Sashe 6
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fadawa Aunty Mami ita kuwa ta ringa min fada akan ya nake Abu kamar doluwa mara wayo na daina haka ai bai dace na ringa bada aron Kaya ba sai dai idan nayi niyya dai na bar mata. Duk yanda naso d'aukar shawarar Aunty Mami kasawa nayi dan sai nake ganin kamar bai dace Ina da abu Luba ta tambayeni na hanata ba. A haka muka je bauchi muka yi sati biyu bayan biki na dan huta a gidanmu da su Ashraf ga cikin dake jikina da ya tafi wata biyar. Ba laifi Salis ba iya iyayena yake yiwa hidima ba har da yan uwana na Kuma ji dadi ba kadan ba. Naso barin Su Ashraf ma a gidanmu tunda hutun makaranta ake suka k'i ahaka muka dawo a motar da Salis ya aika mana duk dasu Aunty mamy Mu ka dawo da yaranta sai da muka sauka a gidanmu muka huta suka tafi muhasim tace zata zauna har sai an koma hutu zata koma gidansu itace Yar yayana ta biyu a lokacin tana da shekara goma Sha biyar. Ta girmi Ashraf da wajen shekara bakwai. Ina dawowa da kwana biyu sai ga Luba ta duro a ranar Salis bai fita ba sabida ranar lahadi ne. Koda na ganta sai da gabana ya yanke ya Fadi. Dan less dina data ara shine a jikinta. Nasan Salis indai yaga less dinan a jikinta sai na Sha fada dan kwanaki da ta sako wani atamfata da ta ara data tafi sai da ya tambayeni nace masa tana da irinsa ba nawa bane yace "Aa toh dan da nakine wlh sai munyi fada kinsan wanan kawar taki bata da hankali Ina tausayawa Wanda tsautsayi zai saka ya aureta" Murmushi kawai na Masa a lokacin dan har a raina bana Jin dadin yanda yake Mata. Tana shigowa nayi sauri na mike na fara k'ok'arin janta dan mu Shiga d'akin Yara. Ai ba muje bakin k'ofa ba naji Muryar Salis a bakin k'ofar d'akina Yana kirana gabana ya yanke ya Fadi na juya a hankali ita kuwa Luba ko a jikinta ta juya itama tana "aa likita bokan turai ashe kana nan? Bai amsa ba naga ya fara Mata kallon sama da kasa take naga ya hade rai ya juyo ya kalleni Yana "Aisha wanan ba less dinan bane da na siya miki?Mai yake yi a jikin Luba"? Runtsa idona nayi dan Sam banso Salis yamin haka ba "Kai likita bokan turai mai dan kayanta ne Ni da ita fa dayane ko ka manta"? "Na manta me ya zaayi na siyowa matata Kaya kizo ki ara kice min ke da ita daya ne ke na siyowa ko ita? A wane dalili zan siyo wa matata kaya mai tsada sai kizo ki ara ki saka" "Dan Allah ka bari Abban Ashraf zan maka bayani" "Bayanin me Zaki min Aisha dama idan na siyo miki Kaya dan kisa kawarki kike bawa sabida wulakanci kwanaki naganta da kayanki kikace min ba naki bane irinsa ne da ita?dama baki San ciwon kanki ba Aisha an gaya Miki kudin banza ne dani? Ko an gaya miki bansan zafin kudina ba na ciri kudi mai tsada na miki dinki ki bawa wata banzar kawarki"? "Kaga dakata Mallam karka sake ka fadamin maganar banza kai har wani arziki kayi da zaka min rashin mutunci karka manta fa tare kaganmu da ita baka isa ka rabamu ba ko ni keda kayan da take dashi zan bata fin wanan har nawa kayan nan suke da zaka tsaya min rashin mutunci" "Luba mai haka kikeyi"? Nace hankalina a tashe dan naga salis idonsa ya kada yayi ja "Cire min kayana tunda ba ubanki ne ya siya ba wlh sai kin cire ban damu ki tafi ko tsirara ba wlh zan nuna miki ni din banida mutunci maza ciremin kayan nan yanzu idan kawarki bata da hankali ni zan koya mata hankali idan taga kinyi tsirara maza ciremin kayana Tunda nake da Salis ban taba ganin bacin ransa haka ba ganin ya nufomu yasa na tsaya a gaban Luba Ina "Dan Allah Abban Ashraf kayi hakuri dan Allah ka bari taje gida ta cire ta Aiko min dashi na hadaka da girman Allah" "Ai wani iirn tureni yayi yana "ba bakida hankali ba yau zan gwada miki rashin hankali har na siyi kaya da tsada ki dauka ki bawa yarinya da bata San ciwon kanta ba ta kashe aurenta sabida babu kuma har tana da bakin ta ringa gaya min magana ciremin kayan nan yanzu ki bar gidanan" Yace Yana fincike mayafin jikinta na saki ihu. Present Luba "Asabe kinsan dai ban yarda da wani asiri asirin nan ba ko to yau Hindatu ta kaini bango inaso na kawo karshen zamanta a gidan Alhaji kinsan banda Ina da zuciya mai kyau da har Aisha na rabasu amma Hindatu dai inaso kije wajen mai miki aiki a raba ta da Alhaji inaso Yana dawowa ya danna mata saki uku mu cigaba da Zama nida Aisha da ta zama hoto sabida kishi" "Luba kenan ai kece tun farko kika bar ta ta sake haka har ta raina ki ai idan haka kikeso tare zamuje wajen mallamin" "Aa ba wani zuwa da zanyi nidai zan baki kudi ayimin aikin kawai Alhaji na dawowa ya saki Yar iska" Ta zuge Jakarta ta d'auko kudi ta bawa Asabe ta mik'e tana "bari naje gida kafin ta kira Alhaji tace masa na fita" Har bakin motarta ta rakata ta shige tana sai sunyi waya. Alhaji Salis... MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4500 Mg's beauty kit Karamin kit 12k Body soap Facial soap Body cream Face cream Glow oil Pink lip balm Flawless skin beauty kit Babban kit 20k Body soap Facial soap Body cream Face cream Scrub Glow oil Pink lip balm Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same, Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* *Page 5* Alhaji Salis A lokacin daya je ya samu mahaifin Aneesa akan turo manyansa izini ya bashi akan ya turo dan Aneesa tace ita tana San shi Kuma mahaifin Aneesa ya dan yi bincike akan Alhaji Salis bai ga Yana da wani matsala ba. Sati ukun da yayi niyyar yi ya fasa ya d'auko hanyar gida dan ya fadawa Iyayensa ko da wasa bai tab'a kawowa kansa sake aure ba, hasali ma addu'ar sa kullum bai wuce Allah ya raba sa da Luba da Hindatu cikin sauki ba, ya zauna da Aisha uwar yayansa Wanda tunda ya aureta sai dai Santa ya karu a zuciyarsa sai gashi kaddara yasa ta maida shi hoto shi yasan akan dole take zaune dashi sai gashi kaddara ta sake hadasa da Aneesa dayaji Santa a zuciyarsa kwatankwacin irin san da yake yiwa Aisha har a yau da yake da manyan Yara Allah ya hore masa lafiya Yana bukatar nutsuwa a rayuwarsa sabida k'in da Aisha take Masa yasa baya samun nutsuwar da yake so a wajenta tunda shi kadai yake kidansa yayi rawarsa Hindatu da Luba kuwa baya kaunarsu ballantana yaji a zuciyarsa Yana samun nutsuwa dasu, hasali har fargabar kwanansu ya zagayo yake,ko a yanzu da yake san auren Aneesa kasan zuciyarsa cike take da fargaba da tsoro dan Luba ba k'aramin daga masa hankali tayi a auren Hindatu ba ko tunawa baya so yayi kalar cin mutunci da ta masa, tayi dambe kuwa da Hindatu tun kafin ma ya aureta yafi a kirga Inda yake dan samun sauki shine Hindatu itama ba kanwar lasa bace sau tari Yana so ya samu ko wata daya ne a gida ya samu lokaci da yaransa ya samu ya cigaba da rarrashin Aisha sai dai bai isa ba dan tashin hankali Luba da Hindatu ke saka shi tafiyar da bai shirya ba. Ko daya iso garin katsina sai da ya fara zuwa gidansu mahaifinsa shekara biyar kenan da rasuwarsa mahaifiyar sa ce kawai ta rage masa. Sai da yaci ya koshi ya fada mata Auren da ya keso ya Kara. Sai da ta jima bata yi magana ba kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu Aure zaka sake yi Salisu? Yanzu baka girma da Aure ba? na dauka zaka cemin Afrah ma aka sawa rana, mai zakayi da Aure yanzu tsakani da Allah Salisu? matan ka gasu nan har uku banda tashin hankali da kake so ka Kara karowa kanka tunda ga lokacin da ka tsiri aure aure kayi bankwana da farinciki Aisha dai itace matarka ta rufin asiri daka tashi mata sakayya sai ka auro kawarta Kai ma tunda kayi auren ka sake wani baka Kara samun kwanciyar hankali ba baka tsaya ma a gidanka ba yanzu kana zancen dauko aure anya Karin auren nan naka Mai yuwa ne kuwa? "Hajiya ya zanyi banida bambancin da Wanda bashida aure shekara da shekaru Ina bawa Aisha hakuri ita kawai nake Jin dadin zama da ita kema wai a haka arzikinki naci Aisha take zaune dani har yanzu. Luba da Hindatu kaddara tasa na aure su hajiya auren nan da zanyi wlh na dolene kawai da ace Aisha zata yafe min laifin da na mata wlh da ba wani aure da Zan sake to ya zanyi kimin addua kawai dan ko na auren ba gida daya zan ajiye su ba yarinya ce ma wacce zan aura bata fi Sa'ar Aliyu ba" "Kai yanzu sa'ar Yar cikinka zaka auro cikin manya manyan