← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 71

Sashe 26

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajen aiki a gajiye yaci abinci kenan Aisha na dan mamatsa kafarsa da yaji na masa ciwo yaro ya kwada sallama a tsakar gida wai ana sallama dashi a waje iya saninsa ba wanda suka yi zai zo nemansa har ya ce yaron yaje ya tambayo mai sallama dashi Aisha tace yaje mana kawai yaga mai sallama dashi Haka kuwa akayi ya fita waje dan ya duba mai sallama dashi Sai dai ko da ya fita bai ga mai sallama dashi ba hasali mace ya hango nesa da gidan ta saka doguwar riga yana k'ok'arin komawa ciki yaji an Kira sunansa Inda yaji Kiran sunan nasa ya kalla yaga wajen da macen ke tsaye ne cikin mamaki ya nufi wajen da take a tsaye a ransa Yana mamakin wacce wanan "Kece kike kirana"? Salis yace cikin mamakin ganin Luba a tsaye Ta sakar masa murmushi tana ""ee ni nake kiranka" "Yaushe gidan ya zama bakonki Kuma dama idan Kika zo a waje kike tsayawa Kuma wajena kike zuwa da zaki aika a kirani"? "Aa gidan ba bakona bane kam ba wajen Aisha nazo ba wajenka nazo shiyasa na aika a Kiraka" "Ikon Allah toh lafiya"? Sai ta fara susune kai Salis mamaki yasa yace "Wai kanki kalau kuwa ko Zawarci yasa kin haukace ne mai haka"? "Hmm Salis kenan kai a rayuwarka kanaso kaga kana cin mutunci na yanzu dan na aika a Kiraka laifine gaisawa kawai zamu yi dama banaso na Shiga ciki sabida dare yayi" Salis tsananin mamaki yasa yama kasa yiwa Luba dake ta wani karkade karkade magana "Wai mai kake ta kallona ne"? "Daga yau karki sake ki Kara min irin wanan haukar ana zaune kalau zaki aika a kirani mai hadina da ke zaki ce gaisawa kawai zamuyi dake Aisha ce kawarki banida hadi dake da wanan zubar da mutuncinki da kike yi da ma wajen uban yayan ki Kika koma ko Kika sake wani auren da yawon bin gidajen mutane da kikeyi kina aron kayan mutane kina sawa" "Banida mijin Auren ai Salis shiyasa banyi ba ko zaka taimaka ka nemo min namiji mai irin sunan ka mai irin komai naka dai" Salis tsabar takaici bai kara mata magana ba yaja tsaki tare da nufar cikin gidan ya shige yana mamakin abinda Luba tayi da ya kasa gane mai hakan ke nufi Koda ya shiga bai damu da ya fadawa Aisha ba dan yasan ko ya fada mata ma ba jawa Luba kunne zatayi ba tunda bata san abinda zai hadasu. A yau Yana zaune a office wata Zainab ta budo kofar ta shigo kawarsa ce Kuma tsohuwar budurwarsa da suka had'u a kasar waje haduwar sa da ita a waje ta koya masa mumanan dabiu rashin mata a kusa yasa ya fara biyeta suna watsewa ita ta kwadaita masa san yaji yana san ya ringa sanin taste din mata daban daban ta kara da dora shi akan wani harka dake mugun shigo masa da kudi mumunan dabiar da ya koya a waje Kuma sirrinsa da bayaso kowa ya taba sani,har ya kusa gama abinda ya Kai shi can Yana tare da Zainab ba Kuma iya zainab din ba yana neman wasu ma, ganowar da Zainab tayi Yana tsalle tsallen yasa suke yi wani irin fada gata da tsananin kishi duk a tunanin ta bashida aure ta Kuma d'auka zai Aureta din. Sai da ya kusa dawowa Nigeria ya fito ya fada mata yana da Aure bazai iya aurenta ba. Kaca kaca suka yi da ita har ya dawo gida Nigeria da kudurin tunda ya dawo wajen iyalinsa zai ajiye wanan halin nasa cikin kudura ta ubangiji Kuma tunda ya dawo bai Kara Neman kowace mace ba duk da wani zubin idan patience masu larurar da zai ga jikinsu idan yagani yakan ji Kamar ya koma ruwa sai ya danne. Ido ya zubawa zainab din har ta zauna kasan ransa Kuma mamaki yanda akayi ta shigo Nigeria har tasan office dinsa. Sai da ta zauna ta sakar Masa murmushi tana yayi mamakin ganinta ko Murmushi ya maida mata yana aa baiyi mamaki ba ya sa aka kawo Mata lemo,suka hau hira,har a cikin hirarsu take fada masa yanda tayi kewarsa ta hau masa magana da jikinta. Zainab tasan kansa take yaji bazai iya jurewa ba Koda ta zaga wajen da yake zaune suka kaiwa juna cafka. K'ofar da aka turo yasa suka saki juna da sauri Hankalin Alhajj Salis yayi mugun tashi da ganin Luba a tsaye taci kwalliya Kamar zata je biki da alama itama mamakin yanda ta gansu ne ya daskarar da ita. Zainab kuwa ta gyara rigarta cikin turanci tace mata bata iya knocking bane kafin ta shigo ya zata fado kai tsaye baa bata izini ba" Alhaji Salis dai kunya yasa yaji kamar an like Masa baki tamkar Aisha ce ta Kamashi haka yaji. Luba kuwa ta watsawa zainab harara ta samu waje ta zauna Salis ya ce mata lafiya mai tazo nema a office dinsa"? "Hmm ashe dai haka ake cin amanar kawata wanan Kuma wacece? "Luba mai kikazo nema a office dina Ina ruwanki da koma wacce mai hadina dake wai kika takura min kwana biyu"? "Ka sallameta magana zamu yi" "Ke din banza da zaki saka na sallami wata dalla tashi ki barmin office" "Hmmm Salisu kenan wlh daga nan gidanka nayi sai na fadawa Aisha abinda kake aikatawa kaji na rantse maka" "Kin dade baki fada ba dalla fita kibani waje" Luba mik'ewa tayi tana "zaka kuwa gani wlh sai na fada Ta fice daga office din sai Salis yaji Kuma hankalinsa ya tashi yabi bayanta da sauri. Da gudu ya cimmata sabida saurin da take ta zubawa ya sha gabanta Yana "Dakata Luba ba abinda kike tunani bane karki je ki hadani da Aisha Mai kika zo nema"? "Ai da baka fito ba wlh sai naje na sameta na fada mata"? "Toh na fito ba sai kinje ba ya akayi"? "Aure nakeso nayi Salisu nagaji da zaman haka ba Aure" Yamutsa fuska Salisu yayi Yana "Toh idan kina san auren Ina ruwana ko wani taimakon kike so ayi miki ai da kin fadawa Aisha ba sai kinzo wajena ba" "Kai kafi cancanta nazo wajenka ai neman taimakon a gaskiya na gaji ma da kumbiya kumbiya Salisu na kamu da sanka nasan zakaji banbarkwai sabida Aisha kawata ce naso na daure amma wlh na kasa" "Luba a cikin hayyacin ki kike kuwa ko kina Shan kwayane"? Ni salisu mijin kawar ki kike so"? "Toh Ina so yasan wani kawance Salisu ai ba ruwan so da wanan ni yarda kawai nake nema nasan Aisha nada saukin Kai indai na fada mata bazata damu ba zata fahimceni" "Lailai bansan baki da hankali da tunani ba sai yau ke ko a mafarki akace miki zan aureki sai ki yarda Luba duk matan duniya na rasa wacce zan aura sai ke yanzu ko nine nazo nace Ina sanki dan Allah sai ki yarda bayan kinsan yanda kike da Aisha? dama haka kike? san abun duniyar naki ya Kai har haka?yanzu zaki iya cin amanar Aisha" "Salisu wai me abin cin Amana anan matsawar a musulunce ba haramun bane ai ba laifi bane dan kawaye sun auri miji daya" "Aisha batayi dacen kawa ba idan na koma gida dole na fada mata wacce ke dole na fada mata tasan irin zaman da zatayi dake" "Ai kafin ka fada mata zanje gida na sanar mata abinda kake aikatawa kai ma dole na fada mata yanda kake cin amanarta babu kunya babu tsoron Allah" "Kije ki fada mata kin Dade baki fada ba ai karshen kawancen ku yazo wuyanta na fada Mata" Luba bata Kara ce dashi komai ba ta dau hanya ta tafi. Salisu da mamakin zancen da Luba tazo Masa dashi ya koma gida ko zainab ma bata Kara gane kansa ba har suka rabu akan zasu had'u a masaukinta. Yana komawa gida bayan yaci abinci a madadin ya fito ya fadawa Aisha abinda ya faru sai ce mata yayi "Aisha yanzu idan nace ki rabu da Luba sai kiji haushina ko"? Take fara'ar fuskarta ta gushe tana "Mai ya faru Kuma Abban Ashraf"? "Aisha Luba ba matuniyar arziki bace ba ki rabu da ita yanda kika d'auketa wlh ba haka ta d'auke ki ba na dade Ina fada miki jinina bai d'auketa ba ki rabu da ita Aisha" "Wai wani abin Luba tayi dan Allah mai yasa ka tsani Luba Abban Ashraf na rasa mai ta ma nidai dan Allah Abban Ashraf karka rabamu dan Allah idan ma wani abu tama kayi hakuri yanzu kana raba mu zata ce sabida mun ga mun yi kudi mu ke so mu wulakanta ta ka ga hakan bai dace ba kar ka manta tun kafin na san zan hadu da kai nake tare da ita" "Hmm Aisha kenan tunda kin dage toh shikenan Ina jiye miki ranar da zaki yi nadamar saninta a rayuwarki ne shi yasa nake so ki rabu da ita tun yanzu" "Babu ma ranar Abban Ashraf dan ka tsaneta ne kawai bansan Kuma mai ta maka haka da zafi ba wlh bata kara aron kayana ba" "Hmmm Ai shikenan" Dama yasan za'ayi haka bazata tab'a yarda ba haka ne yasa ya kyalleta dan yasan ko fada mata yayi ba yarda zata yi ba" A haka Luba ta cigaba da masa naci ta ringa ziryar daga office dinsa shi kuwa ya bud'e mata wuta wajen yi mata rashin mutunci ko Kare bazai dauki wulakanci da yake mata ba inda ya Kara jinjinawa fuska biyun da take dashi idan suka hadu a gidansa bata nuna masa komai. A haka suka fara Shirin komawa sabon gidansa. LUBA Daga lokacin da Salisu ya mata Rashin mutunci ta kudurta a ranta samo miji Wanda yafi salisu yanda zata rama duk wulakanci da yayi mata idan zata samu ma ta Wanda ya dameshi a kudi har da zai ma iya daure Salis din. Sai dai duk san ta samu mai kudin duk masu zuwa wajenta basu kamo kafarsa ba. Ba abinda ya Kara rikita mata lissafi irin tsalallen gidan da yake gwangwaje Aisha dashi da ita gidan ma baya gabanta sau tari idan ta kwanta haka zatayi ta mafarki da gidan idan ta tashi tunanin
Chapter 26 · 0% Book details