Sashe 65
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tashe sai cewa take mai tayi tana cewa Aisha "wane Sharrin kike bibiyana dashi duk da na rabu da mijinki" Aisha ba karamin k'ok'ari tayi wajen danne abunda take ji a ranta ba,bata tab'a tunanin zata yi ido biyu da Luba bata shaketa ba,tunda Suka gano Luba na da sa hannu Ashraf ya hau nemanta,ba inda basu dubata ba itama kanta burinta taga Luba tazo hannu hakane yasa ta matsawa Ashraf akan kamo Luba har sai da a garin bincike suka gano Luba na gidan Habiba dan mahaifin ta ne ya fada musu da suka je gidan. Yana Kiran Aisha tace bari ta fito tafiso a kama Luba a gabanta a cikin mota Ashraf ya ringa rokonta akan Kar tayi wani abu ta bari hukuma suyi aikin su. Luba kuwa har suka isa station jikin ta rawa kawai yake da ace tasan Yan sanda zasu kamata da bata zo bauchi ba a cikin Abubuwan da ta aikata bata san wane asirin nata ya tonu ba, Rabin Abubuwan da ta aikata tasan ba wanda yasani sai Asabe,Asabe ce kawai zata iya tona mata asiri,ta kuma dade da aika Asabe lahira da wanan tunanin taji hankalin ta ya dan kwanta dan koma mai ake zargin ta aikata tasan basuda shaida idan ta kafe dole su rabu da ita. Da isarsu station aka watsa ta bayan canter. Awa daya a tsakani wani dan sanda ya daka mata tsawa akan ta fito. Fuska a daure ta fito dan taga alamar sai ta hada da fuska da borin kunya Koda aka karanto mata zargin da ake mata dan sanda ya hada da "Karki wahalar damu ki wahalar da kanki idan har kinsan kina da hannu a abinda ya samu yarinya nan kifito ki fada mana gaskiya ba sai kin wahalar da mu ba ta hakan zaki samu sausauci a hukuncin da zaa miki ya akayi kika karkatawa yarinya nan wuya da baki"? "Officer wlh banida hannu a abinda ya samu yarinya nan nidai nasan tsohon mijina ne yayi mata fyade daya ga asirinsa zai tonu shine ya karkata mata baki" "Ke ya akayi kika san shi ya karkata mata baki, kina wajen ya karkata mata baki"? "Bana wajen amma nasan shi ya karkata mata baki" "Karki wahalar damu ki fada mana gaskiya idan kinfi san Kuma a saka ki fadi gaskiya ta karfi da yaji sai mu saka ki" Luba ko gezau batayi ba ta dage akan batasan komai a Kai ba su kamo Salis shine ya karkata wa muhasim wuya. A takaice duk da uban azabar da suka ringa ganawa Luba,kafewa tayi akan bata da hannu akan case din Salis ne ya karkata wa muhasim wuya. Ashraf kuwa yariga da yasan wacce luba a binciken da ya karayi ya Kara gano mugayen halayen Luba. Burinsa yanzu ta amsa laifinta ta Kuma fada musu da me ta karkata wa muhasim baki. Tuni ya nemi a mik'a case din kotu dan shi zai tsaya akan case din dan Aisha ta dage masa burinta kawai tasan mai ta yiwa muhasim wuyan ta ya karkace. Kotu Cike take dam da jama'a a cikin wayanda suka zo kotun har da Yaya mustapha Aisha da Aunty mamy,Salis ma baa barshi a baya ba sai dayazo. Dan burinsa kawai gaskiya tayi halinta,shima a yanzu ba wacce yake mugun zargi sama da Luba. Sai da aka gabatar da Sharia wajen biyu kafin a kira case din Luba da yan sanda biyu suka sakata a tsakiya A cikin sati guda duk ta fice a hayyacinta kamar ba ita ba,tana kallon yanda Salis ke jifanta da mugun kallo Kamar ya jawota ya rabata da ranta. Sai da ta shiga wajen da masu laifi ke tsayawa ta tsaya duk da jikinta rawa yake haka ta dake dan ko bindiga zasu saka mata bazata tab'a karbar laifinta ba a yanzu ma burinta a Kama Salisu suyi zaman yarin tare. Koda aka karanto zargin da ake mata Ashraf ya nemi izini a wajen alkali sabida ya Mata tambayoyi dakewa tayi ta Kara fada musu Salis ne ya karkatawa muhasim baki sabida Kar ta tona masa asiri asan shi ya mata fyade Ashraf ya saki murmushi yana "Mallama luba kikace tsohon mijinki shi ya karkata mata wuya sabida rufin asirinsa shin kina wajen ya karkata mata wuya ya akayi kika san shi ya karkata Mata wuya"? "Yanda akayi nasan shi ya aikata mata wanan danyen aiki a lokacin kafin muyi aure Ina yawan zuwa office dinsa dan mu gaisa,toh a lokacin baya wani bani fuska lokaci lokaci idan na bushi iska nakan je dan mu gaisa a irin wanan lokacin watarana naje kafin na Shiga ma asibitin naga ita muhasim ta fito daga asibitin da gudu tana kuka inda take hankalina ya tashi dan nasan yarinya tunda Yar yayan kawata ce take nabi bayan yarinya dan naji mai ya sameta ta fito daga asibitin tana kuka. Koda nabi bayanta sai da na rarrasheta da kyar na samu ta fadamin tsohon mijin nawa shi ya mata fyade ta Kuma gano tana d'auke da ciki,shine ya dage akan sai ta cire ko ya kasheta idan ba haka ba zai mata abinda bazata samu bakin magana ba a lokacin kwantar Mata da hankali nayi nace Kar ta damu ba abinda zai iya mata ni zan masa magana. A washegarin ranar naje na same shi a office na nuna masa nasan abinda yayiwa Yar yayan matarsa dan haka idan baiyi wasa ba sai na tona masa asiri. Hakuri ya bani akan Kar na tona masa asiri,jinsa kawai nayi a lokacin dan na yanke a raina Zanje na samu iyayen yarinya kawai.na fada musu. Kwana biyu a tsakani yarinyar tazo ta sameni tana kuka akan Salis yace ko ta yarda ya zubar mata da ciki ko ya kasheta daga islamiya ma tazo ta sameni dak'yar na rarrasheta akan ta tafi gida a gobe sai na tona masa asiri. Washegari ban kai ga naje gidansu yarinya ba naji labarin an tsinceta a bayan makarantarsu an karkata mata baki take nasan ba wanda zai iya aika aikar nan sai shi, a ranar naje na same shi a office dinsa na nuna masa nasan shi ya karkata mata wuya dan rufin asirinsa yanda yaga na dage zan sanarwa yan sanda yasa yayi tamin magiya akan na rufa masa asiri sharrin shaidan ne yanda akayi nasan shi ya karkata Mata wuya kenan" Ashraf gyada kansa yayi Yana "Hajiya Luba ya akayi duk yanda kike da kawar taki baki fada Mata abinda ke faruwa ba kike b'oye mata sanan kince yarinya zuwa take wajenki ta fada miki duk yanda tayi da shi tsohon mijin naki,ya akayi bata zabi ta sanarwa kowa ba sai ke" "A lokacin banaso na raba kawar tawa da mijinta shiyasa ban fada mata ba" "Toh mai yasa baki sanarwa Iyayenta ba"? "Anan ne nasan nayi kuskure da ban fada musu ba" "A lokacin da abin ya faru kunyi Aurene ko bakuyi aure ba"? "A lokacin bamuyi aure ba sai da abin ya faru mukayi Aure" "Ya akayi kika yarda kika auri wanda ya iya yiwa yarinya fyade har ya karkata mata baki bayan Kuma kinsan Yana da irin wanan mugun halin Kika yarda kika aureshi daga Kuma labarin da kike bamu tamkar dai shi tsohon mijin naki mijin ka warki ne"?ke kinsan shi ya aikata irin wanan danyen aikin bakiyi kararsa ba kike nemi ki rufa masa asiri sabida kema ki samu cikar burinki ya aureki ko"? "Aaa a lokacin gani nayi idan na fito na fada zan Zama silar da zan rabashi da kawata shiyasa ban fada ba" "Shin a gidanki muhasim ke zuwa ta Sameki ta fada miki halin da take ciki ko kuwa ke kike zuwa wajenta dan kisan halin da take ciki"? Luba shiru tayi tana kallonsa Ashraf ya gyara tsayuwarsa Yana kallonta dan so yake ya biye mata kafin ya fito da shaidun da yake dasu akanta..... Wlh nayi typing nayi mistake na goge sai da na sake wani sorry for the late update Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b Mai bukata should Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Team glow *WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN* *+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA* *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *PAGE 36* "Ba gidana take zuwa ba muna dai had'uwa da ita a hanya ne" Ashraf murmushi ya saki yana "yanzu kinyi magana biyu kenan kince yarinya tazo ta Sameki tana kuka akan shi tsohon mijin naki yace mata idan bata yarda ya zubar mata da ciki ba zai kasheta sai Kika rarrasheta akan ta koma gida zaki tona masa asiri" A ranar a hanya kuka had'u ta fada miki Kuma a wane hanya kuka had'u ta fada miki yace zai kasheta"? Luba sai ta dirirce ta rasa ma karyar da zata masa Ashraf ya juya ya kalli alkali Yana ya mai girma mai Sharia inaso a bani dama Zan kira tsohon mijin ta na masa tambayoyi" "Kotu ta baka dama" Salis bai tab'a tunanin Ashraf zai neme ya fito ba,taya Ashraf zai masa haka kiransa da zaiyi na nufin tonan asirinsa a bainar jama'a ko kad'an bayaso ana maganar yayi wa muhasim fyade. Ashraf sai da ya kara masa ido akan ya fito ya tashi jiki a sanyaye sai yaji Yana nadamar ma zuwa kotun ba haka yayi da Ashraf ba taya a bainar jama'a zaice yayi wa muhasim Fyade. Koda ya fito wajen dake kallon Inda