gidan,dan tasan bata isa ta iya dafa musu abinci suci ba,Karin bakin cikinta da ranar girkinta ya zagayo har Alhaji Salis ya gama mata kwanakinta ko tab'ata baiyi ba ko da tayi magana ma manna mata hauka yayi,ita a wajenta ba bukatar ne ya dameta ba burinta idan girkinta ya zagayo ta wahalar dashi ta tara masa gajiya yanda idan ya koma d'akin koma wacce bazai iya tab'uka komai ba. Duk burin da taci na cin uban Aneesa idan girkinta ya zagayo sai gashi Alhaji Salis yace Aneesa bazata yi girkin duk gida ba zata ringa girkinta daban tana ci su masu yaran su cigaba da yanda sukeyi,nan Luba ta daka tsalle ta dire akan ba Mai yuwa bane. Alhaji Salis ko ta kanta bai bi ba ,tsananin tsoron Luba da Aneesa keyi yasa ko fitowa bata iya yi,kullum tana dakinta idan kuwa Alhaji Salis ya fita haka zata zo ta ringa buga mata kofa tana zaginta itama Hindatu idan kishi ya motsa mata sai ta hau taya Luba,dan tunda kuma Alhaji ya auro Aneesa yake wulakanta su a yanzu ko shakkar Luba baya yi inda Luba hankalinta ya Kara tashi tanaso taji mai ya taka a haka Aneesa ta samu wata biyu a gidan idan har ranar kwanan Aneesa ne Luba bata bacci haka zata zo tayi ta musu labbenta a garin labbenta ta jiyo wa kanta mugun tashin hankali da ya sa zuciyarta kusan bugawa a ranar ko runtsawa batayi ba Alhaji Salis na fita daga gidan ta tafi d'akin Aneesa ta hau bugu dan burinta ta bud'e kawai ta mata mugun duka Jijjiga kofar kawai take tana "Shegiya karuwa idan kin isa ki bud'e k'ofar nan har mu zaki zo kiringa yiwa bariki Yar mitstsiya dake" Luba tace cikin hucci tana bubuga k'ofar dakin Aneesa da k'arfi. Hindatu kuwa tana daga gefe tana "kefa kike ganin laifin yarinya nan wlh Alhaji shi yafi bani kunya wai ace Saar Yar cikinsa yake zuba kwartanci da ita a gida har zaa ringa Mana ihu dan a bata Mana tarbiyar Yaya na rasa uban me yagani a jikinta ma ya aurota naga idan farar ce akwai ta a gidanan idan Yar lukutar ce ma akwai a gidan nan idan ma mumunan ce ma duk ya hada" Luba wani irin kallo ta fara bin hindatu dashi tana "wacce mumunar"? "Oho kinji na Kira Sunanki ne"? Luba Kan hindatu ta koma suka fara zage zage Aisha dake yanke farcen ta ta mik'e da rezar hanunta ko kallon wajen da suke batayi ba ta shige dakinta zaman daki isarta yake wani zubin tana san zaman palon amma tashin hankali da fada da Luba da Hindatu keyi ke hanata zama sai gashi bayan tsawon lokaci da ta dan fito yau dan ta Sha iska sun fara fada. Aneesa .. *Mg's skincare* Yan'uwa indai gyaranjiki kukeso inamai Kara gabatar muku da kayan mg's domin kayansu dayane tamkar dubu tested nd trusted sa'annan kayansu yanagyaran jikine naturally domin bawai na bleaching bn natural/organic zaidai gyarajikine yafiddo ma mutum da ainihin kalarshi wato natural beauty dinku Sister nace ba pimples ne matsalan,spot(tabo), sunburn,acne, black heads, knuckles,ko Mai Kika shafa yabatamiki jiki ko fatarkine take tattarewa? Kinasone kawai kikara gyara jikinki fatarki tayi clear tazama smooth tadinga glowing sister's kunemi kayan mg's 08062991549 insha Allah bama kuba har customers saikun kawomusu Sannan fa bana tafi bara kyau domin sunkarama products dinsu ingantattun abubuwa wnd zaifito Miki da baiwar halittar da Allah yamiki Dan duk inda kikayi se anjuya inamasusan suyi haske Suma bana bleaching ba pls kuyi mgn fatarki zatai haske naturally batare da Kun lahanta fatarku ba akwai hadin amare shima bama cika Baki kicire kokwantan kinjaraba abubuwa bemiki ba kigwada kayansu zakisha mamaki bi'iznillah Soap price:4k Small beauty kit:12k Flawless skin beauty kit:20k Chat:08062991549,07046881166,07067210195 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Team glow *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* Last free page *Page 12* Aneesa Wayarta ta d'auko jikinta na rawa ta nemo lambar Alhaji Salis Yana d'auka ta fashe da kuka tana "Baby Nagaji wlh Nagaji Aunty nan so take ta kasheni gata nan sai buga k'ofar take,bby Kar ta fasa k'ofar ta shigo indai ka bar gidanan haka nake zama cikin tashin hankali nidai ka taimaka min ka dawo kazo ka fitar dani daga gidanan na gaji ban Saba da hayaniya ba" Ta Kara rushewa da kuka har ga Allah ta fara nadamar Auren Alhaji Salis ko muryar Luba taji sai gabanta ya Fadi,ta Kuma karanci Luba boss ce a gidan ko Alhaji Salis din ma bai Isa da ita ba Yana fada tana fada sai a yanzu ta fara gano illar da mahaifiyarta ta ringa hango mata na auren Alhaji Salis har ga Allah tana kaunar Salis amma aurensa ya fara fice mata a rai bazata iya da wanan tashin hankalin ba Luba kuwa fadan da suka koma yi da Hindatu yasa ta bar bugawa
Chapter 20 · 0% Book details