Sashe 15
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nace Ina fashewa da kuka. Yayana ya zauna a gefena Yana sallati tamkar yanda Aunty Mamy ta ringa sallati "Aisha kanki daya kuwa mai yayi zafi haka Mai ya hadaku kike neman saki a wajensa" "Yaya Salisu yaci Amanata ya hainceni Yaya Aure yayi har tsawon shekara guda bansani ba ya Kuma rasa wacce zai Aura sai kawata Luba" Hada baki sukayi wajen cewa "Wacce Luba"? Na Kara fashewa da kuka Ina "Luba kawata Yaya Luba dai da kasani har sun haihu jiya suna ban taba sani ba ace duk matan garin nan dan kawai ya wulakantani ya rasa wacce zai aura sai aminiyata da ta san sirrina wlh Yaya na gama aurensa"........ *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* *Page 9* Aisha Kuka na cigaba da yi Ina Jin Aunty mamy na cigaba da sallati yayana sai da ya dau tsawon mintuna kafin yace "Salisu dai mijinki shi ya Auri Luba kawarki har tsawon shekara daya baki sani ba"? "Eee yaya ban tab'a sanin suna soyaya ba duk na d'auka aiki yake yi a Abuja bansan Luba ya aura a b'oye ba ya barni anan Yaya Ina fama da Yara shi Kuma ya Kai Luba Abuja Yaya idan Luba zata iya cin amanata ya dace Salis yaci amanata wlh bai tab'a nuna kaunarta a gabana ba kullum cikin kusheta yake tsana kawai yake nuna mata a fili ashe soyayya suke bansani ba sai ya kwashi wata kafin yazo wajena Yana wajen Luba,idan yazo haka zan ga ana ta kiransa yacemin ana nemansa a asibiti a daddafe yake sati daya bashida lokacina bashida na yaransa ashe Luba ya aura" "Na dade Ina fada miki Aisha ban yarda da kawar nan taki ba a ranar da kuka tare a sabon gidanku idan baki manta ba har daki na kiraki na fada miki sau biyu Ina Kamata tana kallon mijinki kallo irin na soyyaya har ta zauna tana fada miki ita irin Salis take so ta samu ta aura a fakaice har tana baki dace da gidanki ba ita ta dace da gidan Kika sake mata ba inda bata Shiga a gidanki sau nawa na Miki fada anan,yanda Kika San Mara wayo haka Kika maida kanki a wajenta ke gaki bakya so tace bakida mutunci sabida kunyi kudi ai ga irinta nan duk yanda kike da ita ta zage taci amanarki Yan uwanta Suma basuji kunya ba suka hadu aka ci amanarki yanzu Yan uwansa zasu ce basu san ya Kara Aure bane"? "Basu sani ba Aunty mamy dan a boye ya aureta wai da yarjajeniya baza'a su fadawa kowa ba nidai Aunty mamy ki fadawa Yaya wlh bazan koma gidansa ba ya karba min takarda ta tunda har ya fifita Luba a kaina wlh na bar mata shi" Yayana Allah ya kyauta kawai yace ya fice daga d'akin na cigaba da kuka Ina nadamar duk saken da nayi da Luba tarin Abubuwan da nayi mata sakayyar da zata min kenan har ta haihu ya hada mata taro ya Kai abokanansa da matansu gidan suka Zama kawayen Luba ni da nake matarsa bansan abokanan aikinsa sosai har muyi wani muamalla da matansu ba na tuno yanda Luba ta goge tana ta kyalli da alama ba karamin kudi Salis ke kashe mata ba ashe duk labaran nan da luba ke bani Salisu ne har yan uwanta suma dan sunji kudi suka hadu aka daura Auren cin Amana dan idan Salis ya tashi zakkan kayan abinci na azumi wlh mai shegen yawa nake sawa akai gidansu luba haka zasuyi tamin addua ba gori ba ba wanda ban yiwa dinki a gidansu ba har mahaifinsu ashe har suma zasu yarda su daura auren Salis da luba da arziki a gidan wasu gwara a nasu kenan" Na Share kwalar da nake wahalar da kaina wajen sharewa dan ba daina zubowa zaiyi ba. Dak'yar Aunty mamy ta tilasta min na Sha tea yayana ma na tsaye a kaina sai cemin yake sai na dorawa kaina hawan jini sabida namiji shi dai bazai min dole na zauna da Salis ba amma shi baiga abin daga hankali ba tunda ba haramun bane sai dai ace ana barin halak dan kunya,Kuma Salis bai kyauta da ya boye min ba da ya fadamin ai yasan bazan hana ba. Karfe bakwai Ina daga d'aki su Ashraf zagaye dani a kwancen da nake Nana na kwance a jikina duk yarana ma ba mai makale min Kamar ita wlh Ina kaunar Nana yarinya tausayi take bani idan na tuno ba'a san waye mahaifinta ba ban tab'a sallah ban roki Allah ya tona asirin wayanda Suka yiwa muhasim fyade ba da yanzu tana gidan mijinta a mutunce tamkar yanda Khadija tayi aurenta tunda su biyu ne kawai Mata a wajen Aunty mamy. Sallamar Salis naji a tsakar gidan haka yasa na runtse idona wlh muryarsa da naji ya Kara tasomin da wani tsananin bakin ciki ko kaunar ganinsa bana yi jiya da yayi niyya ai zai hau wani motar ya biyoni amma ya koma wajen matarsa sai yau yaga damar biyoni sabida banida wani matsayi a wajensa. Ina jinsa da yayana a tsakar gidan duk Yana bada hakurin abinda ya faru na auren da yayi a b'oye akan kaddara yasa ya auri luba da Kuma rabon dake tsakani baya so ya fada min ne dan kar ya daga min hankali,dan Allah a bani hakuri yasan bai kyauta ba. Ina Jin yayana na fada Aunty mamy na sa bakin cin amanar da yamin ba Haushin auren suka ji ba ya rasa wacce zai Aura sai luba Kuma har tsawon shekara daya badan Luba ta fadamin ba da haka zasu ninkeni kenan inta tunanin aiki kawai yake a Abuja. Ina ji yana ta bada hakuri Yana ya karbi laifiinsa ayi hakuri,kaddara ta riga fata yayana yace shi dai bazai iya min dole ba ya Shiga daki ya Sameni idan zan iya koma masa shi bashida matsala amma tilasta min ne bazai yi ba. Ina jin lokacin ya nufo d'akin rashin kwarin jiki ya hanani mik'ewa na Shiga bandaki na rufe k'ofar yarana kuwa tuni suka zagaye shi ban bud'e idona ba dan banasan ganinsa. Sai da duk ya gama yiwa yaran Wasa yace su fita su bamu guri. Ina jinsa Yana k'ok'arin d'aukar Nana nasan bazata yarda taje wajensa ba dan Kara kwanciya tayi a jikina ya sa hannu ya d'auki ummi. Ya Kira Sunana yana "Gani a durkushe a gabanki Aisha dan girman Allah kiyi hakuri ki yafemin bansan yanda zaayi ki gane kaddara tasa na auri Luba ba, ba san raina haka ta kasance ba dan Allah ki yafe min Aisha ki dubi girman Allah da yaran mu kiyi hakuri,na yarda idan kin hakura zamu koma Abujan gabad'aya" "Wlh wlh na gama auren ka ba abinda zai saka na tab'a koma maka,da ka san tsanar da na ma wlh da baka Soma doso Inda nake ba, Salis Luba fa Luba kawata ka Aura ka d'auketa ka kaita Abuja ka munafirceni ka maidani wawiya a gabana ka nuna ka tsaneta idan na maka maganarta kace bakaso,ashe soyayya kakeyi da ita duk matan garin nan ka rasa da wacce zaka hadani kishi sai luba,ka d'auketa Ka kaita Abuja kukayi zamanku Kuna Shan soyayya ni Kuma ka barni da gadin gida da yaranka idan kazo sati daya sai ka juya ka tafi Wlh ban yafe maka wanan cin amanar da kayi min ba ni na yafe mata Kai kuje can ku karata ka bani takarda sakina" Na karashe Ina fashewa da sabon kuka kirjina wani irin ciwo yake min Luba fa kawata ita Salis ya Aura. Hakuri ya cigaba da bani Yana magiya da rantsuwar kaddara tasa ya aureta shi baya Santa wlh shi bai hada san kowa dani ba Sai a lokacin na bud'e idona banida ma kwari sam dan ji nayi jiri na dan dibana na Mik'e zaune Ina "Kace baka santa ka aureta kayi Mata ciki ta haihu kayi taro da gayya ko? A Abujan mutanen ka waya sani a can ita Luba da ta sansu duk baka santa ka hadata dasu ko"? Salis ba dai kace baka santa ba toh wlh idan kana so na dawo gidanka sai ka rubutawa Luba saki uku yanzu a gabana a cikin mu biyu sai ka zabi daya idan ka zabi rabuwa da ita sai na zauna da Kai idan karin auren kake so sai ka Kara da koma wacce ce idan Kuma ita ka zab'a sai ka daina mafarkin ni Aisha zan dawo gareka" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aisha ki rufamin asiri wanan hukuncin naki yamin tsauri wlh bana kaunar Luba ki yarda Zan saketa anan gaba amma Banda yanzu dan Allah dan Annabi" "Tashi ka fita Salis idan ka saketa ko nan da shekara Ashirin ne sai na dawo gareka amma bazan hada miji da Luba ba" Ganin zai cigaba da magiya yasa na saka masa ihu ya mik'e ya fita sauri Yana fita na Kara fashewa da sabon kuka dan tsananin bakin ciki daga yanda ya nuna min bazai iya sakinta ba nasan ba karamin so yake yiwa luba ba ai tunda har ya Kai ta Abuja nasan matsayina a wajensa. Haka Salis ya ringa sintirin zuwa ba dare ba Rana har yaransa yasa suka ringa rokona suna min kuka ganin yayana shima yace masa ya daina matsamin ya sakeni kawai tunda ya nuna yafi San Luba yaje ya zauna da iya lubar kawai Yasa hankalinsa tashi dan ya tabbata dagaske yayana bazai tab'a sa baki na dawo gidansa ba Washegarin ranar sai ga Hajiyarsa da mahaifinsa sun zo. Mahaifinsa da ake cewa baffa na zaune a palo Hajiya Kuma ta shigo d'akin da nake kwance. Har ga Allah tamkar 'ya ta d'aukeni nasan tana kaunata tana shigowa ta hau cewa "Ashe abinda yaron nan ya aikata kenan Aisha"? Sai hawaye suka hau zubo min ta zauna tana "wlh wlh bamu sani ba sai jiya daddare yaje ya na fada Mana abinda ya aikata har ace Salisu yayi Aure batare da sanin Iyayensa ba ya Kuma rasa wacce zai aura sai kawarki wai ashe har ta haihu ma wlh bai kyauta ba jiya har sai da na buge shi mamana kiyi hakuri matakin da Kika d'auka yayi tsauri taya zaki yarda wata banza