Sashe 25
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nayi sabo ne ma taya zai nemi Yar cikinsa. A zaunen da nake akan sallaya tunanin baya kawai nake tunanin daya fadomin yasa na mike tamkar iska zai d'aukeni na nufi d'akin Luba a Karo na farko a rayuwata da nasan Zan shiga dakinta akwai tambayoyin da nake so na mata tunda har tasan shi yayi wa muhasim Fyade dole zata san Mai yayiwa muhasim ya karkata mata wuya. A rabe na ganta a gefen gado da alama kuka takeyi Ina tura k'ofar ta mike a firgice sai naji yanzu bana Jin zafinta wlh wanan nauyin da nake ji a kirjina a duk lokacin da naganta na auremin miji da tayi duk sai naji babu. Koda na isa d'akin zama nayi nima a gefen gadon ban kalleta ba nace "Fada min komai Luba fada min sirrikan Salisu da bansani ba tunda har kika san shi yayi wa muhasim fyade duk tsawon lokacin nan Luba baki tab'a nuna min ko a fuska ba ashe kallon shasha kike min hada Kai kikayi da salisu kuka cutar dani,iya auren cin amanar da kukayi bai isheku ba sai Kun hada kai kun cutar da yata Luba ya akayi Salisu ya karkatawa muhasim baki ki fadamin komai dan Sunanki bazai fito a shigar da karar da zanyi ba Luba ido ta zubawa Aisha tana tunanin abinda ya dace ta fada mata a yanzu babban tashin hankalin ta rabuwa da Salis Wanda tasan wanan dole ne sai sun rabu dan haka itama zatayi duk abinda zatayi dan taga Aisha ta rabu da Salis zata Kara shafa masa bakin fenti yanda Aisha zata tsanesa gwara duk ayi biyu babu "Kinyi shiru luba ki fadamin" "Hmmm akwai Abubuwan da nasan idan na fada miki wlh Zaki iya yanke jiki ki fadi ba Wai iya fyade da karkatawa Muhasim Kai Alhaji Salis yayi ba da ace zaki san abinda yake aikatawa da baki zauna dashi tsawon lokacin nan ba da tuni kin Dade da rabuwa dashi dabiunsa ba masu kyau bane ko ni da Kika ga na aureshi domin biyan bukatar kaina ne bawai dan Ina sansa ba" Tunda ta fara magana na zuba mata ido Ina kallonta kirjina wani irin bugawa yake "Kina nufin Salisu shi ya karkatawa muhasim kai da Baki"? "Kwarai kuwa shine Kuma yana neman maza ma Salisu fasiki ne mazinaci idan har patient suka je wajen sa tsautsayi yasa yaga jikinsu sai ya kwanta dasu" "Ya isa haka luba koma dan yankan kaine ba abinda ya shafeni ki shirya zaki min shaida a kotu" Da sauri Luba ta mik'e cikin tashin hankali tana "Ba ruwana Aisha karki sake ki sa sunana" Luba sai mun hadu a kotu Na mik'e Ina Jin jiri na dib'ana Ina koma wa d'aki na janyo akwatina na fara had'a kayana. Hayaniyar da naji a waje yasa na dan dakata da hada kayan muryar Alhaji Salis nake jiyowa da alama shi da Luba ne "Ki fita ki bar min gida wlh ko tsinke bazaki dauka ba shegiya tsinanniya" Alhaji salis yace Yana jan Luba dake tirjewa akan ya barta ta d'auki akwatinta da mukulin motarta Alhaji Salis sai da ya kai ta har waje yana "nayi freezing acct dinki,na kwace motata kayan naki ma da kudina na siya filayen da kika siya da duk wata kaddara da kike takamar kina dashi na kwace sai da na fada miki idan kika tona min asiri sai naki ya tonu Luba yanda Kika dandana min bakin ciki wlh sai na dandana miki fiye da yanda Kika dandana min shegiya tsinanniya" Luba bata iya magana ba har ya shige ta dora hannunta a ka tare da bin jikinta da kallo tanadin da tayi na duk ranar da Salis ya saketa ma bazata yi talauci ba sabida kudin da take dashi da filaye sai gashi Salis ya kwace kudin acct dinta kuwa Allah kadai yasan yawan sa dan idan tsiyarta ta motsa tatsar shi kawai take tana ya bata ko ta tona Masa asiri take zai d'auko kudin ya bata ko nawane sai gashi lokaci guda duk shekarar da ta d'auka tana tara dukiya tamkar d'aukewar ruwa Alhaji Salis ya kwace. Ta fara bin kantamemen gidan da kallo da babu irinsa a unguwar shikenan tayi bankwana da gidan taya ma zata fara zawarci da girmanta a kuma gidan iyayenta da baifi daki biyu ba san abin duniya yasa bata iya canza musu gida ba ji take Kamar ta fasa ihu dan bakin ciki tuna ta riga da ta raba ma Aisha da Salis yasa ta fara Jin sanyi a zuciyarta tasan bayan duk maganaganun da tayi wa Aisha ba abinda zai saka ta Kara Zama dashi sai sun rabu. Dak'yar taja kafarta ta nufi gidan Asabe ita kadai ce zata iya taimaka Mata ko da akwai aikin da zaayi akan Salis ya dawo da ita. Alhaji Salis Yana komawa ciki yayi kicibis da Aneesa a bakin k'ofa tana Jan akwatin ta Wani sabon zazzabi yaji yana neman rufeshi a gajiye yace "Ina zaki Aneesa"? "Abuja zan tafi na gaji da wanan auren tunda na aureka daga wanan masifar sai wanan ban taba samun kwanciyar hankali ba wlh nagaji ka sakeni kawai dan bazan iya ba" Aneesa tace tana share hawayen dake zubo mata "Baby kece yau kike cewa na sakeki"? "Kirani Aneesa Alhaji bansan haka aurenka zai zame min ba dama mummy ta fadamin na dage sai na aureka bansan Ashe wanan tashin hankalin ta hango min ba Ashe har wata ma kayiwa ciki har da su ya wlh bazan iya ba ka sakeni kawai na tafi" Alhaji Salis da ke jin kansa Kamar ya rabe gida biyu ya hau Jan "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha" Jikinsa rawa kawai yake bai iya dakatar da Aneesa dake cewa ya Aiko Mata da takardar sakinta ba har ta fice. Muryar Afrah dake kuka yasa yayi saurin waigawa Aisha ce janye da akwatinta hannunta cikin na Nana Afrah Kuma ta rik'e akwatin tana magiya Aliyu da Ashraf na tsaye Suma da alama rokonta suke. A daidai lokacin da Hindatu ta fito daga dakinta tana "Ikon Allah yau Kuma a haka muka tashi Luba dai ta hargitsa gida Amarya ta tafi ga Hajiya itama zata tafi innalillahi wa Inna ilaihi rajiun "Ki cika min akwati Afrah ki cika min nace Miki" "Dan Allah hajiya umma ki rufa mana asiri karki tafi" "Wlh sai na tafi banga mai hanani ba Kuna da hankali kuwa taya Zan zauna da azzalumun da ya cutar da Yar yayana wlh sai na yi kararsa an bi mata hakkinta " Aisha tace cikin ihun kuka tare da fusge akwatin ta Ashraf na Shirin magana tace "Duk Wanda ya Kara cewa na zauna wlh sai na masa baki ku kyalleni" Ta nufi bakin k'ofa Alhaji Salis ya zub'e a kasa Yana k'ok'arin rokonta ta tureshi tana "Wlh wlh sai nayi kararka" "Idan kikayi haka Aisha kin tozarta yaranki zaki shafa musu bakin fenti" ko kallonsa batayi ba tayi waje Alhaji Salis ya runtsa idonsa ya tafi tunanin lokacin da rayuwarsa ta fara tarwatsewa... Posting Monday to Friday nayi ne yau sabida jiya na Dora cigaba yanzu sai Monday insha Allahu Naceba Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195 Call:08064532391 Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida tested nd trusted Natural/organic INGANTACCEN MAGANIN SANYI TOILET INFECTION MAI WANKO DUK DATTIN MARA KOWANI IRIN SANYI NE ZAI MAGANCE SHI DAYARDAR ALLAH SHIN KINAFAMA DA RASHIN SHA AWA? RASHIN NI IMA RASHIN GAMSUWA SHIN KINYI SHEKARA DA SHEKARU KINA NEMAN HAIHUWA RIKICEWAR JINI CIWON JIKI CIWON MARA YAYIN AL ADA DUKA WANNAN MAGANIN YANA WARKARWA ME CIKI BATA SHAN MAGANIN SANYI NA 4K YAKE INA KATSINA INA AIKAWA KO INA A FADIN KASAR NAN HARDA KETARE MAZA DA MATA MAGANIN SANYI MAI GYARA MU AMALAR AURE AUNTY ZEE MOM MUJAHID 08162859027 KATSINA *WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER TA KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN* *+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKINA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA* *Page 15* *Waiwaiye* Alhaji Salis A rayuwarsa ba wacce ya tsana Kamar Luba kawar Aisha halayen ta na san abun duniya yasa yaji ya matukar tsanarta amma ganin Farin cikin Aisha shine taga tana mu'amalla da Luba yasa ya danne tsanar da yake mata dan ya farantawa Aisha rai,ransa ya b'aci a lokacin da ya gano uban kudin da yake kashewa Aisha a siya mata sutura Ashe Luba take bawa Inda hakan yasa ranar da ya gano ya rufe ido yaci mutunci Luba a ransa Yana tunanin indai da zuciya a kirjinta dole tayi zuciya ta rabu da Aisha. Sai dai yanda Aisha ta hana kanta walwala ta karfi da yaji har abin na Neman shafarsa yasa ya hakura yace ta cigaba da muamalla da ita. Dama can ba wani abu dake hadasu sai gaisuwa kafin aurenta ne ma da lokacin da take da Aure suke dan gaisuwar mutunci idan ta kama su tsokani juna idan ta same shi a gida. Abinda ya fara daure masa kai bai wuce salon da ta bullo masa dashi ba a bayan ya mata rashin mutunci ta cirewa Aisha kayanta ya d'auka ko a hanya ta ganshi ko gaishe shi bazata yi ba ga mamakinsa wata daya a t sakani ranar ya dawo daga