← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 71

Sashe 10

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

naji kaunar yarinyar har a raina ni da kaina na zabi a ringa kiranta da Nana. Na lura Kamar daga yayana har Aunty mamy basa san Rainon Nana dan har yayana cewa yayi ko gidan marayu zai kai Nana ni kuwa nace masa ba sai an kai ta ba su bani ita zan riketa. Yayana cemin yayi ba lailai Salis ya yarda ba nace masa indai Salis ne nasan bashida matsala. Koda na koma katsina na tari Salis da zancen shiru yayi yana kallona har na fara Jin ba dadi a raina yace min anya zan iya kuwa da wane zanji da rainon cikin jikina ko da rainon Nana sai yake ganin kamar bazan iya ba bayaso na dorawa kaina wahala ko dai maganar yayana zanji a kai ta gidan marayun. Na girgiza masa kai akan zan iya nidai kawai ya bani izinin karbota. Kamar dai na masa dole.yace min to Shikenan. A yanda Nana ta dawo hannuna kenan kaunarta a zuciyata ta daban ce Inda nasan haka ya hada da san da nake yiwa muhasim da tausayin mahaifiyarta da ke fama da larura. A lokacin da Luba tazo gidana sakin baki nayi Ina kallonta dan wani irin kyau naga tayi Kamar wata amarya,kayan jikinta ma masu balain tsada ta Sha lullubi har saman kanta Kamar dai matar aure. Ni Ina Kare Mata kallo ita Kuma ta zubawa Nana Ido dake kwance a doguwar kujera tana "A Ina kika Samo 'ya nidai nasan ba haihuwa kikayi ba tunda ga ciki nan a jikinki" "Wlh yarinyar wata Yar uwarmu ce na karbota dan maman ta tana haihuwa ta rasu. Ta saki sallati tare da nufo wajen da na kwantar da ita ta d'auketa tana "Allah sarki baiwar Allah kice bata san mahaifiyar ta ba Kwalla ya zubomin na kashe muhasim da nayi da ranta da tausayin ta hanyar da aka samu Nana Ina "wlh kuwa" Na share hawayen fuskata Ina cigaba da kallon luba da nidai ta canja min sosai har sai da na kasa hakuri nace "Luba Kinga yanda Kika canja kike kyalli Kamar wata amarya kuwa"? Ta saki murmushi tana "Ai amaryar ce tunda na kusa shiga daga ciki" "Dan Allah fa"? Nace cikin tsananin murna Ina "wa kika samo dan da alama kin samu irin wanda kike so"? "Wlh na samu Aisha alhamdulillah tunda na kwallafa a raina sai na samo Mai kudi na samu dai" "Kai Alhamdulillah na miki murna sosai wlh kawata a Ina yake aiki"? "Gidan mai ne dashi fa sai dan aikin asibiti da yakeyi" "Kai madalla naji dadi wlh ya turo manyansa?mai mata ne"? "Ke fa dan baki fiye zama bane amma da duk kin san halin da ake ciki,ya turo manyansa mana a ranar da aka kai kudin kawai aka daura Auren,Yana Kuma da Mata" "Na saki baki Ina kallon ta cikin tsananin mamaki" "Wai kina nufin yanzu haka da aurenki"? Ta saki dariya "kwarai kuwa tarewa ne dai banyi ba sai wani satin" "Kai wai dagaske kike ko da Wasa"? "Wlh dagaske nake toh mai abin mamaki nifa ba budurwa bace bazawara ce ni, shima ba saurayi ba wane shiri za'ayi ai kawai Aure aka daura zan tare sati mai zuwa" Na saki ihu dan har ga Allah wlh kamar na taka rawa haka na ringa ji "Na miki murna kawata wlh bakiji dadin da naji ba Kai Kai Kai ke kinji dadin da nake ji a zuciyata a Ina Kuma zaki zauna"? "Abuja zan zauna" "Aikuwa duk da uban cikin jikin nan nawa dani zaa kai ki insha Allahu haba shiyasa wlh da kika shigo naga kina ta walwali Kai Aure ma rahama ne wlh zanso kuwa ganinsa ko baki bashi labarina ba" "Kai ai yasan da zamanki dan baya garine da dashi zamu zo ku gaisa" "Ba damuwa idan munje Kai amarya sai naganshi ai" "Kijiki da wata magana Wai Kai amarya sai kace budurwa ai dagani sai mijina zamu wuce ba mai rakani" Na saki dariya Ina "Ikon Allah kawata yanzu dai kin Shiga daga ciki kema kin zama matar Aure wlh naji Dadi takaicina daya ba gari daya zamu zauna ba" "Ke dai bari dadin abin yanzu ai akwai waya kicewa mijinki ya siya miki nima yace zai siyamin sai mu ringa waya" "Aikuwa wancan sati Salis ke cemin zai siyamin wayar ni kinsan ban wani damu da kyale kyale ba amma ko dan ke dole nasa ya siyamin ko ya zaiji idan nace mishi kinyi aure kullum cikin min yake kice kawarki ta tsayar da hankalinta waje daya tayi Aure" Ta saki dariya tana "aikuwa dai gori ya Kare an daura min aure" "Nikam mai zan baki gudunmawa wanan kyalin ma da kike anya angon nan ba Sha zumar amarya ba" "Toh da ke zai jira" Na saki dariya tare da mik'ewa dak'yar sabida cikina ya tsufa na Shiga d'aki,dan magangunan da nake siye masu tsada da na jingine a gefe da na daina sha sabida ciki duk na zubasu a leda na bud'e show glass dina da na jera humra da turaren wuta masu balain tsada da aka hadomin daga Maiduguri na d'auko wajen kwalba biyar biyar duk nayi waje na kai mata na ma dai rasa toh mai zan bata. Ta kuwa washe baki tana min godiya motsin da Nana tayi yasa na d'auketa. Hira muka yi tayi bata bar gidan ba sai karfe biyar na rakata ta tafi zuciyata fal da farinciki kamar anyi min bushara da gidan Aljanna rabon da na tsinci kaina a cikin irin farin ciki haka har na manta dan tunda yayana ya Shiga tashin hankali nima bana Jin dadin rayuwar amma auren Luba kuwa ya faranta min. A lokacin da Salis ya dawo ko zama ban bari yayi ba baki a washe nace "Luba kawata tayi Aure" "Sai naga ya dan zaro ido yana "ya akayi kika san tayi aure"? "Kai kaji ka da wata magana wlh gidanan tazo dazu nan kasan wlh har ta canza" Na saki baki na hau bashi labari shi dai ya buga tagumi yana kallona bandai gane maanar kallon da yake min ba" "Wai dan Allah Abban Ashraf mai yasa baka san kawata ne abin farinciki ya sameta na fada ma ka tsaya kallona" "Hmm ai wanan kawar taki tsinaniya ce Allah yasa ba ta karfin tuwo ta samo mijin ba" "Innalillahi haba Abban Ashraf mai yayi zafi haka zaka tsine mata idan bazaka ce Allah ya Sanya alheri ba aikuwa bai dace ka tsine mata ba" "Hmmm Allah ya kyauta" Yace tare da d'aukar Nana da ke kwance akan kujera ya hau min wani tambayar duk dan ya Kau da maganar luba. A takaice sati uku a tsakani na haifi ummi wanan karon banyi wani taro ba amma duk hidimar da Salis ke yawan yimin yamin sosai dan arziki Kam Kara ninkuwa yake inda nafi yarda da sabida Salis nada kyauta da sadaka yasa yake ganin budi,dan ko iya dangina ma Allah kadai yasan hidimar da yake yi dasu ba karamin daga min daraja yayi a wajen dangina ba duk Inda naje sai an fada min abin alherin da yayi. Luba kam tana Abuja a ta waya na sanar mata na haihu tace min bazata zo ba zata min aike. Ta kuwa aiko min da kayan jarirai inda na yanke a raina.insha Allahu idan nayi arbain zanje Abuja gidanta tunda anan Salis ke yawan zuwa aiki sati biyu ko uku idan ya tashi tafiya sai na bishi. Sai dai Koda nayi arbain din na tuntube shi da maganar ya had'e rai akan bazanje ba shi Yama rabani da ita tunda Allah yayi ba'a garin take Aure ba. Nidai bansan mai yasa yake haka ba. A haka rayuwa ta ringa tafar mana rungume da yarana da Nana da nake Jin kaunarta na daban a zuciyata lokaci lokaci nakan je bauchi dan na duba muhasim. Abinda ya fara dan damuna bai wuce zaman da Salis baya yi sosai ba yanzu bashida lokacin kansa sosai kullum Yana tafe hanyar abuja idan yaje sai ya kusa sati biyu ko uku kafin ya dawo. Ni Kuma a wanan lokacin bansan dalili ba sai naji Ina matukar bukatar shi a kusa dani,yawan tafiye tafiyen sai ya fara damuna, amma tunda nema ne ba yanda zanyi,idan yayi tafiya zai dawo haka zan ta Shirin tarbarsa Ina murna girki kuwa haka zanyi kala kala Ina dokin ganinsa ba iya ni kadai ba har da yarana. Idan ya dawo kuwa a gajiye tikis sai an samu kwana biyu ma wani Abu ke shiga tsakaninmu dan bacci kawai yake shara idan ya dawo. Ko ya dawon ma bazai wuce sati ba zai Kara komawa sai an samu sati biyu ko uku kafin ya dawo nidai hakuri kawai na koma yi. Har maganar nayiwa luba ta ringa min dariya wai ko dai jarraba na karo ai ko shekara zaiyi bai dace na wani damu ba. A haka dai rayuwa ta ringa tafiya na ringa kula da Nana da ummi da nake ma jinsu Kamar Yan biyu. Wata rana Alhmis da yayi daidai da auren Luba ya shekara daya ta kirani akan ta haihu. Na ringa murna Ina alwashin zanje mata tunda Yara suna hutu zan Kai su gidan Aunty mamy idan naje ma na samu lokaci da Salis dan har ga Allah sai naji Ina sha'awar zuwa Abujan dan ban tab'a zuwa ba zan so zuwa har ga Allah a ta waya na Kira Salis da naji muryarsa Kamar Mara lafiya cikin doki nace masa Luba ta haihu dan Allah ya min izini zanzo Abuja inyaso sai na sauka a gidansa bayan suna sai na dawo cikin Yar murya na nuna Masa inama kwadayin san naga ya garin Abujan yake. Budar bakinsa sai yace min bazani ba shi nan da kwana biyu ma zai dawo na tanade shi ya katse wayar. Na sake kiransa yak'i d'auka Wlh har da kukana dan bansan mai yasa bayaso naje wajen Luba ba abinda ma ba gidan Luba zan sauka ba a wajensa zan sauka astagfurullah a ranar har auna masa zagi nayi a raina Koda Luba ta Kira cikin kuka na fada mata ya hanani zuwa ta saka dariya tana ai bazai so nazo ba Kar nayi mamaki akwai abinda yake b'oyemin wayasani ma ko akwai
Chapter 10 · 0% Book details