← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 71

Sashe 61

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bata san lokacin ma da bacci ya d'auketa cike da mafarkin ta samu Wanda ya mata aiki ta koma gidan salis ya saki ma Hindatu ita kadai ce a gidan ba. Sam bata ji dadin katse mata baccin da akayi ba bugun da aka Kara yiwa k'ofar da k'arfi ana "Luba wlh sai na miki rashin mutunci ki bud'e min k'ofa wanan wane rashin mutunci ne" Luba sai da ta duba agogon d'akin taga wajen karfe tara na dare,tasan zuwa yanzu dai mijin Habiban ya dawo. Wajen k'ofar tayi ta bud'e tana bud'e k'ofar habiba ta janyo ta waje tana "ke karamar Yar iska ce wlh sai kin bar min gida nan dai gidana ne ko ba gidanki ba bari na tuna miki maganar da kika yi abaya "Kowa ya zauna a matsayinsa ba dole ne zumuncin ba ni bana san takura na rasa wanan jarraba ba abinda zai kaini gidan kowa nima a daina zuwa ana takura min" "Luba karki ga kina da arziki kina ganin a haka bamu Kai ki ba watarana zan iya miki Rana" "Allah Kar ya gwada min ranar da zan zo wajen ki Neman wani Abu sai dai ni kizo nema a wajena haba Aunty Habiba ki duba mana taya zan zo neman abu wajenki"? "Luba kenan Ina rokon Allah ya gwada min ranar da zaki zo wajena Neman Abu ni Kuma Zan tuna miki Wanan ranar" "Ba amin ba bakin ki ya sari danyen kashi" "Kin tuna ranar da kika fadamin maganar nan daga zuwa gidanki dan mu gaisa" "Shaidan ke tuna baya Aunty Habiba a lokacin bansan mai nake cewa ba banida hankali a yanzu na janye kalmar ki yafe min" "Wlh baki isa ba kizo ki koma gida wajen baba tunda ba kowa a can nima gidanan bazai dauke ki ba tunda daki uku ne kacal" "Zan na kwana cikin yaran" "Aunty Habiba na k'ok'arin Magana muryar mijinta sabitu ya katse ta yana "Wai me ke faruwa ne tun dazu da na shigo nake Jin magana"? Luba tsugunawa tayi da sauri ta hau matsar kwalla tana gaishe shi Ya amsa tare da maida hankalin sa wajen Aunty Habiba da ta hade rai Yana "Mai ke faruwane"? Caraf Luba ta hau magana cikin muryar kuka" "Wai cewa tayi sai na bar mata gida sabida na roki arzikin zan zauna na kwana biyu kafin mu daidaita da mijina" "Sabida me zaki koreta habiba ba Yar uwarki bace ba"? Habiba cije lebbenta tayi cikin takaici dan batasan da yanda zata masa bayani ba macece ita Mai zurfin ciki da sirri duk wani Abu daya shafi gidansu bata fadawa mijinta dan a ganinta ba komai zata na fada masa ba sirrin gidansu sirrinta ne ba sai yaji ba,duk wani wulakanci da Luba take shukawa ko da wasa bata tab'a fada masa ba" "Idan baki taimaka Mata ba waye zai taimaka mata Habiba Yar uwarki ce fa ko makotane suka zo neman taimako ai Kya taimaka musu balle Yar uwar ki bansan ki da haka ba mai dan ta nemi arzikin ta zauna ki barta ta zauna har zuwa lokacin da zata daidaita da mijinta" "Nagode kwarai Allah ya saka da alheri ya kara girma" Luba tace tana washe baki "Ba komai" Sabitu yace tare da komawa palon. Habiba kuwa sam ba haka taso ba dan har ga Allah tana kallon Luba rashin mutunci da ta mata na dawo mata abune mai wuya ta manta Luba kuwa ta mik'e tana "hakuri zakiyi Aunty Habiba" Tsaki Habiba tayi tayi hanyar Kitchen Luba ta bita a baya dan zuciyarta fes take tunda ta samu yardar mijin Habiba. Abincin ma sai da tayi dagaske Habiban ta zuba mata kad'an. Ta d'auka idan aka kwana biyu Habiban zata hakura ta sakar mata fuska sai dai ina rufe idonta tayi tana wulakanta ta har gori take mata inda abin yake mata ciwo,har banda kaddara da tasaka tayi hauka Salis ya saketa, Habiba tama isa ta doso Inda take ballantana ta mata wulakanci. Ba karamin tsanar Habiba take ji a zuciyarta ba ji take dama zata iya abinda zatayi itama a saketa su zama daya. Da ace tana da wajen zuwa da tuni ta bar mata gidanta ta huta da gorin da take mata,tsabar wulakanci yaran ma dakinta ta maida su banda mazan ita haka take barinta ta kwana a palo dan daki daya suke kwana da mijin, yaranta maza suna da daki daya,na ta Kuma yara matan ke kwana a ciki,abu daya taga Habiban bata d'auka,Bata yarda yaranta su Mata rashin kunya ko suk'i gaisheta. Amma wulakanci Kam tana sha a wajenta ba dama tayi motsi sai taje bakin halinta yasa Salis ya saketa idan ta isa tayi zuciya ta koma gidanta ai idan tanaso taga daidai taje ta nemi yafiyar wayanda ta zalinta Sau uku kenan tana furta mata wanan kalmar da take ji kamar ruwan zafi take watsa Mata. Karshen wulakanci dai Habiba tayi mata inda ta fara shan alwashin sai itama tayi duk yanda zata yi ta kashe auren Habiban. ASHRAF Tuni ya maida hankalinsa wajen bincike dan a yanzu burinsa kawai ya gano Wanda ke da hannu a rashin lafiyar muhasim. Sau biyu kenan Yana gwada nunawa muhasim hoton Luba tana fita a hayyacinta a yanzu ya gano dole Luba tana da hannu a matsalar muhasim amma yafiso ya samu hujojji masu k'arfi kafin ya shigar da Kara akan Luba. Alhaji Salis kuwa har tausayi ya fara bashi dan yayi wani irin sanyi ba iya kunyar Ashraf yake ji ba har da sauran yaransa, Hindatu kuwa sam ta kasa gane kansa da taso matsa masa ma barazana ya mata da zai saketa bayason takura yafiso ma shi yayi rayuwar sa shi kadai,har ga Allah harkar cocaine dinan kawai yasan yake yi bai tab'a shaawar safarar Yaran jamaa zuwa waje ba dan har wa'azi yake yiwa zainab tashi daya ya wayi gari da san yayi harkar safara har ya tsunduma kansa a ciki a yanzu Allah kadai yasan kalar nadamar da yake,duk da a idon duniya karfin kudi yasa an wanke shi baiji ya samu kwanciyar hankali ba maganganun Ashraf sun matukar tsaya masa a rai duk Kuma san kudinsa Yana tsoron ranar da zai tsaya gaban Allah san zuciya ta kai shi ta baro shi, yak'i godewa Allah da niimar da ya masa har sai da ya hada da cudanya halal dinsa da Haram,iya zaman duniya dai salary dinsa da harkar Ngo dinsa ya ishe shi a cikin wata uku komai ya rushe masa ba Aisha a gidan ba Aneesa shi a yanzu ma baya jin wani ciwon rabuwa da Aneesa Aisha matarsa matar rufin asirinsa ita yake Jin ciwon rabuwar da takeso suyi,duk da Yaya mustapha a masu zuwa masa barka har dashi dan shima ya yarda sharri aka masa ba halinsa bane ba. Kira message na ban hakuri bazai iya lissafa yanda yake turawa Aisha ba. Luba kuwa har ya koma ga Allah tsine Mata kawai zai ringayi dan itace ta fara rusa masa gida. A hankali shima ya fara k'ok'ari wajen ganin ya fitar da Hajiya fauza da John dadin da yaji yaran da suka Kai rabi sun dawo gida nigeria da baa Kai ga kaisu wajen larabawan ba. Sauran Kuma baisan yanda zai nemo su ba. A yanzu komai ya fice masa a rai shima burinsa muhasim ta samu lafiya ko Aisha zata rage kiyayar da take masa ta hakura ta dawo gida,a yanzu ya ninke ibadarsa fiye da baya,duk da yasan Allah baya yafe hakkin wani amma har a yanzu yana mamakin san zuciyar da ya kai shi aikata abinda yayi Allah yasan da Neman muhasim da harkara safaran nan yayi nadamarsu fiye da tunanin mai tunani. A yau wajen hudu na yamma Ashraf yaje gidan Yaya mustapha Kamar yanda ya saba bayan sun gaisa da su yaya mustapha ya nufi dakin da Aisha ke zama da komawarta gidan suka bar mata d'akin ita da Nana da muhasim. Koda ya Shiga akan sallaya ya tarar da Aisha tana jan carbi,yasan dauriya kawai mahaifiyar sa keyi zuciyata na cike fal da damuwa. Kuma duk sabida muhasim take cikin damuwar. A Kan kujera ya zauna har sai da ta shafa Addu'ar ta mike tare da amsa gaisuwar da yake mata tana tambayar su Afrah tana "Ni ya batun saurayinta dayace zai turone ko ya fasa ne sabida yaji halin baban ku" "Hajiya umma dan Allah ki ringa kyautatawa Abba zato jiya ma suka je wajen Abban inaga sun tsayar da magana akan sai bayan babban sallah" "Allah ya nuna mana dan Addu'ata kullum Allah yasa Kar laifin mahaifin ku ya shafe ku" "Hajiya umma wlh sabida yanda kike san dorawa Abba duk laifin abinda ya faru yasa na jajirce wajen bincike wlh Abba bashida hannu a larurar muhasim" "Ashraf kenan duk Wanda yake da hannu Allah ya tona masa asiri dan ni Ina da tabbacin mahaifin ku ne ya maidata haka dan rufin asirinsa Yaya dan ya dage min ne idan ba shi bane waye toh zaiyi mata haka"? "Aunty Luba kawarki tana da hannu a abinda ya sameta sabida ta samu Abba ya aureta,a yanzu na sake yowa wani binciken a gabanki nake so na tambayi muhasim kigani" Ashraf mik'ewa yayi ya gyarawa muhasim wuyan ta ya zauna a gaban ta tare da jawo jakar sa Aisha ido kawai ta zuba masa dan tunda yake zuwa gidan da Sunan bincike wajen muhasim daki ya ke kaita dan duk ta d'auka shirmensa yake zuwa yayi. "Aunty muhasim ki daure ki daina firgicewa idan na nuna miki hoto inaso ayi gaggawan Kama Wanda ya karkata miki wuya idan na miki tambaya idan hakane ki lumshe idonki idan ba haka bane ba karki lumshe idonki kiyi hakuri baza su fito daga hoto su cutar dake ba" Aisha tashi tayi tsaye itama taje gaban muhasim ta tsaya tana Jin kirjinta na dukan uku uku Hoton Salis Ashraf ya fara zarowa Yana "Aunty muhasim wanan ne ya karkata miki wuya"? Muhasim bata lumshe idonta ba illa hawaye dake ta zubar mata tana kallon hoton Salis Wanda hakan yasa Aisha fashewa da kukan da take dannewa tana "Salis ya cutar min da 'ya Allah ya Isa tsakanina dashi bazan tab'a yafe mishi ba ya cutar da Muhasim ya kassara
Chapter 61 · 0% Book details