Sashe 39
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Luba "Asabe nice fa yanzu ni zaki wulakanta dan Aurena ya mutu"? "Auwalu kana Ina wai ka Sako min karnukan nan nace" Asabe tace tana Kara daga muryar ta Luba tsakanin mamakin Asaben yasa ta kasa motsawa dan ko a mafarki bata tab'a tunanin Asaben zata iya mata haka ba Tana k'ok'arin Magana taji Haushin karnuka a mugun tsorace ta juya ta kuwa hangosu a koshe su biyu sun dallaro Harshe sun yo wajen da take tsaye suna haushi Baa tab'a sakin karnukan sai daddare tsoron karnukan yasa ba'a fiye zuwa ma gidan Asaben ba dan tsohon soja take Aure. "Yauwa sake su,suyi mata rakiya "Tunda dai bani na kashe mata Aure ba, ita ta kashewa kan ta aure sabida rashin hankali ta doso gidana Wai a gidana zata zauna kafin komai ya lafa Kafin na ankara sai dai naji ana rangada guda. ihu Luba tasa da taga sun yo kan ta gadan gadan tayi palon Asabe da gudu,Asabe ta hankado ta tare da rufe k'ofarta. Luba ta hau zagaye gidan tana ihu karnukan na binta a guje har suna neman cafota dan sun cafo mayafin ta. Da k'yar ta samu ta shige d'akin mai gadi kafarta na gurdewa,tana Jin maigadin na k'ok'arin Mai da su cikin kejin su. Nishin azabar kafarta da gurde kawai take hawaye na zubo Mata. Shigowar mai gadin yasa ta mik'e dak'yar tana cije lebbenta dan kafarta zugi kawai yake Mata. Da dingishi ta fice daga gidan tana tafe tana hawaye ko biyar babu a hannunta kunyar ma doson gidan nasu take,akan fadan da iyayen ta suka koma yi Mata akan yanda take tafiyar da rayuwar aurenta a gidan Salis yasa ta tsiri gaba dasu sai ta ga dama take zuwa gidan nasu,a yanzu ma ta lura ido kawai suka kawo suka zuba mata, ba wani hidima da take musu burinta kawai da kansu su fito suce ta musu abu kafin ta musu Amma indai ba tambayar ta suka yi ba gani take basu da wani matsala,rabata da komai da Salis yayi yafi komai daga mata hankali Rabin dukiyar ta da take Kuma takama tana dashi Yana wajen Asabe,Asaben ma bata tsaya ta saurareta ba ta mata koran kare,Rabon da tayi tafiya a kafa haka ma ta manta, Ciwon da kafarta ke Mata yasa ta tsayar da abin hawa ta nufi gidan da zumar idan taje sai ta karbi kudin motar ta bayar. Tafiyar minti goma ya Kai ta gidan iyayenta Koda ta sauko sai taji ta kasa ma shiga gidan an tafi wata biyar rabon ta da gidan nasu,horn din da mai Napep ya mata yasa ta shige gidan da sallama. Ba kowa a tsakar gidan sai take Jin kanta Kamar wata bakuwa a baya idan zata zo ko sallamar bata yi haka take Shiga tana yatsina fuska daga tace ya taga gidan haka,ya ko ina kaca kaca ba kintsi,haka zata yi ta yatsine fuska tana fesa turaren da tazo dashi,har Kuma ta baro gidan bata saka komai a bakinta sai dai taci abinda ta zo dashi, mahaifiyarta najin ciwon abinda take yi idan ta kasa hakuri haka zata rufeta da fadan tama daina zuwa gidan ai tunda tayi kudi ta canza iyaye kawai. Mahaifin ta kuwa baya ce Mata komai sai dai yace taje gata ga duniyar nan shi dai yafi kowa Jin zafin auren Salis da tayi ba yanda zaiyi da ita ne dan bazai manta mutuncin da Aisha ta musu ba. A hankali ta kara kwada sallama taji muryar mahaifiyar ta da suke cewa Inna larai ta amsa sallamar a daidai lokacin da ta fito daga d'akin. Luba da sauri ta sunkuyar da Kai tana "Inna Ina kwana" Bata amsa ba sai da ta kalli gefe da gefenta tace "Toh ni ko dai idona ne suke min gizo ba Luba bace" Kukan da take rikewa ya kwace mata tana "Nice Inna dan Allah ki bani naira dari zan bawa mai machine" Tsananin mamaki yasa Inna bata motsa ba ta saki baki tana kallon Luba sai da Luba ta Kara cewa ta taimaka mata da darin Inna ta koma d'aki ta fito da dari a hannunta ta bawa luba. Luba ta fita ta kai wa mai machine din ta dawo ta zub'e a tsakar gida ta rushe da kuka. Har lokacin mamaki bai saki Inna ba dan a iya sanin ta Luba ma idan zata zo gidan horn ma take musu a motar ta yau Kuma sai taga lubar tazo a kafa har tana neman kudin machine a wajenta ga fuskarta a kumbure ta dade da cire damuwar Luba a ranta,ido kawai suka zuba mata dan sun san dole watarana tayi dana sanin wofintar dasu da tayi,dan bata da sama dasu din. Dakin ta ta koma tayi zamanta tana cigaba da kulla man gyada da man jan da take siyar wa. Shigowar ta da zub'ewar da tayi a gabanta cikin kuka tana "Inna Salis ya sakeni,Salis ya sakeni saki uku ya kwace komai daga hannuna ko kaya bai bari na d'auka ba" "Ashe sakin ki akayi shiya sa ki ka zo gidan nan ai na d'auka kina da gidan da yafi wanan,ashe dai muna da gidan da zaki zo? Yau dai ga ranar mu ashe,an saki hajiya ta dawo gida Allah ya kyauta" "Inna dan Allah kuyi hakuri karku yi fushi dani nasan abinda nayi ban kyauta ba" "Ai ba sai kin bamu hakuri ba hajiya ai duniyar kika zab'a ya tun ba'aje ko ina ba zaki karaya ice dai zaki iya zama a gidan da ba kintsi gidan da ke miki wari ya Kamata ma ki nemo turare karki shaki wari" Luba hawaye kawai take bata iya Kara magana ba dan tasan magana mahaifiyar ta ke kwaba mata, Inna bata Kara nunawa tasan tana d'akin ba har ta gama kulla man ta mik'e ta bar mata d'akin. Luba kuwa ta mik'ar da kafarta dake mata zugi ta buga uban tagumi ta kasa yarda da duk abinda ke faruwa da ita,bata tab'a kawowa kanta sakin da Salis zai mata idan ta tona Masa asiri ba,bata tab'a kawowa kanta dawowa gidansu tayi zawarci ba,bata tab'a kawowa kanta rasa tarin dukiyar da take dashi da duk Salis ta ke karbewa kudi tana barazanar idan bai bata ba zata tona masa asiri,bata tab'a kawowa kanta wai Asabe da ta dauke ta a matsayin aminiya ta bata fiye da Rabin abinda take dashi akan ta juya mata sabida amincin dake tsakaninta da ita zata iya murzawa idonta toka ta Mata irin wanan cin mutuncin akan ta nemi ta zauna a gidanta zuwa wani dan lokaci kila idan ta Kai ta wajen mallamanta a samu a asirice mata Salis ya Mai da ta dakinta Asabe ma bata tsaya ta saurareta ba ballantana tace ta bata kudadenta dake wajenta. Yanzu shikenan duk wani karfinta da mulkinta da duk wani takamar ta rushe shi da hannunta Mai yasa tunanin ta bai tab'a bata idan ta tonawa Salis asiri itama nata asirin zai tonu ba,mai yasa tunanin nata bai tab'a bata akan idan ta tonawa Salis asiri tamkar ta saka almakashi ta datse igiyar dake tsakanin su ne ?taya sai da ta kawo girma zata dawo gida tayi Zawarci,shikenan duk san taga ta raba Salis da duk matansa ta zauna dashi ya tashi a banza kenan itace ma zata rabu dashi,shikenan Hindatu ta samu abinda take so kenan ta bar mata gidan? Taya zata soma rayuwa agidan nan ta hau karewa dakin mahaifiyar ta kallo bashi da girma balle a samu wadatar iska. Yanzu daga Ina zata fara shikenan ta tashi ba miji ba kudi kenan ta zama bazawara kenan Luba da Aisha na zaune a matsayin matan Salis Ina da sake ya zama dole Asabe ta bata kudadenta taje ta nemi mai mata aiki ta koma gidan Salis idan komawarta bazai yu ba gwara ayi abinda zai sake su gabad'aya kowa ya rasa tama san Aisha ta gama auren sa tunda duk ta fada mata maganganun da zata tsani Salis Hindatu da Aneesa zata yi aiki akan su Asabe kuwa ta karfin tuwo sai ta bata kudinta. Haka ta zauna a daki tana sake sake har mahaifin ta ya dawo. Sai dai a lokacin da Inna ta bashi labarin sakin da aka mata ta dawo gida murzawa idonsa toka yayi akan bazata zauna Masa a gida ba taje ta nemi gidan da zata zauna ya dade ma Yana Addu'a Allah ya nuna masa wanan ranar. Luba duk yanda taso ta masa magiya da kuka haka ya watso ta waje. Tunda take a rayuwata bata tab'a tsintar kanta a cikin tashin hankali irin wanan ba wai yau itace ta wayi gari bata da komai har wajen da zata zauna babu sabida mahaifin ta ya koreta bata tab'a sanin mahaifinta na da zuciya haka ba sai yau. Bata da waya a hannunta balle ta Kira sultan ko ilham a waya a yanzu ba masu taimaka mata sai su duk da suma taga alamar Hamza ya cusa musu kiyayyrta a zuciyarsu idan ba ita ta neme su ba basa tab'a nemanta, auren Salis da tayi yasa bata damu da kudin da hamzan yayi ba har matansa sun kai biyu,sanin ba wajen da zata iya zuwa yasa ta nufi gidan hamzan da shima ba boyayye bane zata wayance da zuwa gidan akan ganin su sultan. Aisha Da ikon Allah ta isa gidan Yaya mustapha dan jirine kawai ya ringa dibarta ga azabar ciwon Kai ta ma daina kukan fili ta koma na zuci. A lokacin da ta isa gidan karfe bakwai da rabine na safe,Bata da karfin buga k'ofar sai Nana ce ta ringa buga gate din har aka zo aka bud'e. Yanayin da Umar ya ganta yasa ya saki sallati Yana "Aunty Aisha lafiya kuwa mai ya same ki"? Bata iya bashi amsa ba dan bibiyu take ma ganinsa da dafa bango ta Shiga palon ta zub'e akan kujera ta rushe da sabon kuka,wai Salis shine yayi wa muhasim fyade,Wai Nana Yar Salis ce wani irin suya take ji a kirjinta wanan cin Amana sa zalincin da Salis ya mata ya munana. Muryar Yaya mustapha da taji a kanta yasa ta bud'e idonta da suka kankance sabida kuka. Yaya mustapha kuwa hannunta ya ruko cikin tashin hankali Yana "Aisha mai ya faru