Sashe 49
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba dan a yanzu bai san mai zai ce mata ba sun taso su biyu tare da mahaifin su,da ya matukar gwada musu so da kauna,duk da yana yaro bai manta yanda Luba ta watsar dasu tayi tafiyarta ba Suka ringa rayuwa kamar marayu,daga makaranta sun sha zuwa wajen ta amma haka zata rufe ido tace su koma wajen ubansu ita bama taso asan ta tab'a haihuwa su daina sintirin zuwa gidansu har akwai lokacin da suka je gidan ta rufe shi da duka sabida ya kirata da Sunan mama a gaban Wanda take zance,ire iren Abubuwan nan yasa basa jinta a zuciyarsu ko kad'an ilham ma tafi shi ruko dan ta Sha cewa ita bata da uwa ta mutu,bata tab'a waiwayar su ba har sai da mahaifin su ya fara samun Yan canji,takan kirasu a waya idan ta bushi iska tazo ta gansu Wanda da zuwanta da Babu duk dayane a wajen su dan matan babansu sun rike su tamkar su suka haifesu, sun ma fi Jin kaunar su a kanta" "Yana ji ka min shiru ko baka ji mai nace bane"? "Toh mama mai zance yanda kike magana ne Kamar irin nasan an sakeki ne bayan ni bansan an sake ki ba" "Toh a yanzu ka sani gani nan a titi na rasa wajen kwana kazo ka nema min wajen kwana ko hotel ne ka Kama min ai baka isa kace min baka da kudi ba" "Mama wlh banida kudi Abba bai fiye bamu kudi ba duk abinda dai muke so yimana yake yi Kuma ni kinsan ba aiki nake ba ki roki su Inna su barki ki zauna tunda bakida wajen zuwa" "Sultan yanzu ni zaka cewa baka da kudi,? sultan wulakanta ni zakayi nifa na tsugunna na haifa ka da motar ka da babbar wayarka a hannu ko su bazaka siyar dasu ba ka nema min wajen zama kafin komai su daidaita? idan har baka min ba wa zaka yiwa sultan? Yanzu karfe tara har da rabi banci komai ba ga sauro dake ta cizona ku kuna cikin Ac da gado ni Ina titi a zaune"? Shiru sultan yayi dan ji yayi kansa ma ya fara ciwo sai da ta kara magana yace "Kina Ina Yanzu"? "Ina k'ofar gidanmu a zaune"? "Toh gani nan zuwa" Ya katse wayar luba ta hau cewa "Banda b'atan basira ma irin nawa duk abinan na manta Ina da yaron da zai iya taimaka min kila da jiya da shegen ubansa ya koreni da na kirashi a waya da kila ya nema min wajen kwana naje na samu tsinannen yaron nan ya min fyade na rantse da Allah sai na wulakanta yaron nan" Tace tana sosa gabanta minti sha biyar a tsakani ta hango sultan ta kuwa mik'e da sauri tana washe baki ai ko bai sama mata wajen kwana ba ta kwana a motarsa kafin ya nemo mata gidan haya ta zauna. Tun kafin ma ta tsayar da motar ta bud'e tana k'ok'arin shiga sultan yayi saurin cewa "Wai so nake na shiga na roki baba ya barki ki zauna a gidan mama wlh banida inda zan Kai ki kema kinsan ko gida na kai ki Abba ba yarda zaiyi ki zauna ba" Tsaki taja ta shige cikin motar tana "Karma ka wahalar da kanka wajen ma zuwa wajen baba dan yayi nisa idonsa ya rufe da san yaga na wulakanta burinsa yaga Ina garari a titi nima Banda kaddara mai zai kawoni gidan nidai muje ka Kama min d'aki gobe sai ka nemo min gidan haya na zauna na dan lokaci" "Mama Dubu hudu ne kawai dani bai zai isa a Kama Miki daki ba sanan Ina zan samo kudin da zan kama miki haya"? "Idan baka san yanda zaka yi karya ka samu kudi a wajen baban ku ba sai ka siyar da wayar ka ko motar ka ka Kama min haya Ina da kamar Kai bazai yu na ringa garari a titi ba,wane irin wahala ne ban sha akan ku kuna Yara ba sai dan yanzu ka min abinda bai taka Kara ya karya ba sai kace min wani baka da kudi" Ya riga da yasan kalar rigimarta baice komai ba ya tada motar Suka dau hanyar wani karamin hotel dake bayan gari Dubu uku ne kwana daya har suka isa hotel din bambami take baice mata komai ba dan ya riga da ya Yanke mai zai yi Dubu hud'un ya fito dashi ita kuwa ta tambayeshi nawane kwana daya yace mata dubu biyar ne,Dubu daya ta d'auko ta bashi ya barta a cikin motar sai da ya lalubo dubu daya ya cika ya Kama mata na kwana biyu aka bashi mukulin d'akin,ya fito wajenta. Suka koma ciki tare shi ya bud'e mata d'akin ta shige tana "A yau nima da ban Haifa ba sai na hadiyi zuciya na mutu jiya da ace na kiraka da duk abinda ya Sameni jiya da bai sameni ba wanan wane irin hotel ne d'akin wani iri kamar ba hotel ba ko dai yake ya dai fi rufin asiri da na ringa bin mutane ana wulakantani karbi ka samo min abu naci dan yunwa nake ji ka hado da dan bredi naci da safe idan Kuma zaka kawo min abincin karyawa da safen shikenan " Kudin kawai ya karba yayi waje minti goma a tsakani ya kawo mata abincin Ta karba tana "Yauwa dan albarka kai baka iya dan dabaru wajen karbar kudi a wajen Abban naku ba yanzu karya zaka masa akan motar ka ta lalace ka yanka masa kudi yana baka ka kawo min muje mu kama haya idan da canji na samu na dan siyi kayan sawa iya wanan na jikina ne kawai dani wlh Salis ya wulakantani ko tsinke bai bari na d'auka ba ba abinda ya bari na d'auka" "Ba damuwa mama zan k'ok'arta insha Allahu" "Allah ya maka albarka gobe zaka kawomin abincin karyawar"? "Eee insha Allahu" "Yauwa dan Allah dan Allah ka hado da dan romo romo an kwana biyu baa hadu ba" Gyada.mata kai Sultan yayi ya mata sai da safe Yana fita ta baje a tsakiya gadon taci ta koshi ta shige bandaki ta daura alwala tazo ta Rama duk sallolin da batayi ba tana iddar wa ta kwanta ta hau sosa gabanta da taji yana mata masifar kaikai yi tana "Allah ya tsinewa yaron nan Albarka ya saka min cuta dole na nemi kudi na tafi asibiti. Bacci na fara d'aukar ta kaikaiyi zai saka ta tashi ta fara susa. Alhaji Salis Shiru ne ya ratsa motar bayan ya gama bawa Yaya mustapha labarin duk abinda ya faru Kama daga yanda Luba ta fara bibiyarsa har zuwa lokacin da ta saka masa magani dan ya nemeta a ranar muhasim ta tsallake bai mata fyade ba har zuwa yanda Luba ta cigaba da bibiyarsa da yanda ya wayi gari da bukata komai sai da ya kwashe ya fadawa Yaya mustapha dan gani yake a yanzu fadar gaskiyar shine mafita a gareshi. Ashraf kuwa kansa a sunkuye har ya gama bada labarin yana kara bibiyar labarin a kansa. "Kayi babban kuskure wajen b'oyewa Aisha yanda Luba ta ringa bibiyar ka da ace ka fada mata da tuni ta dade da rabuwa da ita" "Yaya wlh a lokacin ko na fada mata bazata rabu da ita ba dan akwai lokacin da na rabasu haka ta hau fushi dani, wlh tsoron Luba ta tona min asiri akan abinda na aikata Wanda Allah shine shaidata baa hayyacina nayi wa muhasim fyade ba wlh wlh ba'a hankalina nake ba Yaya muhasim 'yace a gareni bazan tab'a yi mata haka da gangan ba da ace Kuma Ina da hannu a karkata mata wuya wlh Yaya da na fada maka tunda asirina ya riga da ya tonu banida hannu a abinda ya same ta" Shiru ne ya Kara ratsa motar tsawon mintuna kowa da tunanin da yake a zuciyarsa. Kafin Yaya mustapha yayi gyaran murya yana "Daga labarin da ka bamu duk yanda akayi Luba tasan wani abu damu bamu sani ba bansan Mai yasa nake zarginta ba bana jin muhasim zata iya tararta ta fada mata tana d'auke da juna biyu akwai dai abinda ke b'oye. Ashraf gyada kansa yayi Yana "Tabbas nima daga labarin da Abba ya bayar na Kara tabbatar da zargin da nake mata bazan iya tunawa ba akwai ranar da naji suna hira da kawarta a dakinta wanan bakar kawar tata mai bille sunan muhasim da naji ta Kira yasa na tsaya sai Kuma naji sun kara kasa da murya ban kawo komai ba sai ayanzu sa Abubuwan nan ke faruwa naji na Kara tabbtar da zargina amma ba komai uncle ku bar komai a hannuna zanyi bincike insha Allahu" Gyada kai yaya mustapha yayi Yana "nima a yanzu gabad'aya zargina ya koma kanta kayi bincike da kyau" Salis kamar an cire Masa wani gundumemen dutse akansa haka yaji yaji Dadi da yanda Yaya mustapha bai d'auki zafi kamar yanda yayi tunani ba har sukayi sallama dashi Suka fito daga motar shi da Ashraf sukayi cikin gidan. Suna Shiga Palo wayarsa ta fara ringing ganin worker ke kiransa yasa yaji kirjinsa ya buga kasa d'aukar wayar yayi ya shige daki da sauri. Ya daga wayar maganar da Uje ya Masa ya sa shi sakin sallati yana "Shikenan asirina ya sake tonuwa uje da wane irin ido Zan kalli mutane idan suka gano halin da muka jefa kanmu innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Shigowar Ashraf d'akin yasa shi sakin wayar sabida jikinsa rawa kawai yake. Ashraf ya zuba masa ido, Uje kuwa sai hello hello yake Ashraf yace "Abba akwai wani sirri bayan na muhasim da kake ganin ya Kamata nasani"?..... Wlh wlh bana Jin dadi dak'yar nake rubutun nan Ammnur _kayan mata tazo muku da zafafan kayan matan da babu algus 09080070762 Ina uwargida da ta haihu vjay dinta ya bude tana bukatar taji ta koma budurwa gam ga ammnur Nan ta kawo muku zafafan kayan mata Ina amare masu Shirin shiga daga ciki,Ina Zawara da suke so suji Basu da bambanci da budurwa Enjoyment doesnt stop just because you have given birth. The afterbirth package is made to take care of you postpartum sexual needs . This package includes sweetner, wetner, tightener infection