← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 71

Sashe 4

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba. "Gaskiya nayi kewarku sosai no place like home indo Kinga yanda kika canja kuwa Anya kinyi kewata" "Uhum uhum" Luba tayi gyaran murya ya waiga da sauri ya kalli wajen da take zaune Yana "Kai Luba wai dama kina palon nan ai ban lura dake ba" "Ya za'ayi ka lura dani likita bokan turai" Dariya yasa Ya zauna akan kujera a daidai lokacin dana zuba kunun aya dana hada masa na mik'a masa ya karba yana "Yauwa indona kice kawarki tana cikin masu kular min daku" "Aikuwa Luba kam ba daga nan ba wlh bata bari munyi kadaicinka ba" "Aikuwa ta kyauta Allah ya bar zumunci ya mai gidan" Tuni murmushin dake fuskarta ya kau, salis bai ma lura ba sai tambayoyi yake yiwa su Afrah a takaice Luba sai da magriba ta tafi na lura jakankunan da salis ya shigo dasu take so a bud'e nidai tunda na kai d'aki ban bud'e ba,na dauka ma zata tafi da wuri tunda ya Kamata taga dacewar haka,amma bata tafi ba duk da salis ya shige d'aki. Nima na matsu na keb'e da mijina amma haka na daure na zauna muka ringa hirar a lokacin da tazo tafiya da yake girkin da nayi da dan yawa a flask na diba mata da yawa canjin daya min saura na bata ta tafi akan sai ta zo karbar tsaraba nace mata sai tazo. A ranar kusan raba dare muka yi da salis Yana bani labarin rayuwar da yayi a waje da cigaban da ya samu dan ya dage sai ya dawo ne sun bashi aiki acan amma a Yanzu ma ya samu aiki a wani baban asibiti ga Kuma aikin NGO daga labarin da yake bani nasan Salis ya zama mai kudi babban burina naga na taimaka wa Luba kwana biyu da dawowarsa bayan duk ya hucce gajiyarsa ya dan zaga dangi na shigar Masa da maganar taimakon da nake so a yiwa luba da mijinta. Cemin yayi zai yi iya k'ok'arinsa amma a Yanzu daya dawo gininsa kawai yake so ya sa a gaba zai bani abunda ya samu na bata kafin ya kamalla gininsa. Abinda ya bani mamaki Luba bata tab'a sati guda bata zo ba sai gashi tun ranar da Salis ya dawo bata Kara zuwa ba gashi a cikin lodin tsarabar da salis ya kawo mana da yayana na d'aukar mata itama da yayanta tunda itama namiji da mace ne Sultan da Ilham ganin an tafi kwana goma banganta ba yasa na nemi izinin a wajen salis akan zan je na dubata naga ko lafiya danazo tafiya ya bani Dubu Ashirin akan na bata taja jari a lokacin kudine mai yawan gaske tamkar ni yayi wa kyauta haka naji sabida tsabar murna. A lokacin da na isa gidanta a tsakar gida na sameta Sultan danta a shimfide akan tabarma Da alama bashida lafiya da sallati na karasa nayi wurgi da ledojin hannuna Ina "Luba dama sultan bashida lafiya"? "Hmm Aisha kenan yanzu tsakani da Allah tun ba'a je ko Ina ba kin fara juya min baya dan mijinki ya zama mai kudi,har ace baki gani ba kwana goma ko ki nemeni kiji dalilin dayasa ban zo ba" "Haba Luba Mai yasa kike hakane kefa mai fadawa wani halina ne wlh tunda Salis ya dawo nake ta bak'i Yan sannu da zuwa hankalina na wajenki a yau na samu kaina nace bari nazo na duba ki naga ko lafiya amma har Zaki min mumunan fassara haba mana Allah Kar ya bani arzikin da zai saka na wulakanta mutum wlh banji dadin maganarki ba" "Aisha kenan Allah ya baki hakuri nidai Ina tsoron kin canja din dan yanzu gani nake ma idan nazo wajenki zaki ga Kamar na takura ki ko nazo maula" "Allah ya kyauta tashi mu Kai shi asibiti" Nace dan har ga Allah na ji haushin maganar luba. Mik'ewa tayi ta Shiga d'aki sai da ta d'auko masa Kaya ta taimaka masa ya cire na jikinsa ta rik'e hannunsa Muna k'ok'arin yin waje sai ga Hamza ya fado gidan da leda a hannunsa. Luba kuwa ta saki hannun Hamza taje ta cakumo wuyan rigarsa tana "Hamza ka bani takardar sakina na gaji da aurenka maganin naira dari ma bazaka iya siyowa danka ba ka sakeni Hamza bazan iya da wanan auren naka ba" Hankalina idan yayi dubu sai daya tashi, dan zagi na rashin mutunci haka ta ringa yiwa Hamza. Luba bata ji bata gani haka ta ringa ihu tana ce Masa idan ya cika dan halak ya saketa sallati na saki da k'arfi a lokacin da naji Hamza ya furta mata saki biyu ita kuwa ta sake shi da sauri tana hamdala akan ya saketa. Nayi matukar bakin ciki da mutuwar Auren Luba ita kuwa ba abi nda ya shafeta sai ma murna da take da ta tashi ma barin gidan iya kayanta ta dib'a tace yaran suyi zamansu a wajen babansu bazata tafi da kowa ba. Tsananin tausayin Hamza da yaran yasa kudin da Salis ya bani akan na bata na bawa Hamza ya ringa min godiya yana min Addu'a. Luba kuwa tayi nisa a hanyar tafiya gidansu da kayanta. Haka naje gida jiki duk a sanyaye. Koda na bawa Salis labarin abinda ya faru cemin yayi dama Luba bata da hankali ai ya taya Hamza murna da ya rabu da ita. Present ANEESA Ki sake tunani Aneesa taya zaki rasa Wanda zaki aura sai mai mata har uku kije a ta uku mai zakiyi da tsoho bayan ga dan uwanki nan da ya dade Yana kaunarki,nidai wlh bazan barki ki auri mutumin nan ba sai kace kin rasa mijin Aure" "Wlh Alhaji Salis Yana kaunata Yama ce ba gida daya zai ajiye mu ba nidai shi nakeso na aura" Aneesa tace tana zumburo baki "zan ga kuwa mai aura miki shi" Mama binta tace tare da mik'ewa ta bar palon. Adaidai lokacin da Kiran Alhaji Salis ya shigo wayar Aneesa tana dagawa yace "Gani nan a waje na karaso" "Gani nan zuwa" Aneesa ta mik'e ta Shiga d'aki tare da d'auko hijabinta ta saka tayi waje...... Nayi typing mai tsayi wlh ya goge MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4500 Mg's beauty kit Karamin kit 12k Body soap Facial soap Body cream Face cream Glow oil Pink lip balm Flawless skin beauty kit Babban kit 20k Body soap Facial soap Body cream Face cream Scrub Glow oil Pink lip balm Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same, Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* *Page 4* Alhaji Salis k'ofar gidansu Aneesa kawai yake kallo Yana murmushi cikin wata uku da haduwa da Aneesa da bata fi Sa'ar Aliyu ba,duk ta bi ta rikita masa lissafi,asibitin da yake aiki a Abuja taje ganin likitan ido,bata gane office d'in da aka tura ta ba ta fado office dinsa yanda ta saki fuskarta da fara'a ta gaishe shi yasa yaji ta burgeshi anan take ce mishi tana neman Dr Ahmad murmushi ya mata akan ba office din Dr Ahmad bane wanan wanan office din Dr Salis ne idan matsalarta abinda ya shafi mata ne to ta zauna (Dr Salis Gynecologist ne) Girgiza masa kai tayi tana ita ciwon ido take mik'ewa yayi Yana ta tashi ya rakata wajen sa. A takaice a yanda ya had'u da Aneesa kenan da yaji kaunarta lokaci guda,zai iya cewa itace mace ta biyu da yaji ya kamu da tsananin santa tunda Kan Aisha bai Kara Jin san wata 'ya mace ba,duk da yana ganin abune mai wuya ma Aneesa ta yarda ta aureshi lura da shi din babba ne,na biyu Kuma taya zaiyi auren ya samu kwanciyar hankali bayan kullum cikin tashin hankali ake a gidansa kuskure kwaya daya tal ya canza masa rayuwa ya hana shi nutsuwa tsawon wanan lokacin. Kamar wasa daga waya da chatting ya kai wa Aneesa ziyara ga mamakinsa yarinya da alama ta amshi tayin soyayyar sa ba Kuma ya Jin wai dan kudinsa take San shi dan da alama Iyayenta nada kudi. Wata uku kenan da haduwarsu da ita a wajenta kawai yake Jin wani farinciki dan Aisha ta kulle zuciyarta ya rasa yanda zai goge laifin da ya mata idan hakkinsa ne tana bashi duk wani abu daya rataya a wuyanta tana mishi sai dai sam bayajin dadin yanda ta cire shi a ransa ba abinda baiyi na ban hakuri ba amma duk a banza bata san cewar Shima laifin da ya mata ba a san ransa bane ta Kan dole ya aikata abinda ya aikata. A yanzu maganar Aure yayi wa Aneesa ta Kuma ce ta amince zata aure shi duk da kasan ransa cike take da fargaba auren baisan Karin auren nutsuwa zai haifar masa ba ko akasin haka,idan ya tuna luba kawai sai gabansa ya Fadi, bai tab'a ganin shuumar mace irinta ba duk tsawon shekarun nan da suke tare bai tab'a kaunarta ba akan dole yake zaune da ita sabida wani boyayyen sirrinsa da yake fatan har ya mutu ba Wanda zai tab'a sani. Isowar Aneesa da kamshin turaren daya daki hancinsa yasa shi sakar mata murmushi ba ruwan so da tsufa ko yarinta Jin kansa yake Kamar wani matashin Saurayi suka hau hira da yake kuma akwai wayewa sosai a tare da Alhaji Salis tuni ya maida kansa yaro a wajen Aneesa Wanda daga yanda take magana aurensa babu gudu
Chapter 4 · 0% Book details