Sashe 16
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tazo ta rabaki da mijinki da tun bashida ko sisi kike tare dashi taya zaki bar mata mijinki?Ina zaki Kai yaranan ki bar mata gidan ita kadai bayan dake aka Sha wahalar ya zama abinda ya zama a yau kinsan mutane basa tsoron Allah wlh karkiyi mamaki asirce shi tayi ya aureta kiga fa ba ke kadai ya boyewa ba har mu da muka tsugunna mu ka haifeshi bai fada Mana ba dan haka kiyi hakuri badan na isa ba ko Zan tilasta miki sai dan girman Allah da yaranki kiyimin wanan alfarmar insha Allahu idan dai har ba dan Allah akayi auren nan ba muna nan dake sai Kinga yanda zasu rabu bare abu da cin Amana kiyi hakuri kinji mamana bari ma na durkusa miki ai bazan yarda nayi Asarar suruka irinki ba" Sai ta fara k'ok'arin tsugunnawa na rukota da sauri Ina "Dan Allah ki bari hajiya" Har ga Allah ta d'aureni da jijiyoyin jikina bana kaunar Salis ban hararo yanda wai zanyi zaman kishi da luba ba,bansan da wane idon zan Kara kallon Salis a matsayin mijina ba domin babu digon kaunarsa a raina. Kuka na naci na gode Allah dan wlh baa san raina zan koma gidan Salis ba. Mahaifin Salis ma yasa aka kirani ya Kara bani hakuri ya bawa yayana ya min nasiha akan masu hakuri zanga sakamakon biyayyar da na musu na yarda zan komawa Salis din. A haka suka Mana sallama suka tafi akan karshen sati zan koma gidana. Yayana shima ya Kara bani baki Aunty mamy kuwa itama baa barta a baya ba ta ringa bani shawarwarin yanda zan jawo hankalin Salis wajena itama tasan Luba asiri ta Masa ya aureta idan ba haka ba ita bata ga mai zai yi da wata Luba ba. A ranar lahadi na koma gidana Salis sai rawar jiki yake ya Zama hoto a wajena domin babu kaunarsa a raina zan sauke masa duk wani hakkinsa daya rataya a wuyana amma batun mu koma Kamar da babu domin Salis da luba sun min raunin da bazai tab'a warkewa a zuciyata ba. Magiya Kam da rarrashi haka ya cigaba da min Inda ya sakomin zancen komawa abuja ya siya wani gidan daban da Zan zauna inyaso Yara sai ya sama musu wani makarantar idan anyi hutu sai mu ringa zuwa Na girgiza masa Kai akan ba zanje Abuja ba zanyi zamana anan yaje ya zauna da Luba a Abuja ai inaga dama ban dace da zaman abujan ba shiyasa bai tab'a tunanin ya tafi dani ba inda yaga ya dace dani ya ajiyeni ya barni da yayana kawai anan" Na lura Sam baiji dadin maganata ba ya hau min rantse rantse ba haka bane na share shi ban Kara bi ta kansa ba. A daki daya dai muka ringa kwana kafin ya tafi Ina kallon yanda yake boye boyen waya nasan Luba ke kiransa wlh sai naji bana Jin haushi ko wani kishi dan dagaske bana Jin komai a kansa. Duk yanda yaso mu koma kamar da abu ya faskara shopping kuwa har da na banza. Ana washegari da zai koma Abujan da yamma naga ya shigo da wata jar mota karama daidai na mata nidai tsakanina dashi idone hirar ma shi kadai yake yi. Ta window tsakar gidan na gane bada motarsa ya dawo ba Sai da ya shigo yaci abinci ya zauna a gefen kujerar da nake zaune ya ajiye mukulin mota akan cinyata Yana "Bansan mai zan miki na faranta miki ba Aisha banaso na tafi batare da naga dariyarki ba banaso na tafi batare da ko sau daya kin min hira ba ga mukulin mota nan naga karamin mota daidai na Mata na siyo miki burina naga na goge laifin da na miki Aisha komai ya wuce dan Allah" "Ina ganin Luba ta fini bukatar motar nan ko dayake kila ka dade da siya mata da baka wahalar da kanka wajen siyamin ba dan bana wani bukatar ta tunda ni ba ko'ina nake zuwa ba" "Wlh ban siyawa Luba komai ba ke Kika fi cancanta na siya miki shiyasa na siya miki dan Allah ki daina hada kanki da luba na rokeki da girman Allah dan ba matsayinki daya da ita ba" Gyada masa Kai kawai nayi burina ma ya bar gefena wlh ban sake ganin farinsa ba ko duk duniya zai ajiyemin bazai tab'a burgeni ba. Washegari ya dau hanyar Abuja bayan ya ajiye min kudi mai yawa akan Nan da sati biyu zai dawo. Luba Kamar tayi karamin hauka a lokacin da taga Salis ya daga hankalinsa akan Aisha har marinta yayi sabida ta nana Aisha da kasa a lokacin da ta kawo mata mari. Sai gashi tunda ya tafi katsina fiye da sati biyu bai dawo ba kamar ta mutu dan azabar kishi ko ta kira Salis din baya d'auka hakan ya Kara daga hankalinta Inda ta fara shirye shiryen biyo shi sai gashi ya dawo fuskar nan tashi a hade bakin cikinsa mai yasa ta tona musu asiri. Koda ya dawo banza ya bawa ajiyarta ta ringa masifarta ita kadai. Abincinta ma ba ci yake ba abu kad'an zata ga ya dau wayarsa ya Kira Aisha da wayar zai karaci ringing bata d'auka ba. A haka zata bi wayarsa daddare tana karanta messages din da yake turawa Aisha kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,abinda ya fara daga Mata hankali bai wuce sati sati da yake tsirar tafiya katsina ba sai ya shafe sati biyu uku bai dawo ba. Tuni taji zaman abujan ya isheta wani dawowa da yayi ta sako shi a gaba akan itama zata koma katsina da zama bazata yarda da wanan cin amanar da ake mata ba. Ta karfi da yaji ya amince zata koma katsina ya sama mata karamin gida daidai ita. Sai dai tana ganin gidan ta dage bazata zauna ba sai dai ya dawo da Aisha gidan ya maidata wancan katon gidan idan bazai iya ba gwara ya hadesu. Ba karamin tashin hankali suka ringa da Salis ba dan Salis bayaso ya hada luba da Aisha a gida daya sai yake ganin idan Aisha tana ganin Luba a gidan tamkar zai kara jawowa kansa ne a wajenta. Hakane yasa ya sake nemo gidan da yafi gidan girma amma Luba ta Kara dagewa akan ita yanzu bataso ma tafi so su zauna gida daya da Aisha dan tafiso duk abinda akeyi ya zama tana gani Kar ma Salis ya ringa cutarta Yana cin amanarta. Har kudi Salis ya bata mai yawa dan ta hakura ta zauna a gida daban taki akan dole ya tari Aisha da maganar hankalinsa a tashe sai dai ga mamakinsa Aisha cewa tayi su biyun bata da matsala dasu ita samant yaranta take Luba ba kishiyarta bace ba ita ai bata da mijin yanzu" A takaice da haka Luba ta dawo gidan aka ware mata part din da bai kai na Aisha girma ba. Tunda kuwa ta dawo gidan bata da burin daya wuce taga ta yiwa Aisha abinda zai saka ta zuciya ta sa Salis ya saketa sai dai haka zata karaci abin ta Aisha bata tab'a tankata ba hasali sai ta kusa sati bata sa Aisha a idonta ba a lokacin da ta gano Jan motar da take gani a tsakar gidan na Aisha ne ba karamin yak'i akayi ba dan sako Salis tayi a gaba akan lailai sai ya siyo mata itama, Salis kuwa ya rantse akan bazai siya Mata ba kullum cikin tashin hankali da fada Idan suna yi Aisha bata yi kamar tasan me suke yi kasan ranta Kuma ta fara yarda da zancen hajiya da Aunty mamy akan asirce shi Luba tayi dan da hankalinsa bata Jin zai dauki rabin iskancinta. Ganin Abu yak'i ci yak'i cinyewa yasa ta d'auko mukulin motar ta bawa Ashraf akan ya Kai Mata dan taci kwalar rigar Salis akan ba inda zaije sai ya siyo mata nata motar. Ashraf kuwa Yana zuwa yace ga mukulin mota inji Aisha ta wufce mukulin da sauri tana gwara da aka kawo mukulin da anyi tashin hankali a gidan. Koda Salis yaje ya samu Aisha akan mai yasa tayi haka ce masa tayi bata bukatar motar indai akan motar suke zubar da mutuncin su a gaban yaranta gwara ta bata kawai. Kwana biyu a tsakani Salis ya siyo motar da tayi biyun wancan a tsada ya Kara kawowa Aishan Luba kuwa Kamar ta mutu dan bakin ciki. Duk takalar Aisha da take da fada da laben da take Mata bata tab'a bi ta kanta ba a haka har suka shekara biyu Allah ya kawo rabon haihuwar Aliyu wata uku a tsakani itama Luba ta haifo danta namiji aka sa Masa Abdul. Kiri kiri take ganin rawar jikin da Salis yake akan Aisha da ta maida sa baho sosai take kishin Aisha ba yanda zatayi ne. Aisha ma bata bi ta kanta ballantana su yi tashin hankali da ita. A irin wanan lokacin Salis yazo da zancen Karin Auren Hindatu Yar Mai gidansa da ya Masa hanyar aikin NGo dan shi ya nemi daya auri Hindatu dan ta gama makaranta ba mijin aure Salis bazai iya ce masa Aa ba baya kaunar Hindatu amma a haka ya karbi tayin aurenta. Luba kamar ta hauka ce dan kishi, Salis kuwa ya zagu haka ta nemo gidan su Hindatu taje tayi rashin mutunci inda sai da ya Kai su ga dambe har police station. A lokacin Hindatu taso ma ta hakura da auren sai kuma taga idan ta hakuran Luba taci galaba akanta. A haka akayi auren Hindatu da Alhaji Salis ana zuba tashin hankali a gidan Aisha kuwa tuni ta Kara komawa gefe ta kawo Ido ta zuba musu ba ranar banzan da basa zage zage da Hindatu ko ayi dambe a gaban Yaya suna kallo wanan kenan. Yanzu Kuma mun dawo labari Dangin Salisu da hajiya Tarba mai kyau suka yiwa dangin Aneesa Inda sai a lokacin hankalin mahaifiyar Aneesa ta Dan samu kwanciyar hankali da taga mahaifiyar Salis din tana da mutunci da alama baza'a samu matsala da ita ba matansa ne dai bata sani ba hakane yasa bayan sunci sun Sha lokacin an Kai Aneesa d'akin hajiyar dan da Magriba zata kaita gidanta duk da gidansu Salis din kato