← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 71

Sashe 3

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne sai sarka da dankunne da mayafi kala biyu ganin tana ta kallon ledar yasa na fito da kayan ciki na nuna mata ta ringa juya kayan tana yabawa a cikin turamen zanin da aka kawo daga gidanmu na dauko daya na bata dak'yar ta karba tana da na barshi ita wanan haihuwar da nayi bata da abin bani. Koda tazo tafiya ma sai da Salis ya bata kyautar kudi,na rakata ta tafi. Ahaka akayi sunan Afrah banaso na sosa mata zuciyarta taji ba dadi Kaya kala biyu kawai na saka. A haka rayuwa ta ringa tafar mana daidai gwargwado Ina k'ok'arin taimakawa luba indai ta kawomin kukanta zan k'ok'arta naga na share mata hawayen ta Afrah ta tafi shekara biyu wataran Salis ya shigo gidan da takarda a hannunsa cikin tsananin murna Yana nuna min sunansa ya fito a cikin wayanda suka ci scholarship da zasu fita Kara karatun da zai zama cikakken likita. Ji nayi Kamar na zuba ruwa a kasa na sha dan murna dan duk Wanda yasan Salis yasan burinsa kenan yan uwa da abokanan arziki kuwa sai taya mu murna ake ciki kuwa har da Luba da ke fama da tsohon ciki duk ta fice a hayyacinta sabida damuwa da ta sa a ranta. Duk kudin da salis ke dashi ya ajiye min akan zai na min aike,a haka ya shirya kayansa ranar tafiya na sha kukana na gode Allah Kamar bazamu rabu ba gashi lokacin sai dai sako ba yawaitar waya ya damka amanarmu a hannun Iyayensa ya tafi. A takaice bayan tafiyar Salis da shekara biyu komai namu ya Kare kudin haya ma ya Kare gashi banaso na ringa dorawa Iyayensa nauyi dan suma suna da nauyin kannensa akansu sosai,a haka Yayana ya ringa hidima dani, ganin ni kadai ce ba Kuma a yanzu Salis zai dawo ba, yayana yace na dawo gidansa na zauna har zuwa lokacin da Salis zai dawo,dan iyayen mu suna katsina tunda yayi Aure shekara da aurensa rukona ya koma hannunsa. Yayana shi ya ringa hidima damu ya saka yarana a makaranta. Luba kuwa tana ta fama ba yanda ba tayi dan ta kashe aurenta ba Hamza yak'i sakinta har magana nayiwa yayana akan ya taimaka mata da ko jarine sabida kawai ta kwantar da hankalinta Amma duk da ya bata jarin burinta taga ta kashe auren wulakanci kuwa kwando kwando haka ta ringa Masa. Nidai tsakanina da ita shawara ne abinda nake dashi iya Karfina Kuma Ina taimaka mata dashi a haka kwanaki suka ringa juyawa zuwa sati,satika zuwa watani,watani zuwa shekaru,tunda Salis ya tafi sau biyu kawai ya tab'a Mana aike. A takaice Kamar Wasa sai gashi har Salis ya tafi shekara biyar saura Masa watani ya dawo ya turo kudi ta hannun yayana aka siya masa katon fili aka fara Masa gini. Koda na gayawa Luba murna ta ringa yimin tana "Aisha Allah ya baki wasa wasa mijinki ya zama mai kudi" "Luba kema dan kin k'i kwantar da hankalinki ne ba abinda baya wucewa mijjnki Yana nema ai watarana zai dace insha Allahu" "Hmm banga ranar ba Aisha nidai banida burin daya wuce ya sakeni dan bazan iya ba" Shirye shiryen dawowar salis na farayi dan baifi saura wata biyu ya dawo ba shekara biyar ba Wasa ba daga irin ginin da ake kerawa nasan Salis ya samu kudi ni bashine a gabana ba nidai burina ya dawo naganshi dagani har yarana munyi kewarsa. Saura sati uku ya dawo naje gidansu da yara anan mahaifinsa ke cemin ya turo kudi akan aka ma mana haya. A takaice gidan hayan ma da aka kama Mana katoton gaske kayan dakina kuwa duk na siyar dan sun zama tsohon yayi a kudin dayayi saura Wanda ya turo na cika na sake sababin kayan d'aki Kamar dai amarya yayana ya taimaka min shima dan ba karya yayana Yana ji dani. Luba kuwa sai saintyn gidan hayan take tana ai Salis ya zama mai kudi da dukan alamu saura na wulakantata na juya mata baya ni dariya ma take bani dan bana Jin ko mai Zan samu zan ari halin da ba nawa ba ni bana ma fada mata komai,yanzu dan Kar taga Kamar da biyu nake bata labari amma kullum tana tafe dole ta ringa sanin halin da nake ciki... Presently Yaran duk suna zaune a palo suna kallo Hindatu itama tana zaune a palon. Fitowar Aisha daga d'akin yasa ta saki murmushi tana "Hajiya kin fito" Murmushi Aisha ta saki tana "Eee wlh wai da so nake na leka gidan sunan na idan banje yanzu ba bazan samu zuwa ba" "Bari na saka mayafina na rakaki" Hindatu na k'ok'arin mik'ewa Luba ta fito daga dakinta tana "ke dai anyi shugaban munafikai Sam bakiji dadin rayuwarki ba wlh idan ma duk so kike ku hada kai dan ku cutar dani wlh ba abinda zaku iya min" "Allah ya baki lafiya ku tashi ku koma karamin Palo kafin ta fara kawo muku duka" "Kambalai kina nufin ni mahaukaciya ce"? "Toh da fa kina da hankaline..... MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4500 Mg's beauty kit Karamin kit 12k Body soap Facial soap Body cream Face cream Glow oil Pink lip balm Flawless skin beauty kit Babban kit 20k Body soap Facial soap Body cream Face cream Scrub Glow oil Pink lip balm Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same, Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 LUBA... *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* *Page 3* Present "Hindatu wlh taraki nake karki ga Ina kyalleki wlh zan baki mamaki" "Ke a yanzu akwai abinda zaki yi ki bani mamaki Luba ai banga abinda dai zaki yi yanzu ki bani mamaki ba, asara dai kinyi ta abin kunya dai kin aikata kowa yasani Idan kina haukarki ki daina zuwa wajena kije can ki karata ke daya" Ashar Luba ta lailayo ta fara zagin Hindatu da taja tsaki tabi bayan Aisha da ta dade da ficewa daga palon dan idan suna abin su ko tankasu bata yi har yanzu tana mamakin halin Luba. Tare su kaje sunan suka dawo Aisha sam bata bata fuskar da zata mata maganar luba ba dan tana Jan girman ta duk da Hindatu tana iya k'ok'arinta wajen girmama ta tun daga bakin k'ofa suka fara jiyo ihun ummi Yar gidan Hindatu dan yaran hindatu uku da Alhaji ummi itace karama. Da mugun gudu Hindatu ta Shiga gidan a daidai lokacin da Luba ta kara daga bulalan hannunta zata zabga mata Hindatu cikin ihu tace "wlh wlh sai na rama dukan da kika mata cikin wani irin super ta dira gaban Luba suka fara wani irin k'ok'awa. Aisha da sai a lokacin ta shigo gidan har zata wuce su ta tsaya tana "Dan Allah yaushe zaku girma ku daina abu Kamar kananan yara ko akauye ba'a irin wanan rayuwar ace kullum sai kunyi fada kunyi dambe a gaban yayanku wanan wane irin rayuwa ne"? Hindatu cikata" dak'yar Suka rabu suna hucci dan hindatu ta dan fi Luba tsayi da kib'a "Kinyi asara wai sabida kina Jin haushina kika hau dukar min 'ya toh wlh daga yau duk ranar da kika Kara tab'a min Yara Allah sai na baki mamaki" "Kafin ki bani mamaki hindatu ni zan baki mamaki" Ta shige dakinta da sauri tana shiga ta d'auki wayar ta ta nemo Asabe a waya (itace aminiyar luba) Tana dagawa tace "Asabe gobe Ina nan tafe inaso na koyawa Hindatu hankali" "Ta Kara hadoku kenan"? "Eee idan nazo zan baki labari" "Sai kinzo" Ta katse wayar tana jijjiga kafa a duniyarta bata da burin ma taga ta raba Alhaji Salis da kowa tafiso taga ta juya taga ita kadai ce a gidan bata san ya akayi Hindatu taga gadon baccinta haka ba" Past Aisha A ranar da salis zai dawo daga ni har yayana shiri mu ka tayi,duk abincin Dana san yana so na dafa masa dagani har yayana munyi tsaf damu bansan dai karfe nawa zai iso ba amma nasan a ranar zai dawo wajen karfe uku sai ga luba tazo wai tazo yiwa salis sannu da zuwa dariya nayi Ina ta kyauta,sosai nake Jin luba a raina tamkar Yar uwata tunda duk ta damu da damuwata,abincin da na girkawa salis na zuzubo mata tana ci muna hira tana bani labarin irin talaucin da Hamza ke fama dashi ko abinci ma babu a gidan,sai naji tausayinta har a raina na yanke idan Salis ya dawo naga yazo da nauyinsa zan masa magana ya taimakawa hamza. Wajen karfe biyar na yamma muka ji dirar mota a k'ofar gida. Dagani har yaran muka diba mu kayi waje da gudu shekara biyar ba Wasa ba, ai Salis bai gama fitowa bama na daka tsalle na rungumeshi ina ihun murna,dariya kawai yake Yana na barshi ya d'auki yayansa. Kaninsa sai dariya yake mana driver taxi din Kuma nata fito da akwatuna da jakankunansa kaninsa ya ringa d'auka Yana Kai wa ciki. Afrah ya d'auka yana ta fadin girman da tayi daya hannun nasa rik'e dana Ashraf nidai tunda ya sakeni kallonsa kawai nake ya balain canjawa kamar bashi ba ya zama wani dan gayu ya goge Kamar wani bature duk sai na raina ma kwalliyar da nayi na tarbarsa. A haka muka shiga cikin gidan sai da muka je Palo ya sauke Afrah ya juyo Yana kallona da alama bai lura da Luba dake rabe a gefen kujera
Chapter 3 · 0% Book details