← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 71

Sashe 42

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ruwan zai mata a haka ta watsa a gaban ta ta cire dan skirt din ta ta goge duk jikin ta kyankaymin kanta kawai take tana tarar yawu a bakinta sai da ta kara awa daya a d'akin dan sau biyu tana gwada tashi sai taji Kamar iska zai d'auketa da alama magani mai k'arfi gambon ya sa mata a furar. Sai da ta dan ji dama dama ta mik'e ta fice daga d'akin tana Shan alwashin Nemo gambo a duk Inda yake dan ba abinda zai hana ta daureshi har sai taga gatansa. Babban burin ta yanzu ta samu wajen da zata cuda jikinta ta wanke jikinta da take Jin ya Kama warin jikin gambo ta samu ta canza kayan jikinta ta tafi gidan Asabe ta bata kudadenta dan bazai yu da uwar kudadenta ta ringa bulayi tana neman wajen zama ba kudin ta na wajen Asabe zasu ishet a ta siyi karamin gida ta juya sauran kudin ta yanzu wajen da zata fara zuwa tayi wanka ta canza kayan jikin ta take nema ko a mafarki bata tab'a tunanin Asabe zata juya mata baya ba,yanda Aisha ta Zama tamkar shashasha a wajenta ta ringa mulkarta haka Asabe ta ringa juyata tana mulkarta wani zubin sai taji Kamar ta rabu da ita sai Kuma ta fasa dan Asaben tana taimaka Mata sosai wajen samun cikar burinta,sai gashi daga mutuwar aurenta Asabe ta murzawa idonta toka,rashin basira da hauka ya Kai ta tonawa Salis asiri,sai gashi ita nata asirin ma yafi tonuwa daga lokacin da ya saketa har zuwa yanzu bata Kara samun kwanciyar hankali ba garari kawai take har da almajiri mai doyi da bai wuce saan dan cikinta ba ya mata fyade. Ba inda zata je dai tayi wankan daya wuce gidan su tasan mahaifinta nada zuciya ko duk mutanen garin nan zata Kai akan a roke shi ya barta ta zauna bazai tab'a sauraran su ba da ace ta tab'a kawowa kan ta irin wanan ranar da ta zage wajen kyautata musu. Gidan nasu ta nufa dan tasan a yanzu mahaifinta ya fita bazata same shi a gida ba ballantana ya hana ta shiga gidan. A lokacin da ta isa gidan kuwa bata same shi ba sai Inna da yayarta Habiba da basa ko magana ballantana su hada inuwa daya dan rashin mutunci sosai ta karta mata da ta isheta da waazin abinda takeyi bai dace ba ya zaayi ace iyayensu ma bazata na mutunta su ba. Ganin ta take matar mai kudi duk girman mutum yayi kad'an ya taka ta hakane yasa tayi wa habiba kaca kaca dan tasan sai dai habiban ta moreta ba ta da abinda zata bata, habiban kuwa ta Sha alwashin fita daga harkarta. Inna ce kawai ta amsa sallamar da tayi habiba dankwalin kanta ta turo gaban goshinta tana "Mai matar Alhaji tazo nema a gidan talakawa baiwar Allah ko b'atan hanya kikayi"? Luba ko kallonta bata yi ba ta fara k'ok'arin shiga cikin d'akin. Inna ta dakatar da ita tana "Luba ki rufamin asiri kizo ki tafi karki jawomin dan wlh Baban ku yace idan har na sake na Kara barin ki kika zo gidanan bai yafe ba Kuma a bakacin Aurena" Luba juyowa tayi cikin wani irin muryar masifa tana "Inna idan ban zo gidanan ba Ina kuke so naje"? Ina da sama da kune shikenan dan Aurena ya mutu sai a nemi a wulakantani Inna ko Abba zai koreni ya Kamata ace ki biye mishi har Kina na rufa miki asiri nazo na fita,Ina da iyayen da suka wuce ku ne" "A yanzu da aka sako ki Kika san kina da iyaye ai mallama kizo ki fice a gidanan ba abinda ya shafe mu da sakin da aka miki sai a yanzu da kika zama sakakiya kika San ma kina da iyaye har ma suna da gidan da zaki zo gidan da kike kyankyaminsa, gidan da idan zaki zo sai da turare,gidan da idan kika zo kike toshe hanci yau shine gidan da zaki zo ki zauna kiyi Zawarci ai wlh baki isa ba ko inna ta bar ki wlh sai na zuga Abba ya koreki ba dai duniya kika zaba ba wlh baki fara ganin komai ba" "Sai ki bari idan akwai kudinki a gina gidanan sai ki koreni,idan kuma kina da k'arfi zaki iya zuwa ki fita dani, Abba Kuma ko ya koreni wlh sai na dawo ba inda zanje dan shine ya haifeni idan Kuma ya dage bazan zauna a gidanan ba sai ya kaini Inda zai ajiye ni shikenan mutum bazai yi kuskure a yafe masa ba idan ma banda kaddara ma wlh ko labarin sakin nawa ba mai ji kike wani tada jijjiyoyin wuya da kudina karki dauka a wulakance nake ko a yanzu kudin nawa Suka dawo hannuna ko da kudinki kema.kinsan baki isa kizo wajen da nake ba" "Yayi kyau matar mai kudi kinsan kina da kudinki uban me Kika zo nema a gidan namu ai yanzu ki burgeni kije ki nemi gidan da zaki zauna din sanan duk cika baki kike ki bari Abban ya dawo ya Sameki a gidanan kiga yanda zaki kwashe dashi,ba dai ba abinda Kika sani sama da cin amana da wulakanta mutum ba insha Allahu sai Kinga yanda karshen ki zai yi duk wani mugun Abubuwan ki da kike yi a boye duk nasani kallon ki kawai nake domin shi sharri dan aike ne Allah ya baki dama duk kin tsulla tsiyar ki a yanzu lokacin da zaki girbi abinda kika shuka ne" "Ai insha Allahu kuwa bazaki ga karsshena ba sai dai ni naga karshen ki mugun halin ki yasa bakya cigaba kina nan shekara da shekaru kina fama" Mik'ewa Habiba tayi da sauri tayi kan luba,Inna ta mik'e da sauri ta tareta tana bata hakuri. Luba kuwa taja tsaki ta shige daki ta tub'e kayan jikin ta ta jawo soso da sabulun inna dake kasan gado ta fito da daurin kirji sai da ta cika katon bokiti da ruwa ta shige bandaki. Sai da ta kusa karar da duka sabulun a jikinta dan har yanzu tana Jin warin jikin gambo a jikinta tana Jin Inna da Habiban suna ta magana idan ba kaddara ba mai zai ma kawota har da Habiba zata samu damar mata maganganun banza. Alwala ta daura ta fito,dan bata yi ma sallah asuba ba gashi ta fara Jin Kiran sallah azahar,kayan ta ta Kara wankewa ta shanya dan bata da kayan sawa dole su zata maimaita dan kayan inna bazasu tab'a shigar ta ba dan tafi Inna kib'a. Salis ya cuceta da ya hanata d'aukar komai har wayata bai bari ta d'auka ba,bata tab'a zaton zai iya mata rashin mutunci da ya kai haka ba yau da ko iya kayanta ya bari ta kwashe dan kunnenta da sarka kawai sun isheta ga kayanta da duk masu tsada ne wa ma zai yarda motocin ta sun Kai biyu taya ta gama dandana irin wanan daular shekara da shekaru a cikin Rana daya ta zama abin tausayi har da kwana shagon da ko mai gadin gidan Salis bazai iya kwana a d'akin ba ta karfin tuwo sai ta komawa Salis idan bata koma ba gwara ya zauna shi kadai dadin abin Ba Asabe kadai tasan hanyar wajen mallamin ba itama zata iya zuwa duk da Rabin zuwan Asabe ke zuwa, bama tabin ta Kan mallaman sosai Asabe ke mata sintirn zuwa tana cazarta kudade masu yawa Sai da ta iddar da Sallah ta fito daga d'akin fuskarta a hade tayi hanyar Kitchen dan wani irin yunwa take ji rabon ta da abinci mai kyau tun a gidan Salis. Tana Jin Inna na ta fito mata daga kitchen Tukunyar dake kan gawayin ta bud'e. Tuwo ne da miyar kuka da alama na jiyane aka dumama sauko da tukunyar tayi gabad'aya ta zauna a kitchen din ta fara ci hawaye na taruwa a idonta rabon da taci wai abinci ma ba nama har ta manta ta Kuma Saba din idan abinci akayi ba nama bata iya ci . Sai da ta Kai hannu taji babu komai ta cire hanunta daga tukunyar ta wanke hannunta ta fito daga Kitchen din. Da alama Habiba ta tafi dan bata ganta ba Inna kawai ce a tsakar gidan ta hade rai tamkar yanda itama ta hade ran. A d'akin Inna tayi zaman ta har sai da kayan ta suka bushe ta debo su daga Kan igiya ta saka kayan ta fito wajen Inna tana "Inna zanje wajen Asabe akwai kudadena da yawa a wajenta idan ta bani zan siyi karamin gida nayi zawarcina kawai dan nima nasan na girma da dawowa gida nayi zawarci banda Salis ya hanani d'aukar komai iya zobuna na da sarkokina sun isa na siyi gida har na juya sauran kudina nima Zan fi sakewa ingani a gidana ni kadai idan Kuma Allah ya taimakeni na koma dakina shikenan idan Kuma Asabe ta hanani kudina dole na dawo kuyi hakuri balle ma nasan dole ta bani kudina dan har station sai munje a Kan kudin nan. "Ba zancen dole sai kin dawo bane muyi hakuri ni dama banida matsala Mahaifin ku ne dai yace bazaki dawo ba Kuma da kina da hankalin Kamata yayi kiyita bibiyarsa kina neman yafiyarsa har sai ya sauko amma dayake bakida hankali yanda zaki siyi gidan da zaki zauna kike nema wato munyi kadan ma ki bimu ki bamu hakuri,ni uwa ce bana so nayi munanan kalma a kanki sai dai nace Allah ya ganar dake gaskiya dan idonki ya riga da ya rufe" "Inna wane irin hakurine ban bawa Abba ba jiya naga har kuka na ringa masa haka ya rufe ido ya koreni dan kawai ya ga na zama bazawara a lokacin da nake da kudina da mutuncina ai Bai min haka ba" "A inda na Kara sanin bakida hankali kenan a lokacin da kike da kudin wa Kika bawa Mai Kika tab'a masa nuna min wani abu a gidanan da zaki ce ke kika kawo Kinga zo ki tafi bana san hayaniya lubabatu. Luba waje tayi tana Jin wani sabon b'acin rai sabida kawai bata zo da nauyinta ba suke mata haka. Tana fita titi ta samu abun hawa ta shige tare da fada masa
Chapter 42 · 0% Book details