Sashe 1
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data Normal *NIDA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* *BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM* *Page 1* *1am* LUBA "Alhaji Alhaji" "Ummm wai mai haka ne Luba bazaki barni nayi bacci na huta ba fisabillahi"? "Taya zakayi bacci ka huta bayan ka ajiye mu? ai tunda ka ajiye mu kace mu biyu bamu isheka ba ai baka ga hutu ba Alhaji. jiya da kake d'akin Hindatu ai ba bacci kayi ba kwana kayi Kuna abu sai da ka zagayo dakina zaka zo ka ringa baccin gajiya Alhaji tashi ka bani hakkina" "Luba dan Allah ki bari sai da safe kafin na tafi aiki wlh kaina ma ciwo yake ni kwana biyun nan ma bana iya komai wlh sabida gajiya" "Eee kwarai baka iya komai fa shiyasa jiya naga ka dade baka fito daga d'akin hindatu ba,dama kasan bakada kwarin rike mata uku ka Kara aure ai tunda har kaga zaka iya nima bazan iya daga kafa a tauyeni ba bana Jin bacci ka bani hakkina" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Alhaji salis yace tare da mik'ewa zaune Yana kallon luba da ke zaune dirshan a tsakiyar gadon ta ma yaye bargon daya rufa sai wani girgiza take yasan ba wani bukata da take tsabar rigama ce ba inda yake samun bacci mai dadi da nutsuwa sama da dakin Aisha amma indai kwanan hindatu da Luba ya zagayo haka zasu sako shi a gaba kamar su kashe shi ya rasa wanan masifa da me tayi Kama "Luba nace miki kaina ciwo yake ki bari da safe kafin na tafi aiki nifa ba injin bane ba" "Alhaji jiya bakace wa hindatu kanka ciwo yake ba sai da kwanana ya zagayo dan ka raina min hankali ka bani hakkina sai ka sha baccinka" Ya riga yasan halin Luba indai baiyi din ba bazata tab'a barinsa yayi bacci ba. "Tunda na gaya miki bazan iya komai ba Kika dage sai kiyi luba" Kansa ta fada ba dan ransa naso ba ko Yana da wani bukata ba yayi. Yana jin tana masifar ita daya ya mata kad'an ai ba daya yakeyi a d'akin Hindatu ba yaja tsaki tare da juya mata baya daya ga ma zata dame shi ya sauka daga kan gadon yayi kwanciyarsa a kasa nan da nan bacci yayi awon gaba dashi. Hayaniyar da ya ringa jiyowa daga Palo yasa ya bude ido yaga gari yayi haske ya mik'e da sauri Yana "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun gari fa ya waye wanan wane irin masifa ne" Kullum sai hindatu da Luba sunyi fadan daya zame musu farilla ya rasa wanan masifa Kamar suna ganin hanjin junansu ace karfe shidda na safe har sun fara fada. Bai fita waje ba ya fada bandaki yayi wanka a gurguje yazo ya tada sallah,Yana sallah ma hankalinsa na wajen palon dan har lokacin Yana jiyo zage zagen da sukeyi yasan har makota ma ana Jin hayaniyar su. Yana sallamewa yayi waje da sauri Yana bude k'ofa takalmin da hindatu ta jefowa Luba ya sauka a kansa. Ya dafe kansa Yana sallati "Na Riga da na kafu a gidanan wlh ba yanda zakiyi dani luba mutuwa ce zata rabamu mumunar banza mumunnar wofi ni bansan ma mai Alhaji ya gani a jikinki ya auroki ba Alhaji ma yace hakuri yake yi dake" "Ke da sadakarki aka bashi ko lefe fa baayi miki ba ni kuwa ki tambayi kowa kiji ba karamin kudi ya kashe a auroni ba tsabar kwantan da kikayi sadaki ma yafe Masa akayi sabida tsabar kin rasa mai aurenki" "Ya isa ya isa haka" Alhaji Salisu yace a tsawace Yana mulmula goshinsa dake Masa zugi "Wanan wane irin balai da masifa ne da asusuban nan zaku fara masifa wai wanan wane irin rayuwa ne Hindatu Nagaji Luba na gaji Wai ku yarane?ace da manyan yayanku ku addabeni ku hanani sukuni,ba dama na dawo gidanan na tab'a samun kwanciyar hankali dan balai idan na doso gidana haka zan ta fargaba a wane dalili? Haka kuka ga Aisha nayi domin Allah bazakuyi koyi da ita ba to wlh Nagaji idan kuka kaini bango ko duniya kuka haifa min wlh sakinku zanyi kowace ta Kama gabanta" Ya koma daki a fusace har Yana tuntube Luba taja tsaki tana "Ai baka ga komai ba tunda ka auro wanan mai zubin samudawan Ina zaka taba samun kwanciyar hankali" "Hindatu kuwa dakinta ta shige tana masifa kasa kasa. Wajen karfe bakwai da rabi yaran duk Suka fito cikin Shirin tafiya makaranta dan bangarensu daban da na iyayen matan an ware musu dakinsu daban mazan ma dakinsu daban Afrah itace babba a Mata tana matakin karshe a secondary ita take kula da sauran kanen nata, inka d'auke Ashraf da Abubakar da suke karatu a A b u zaria. Basu tsaya neman abinci ba dan sun san sai dai a biyo su dashi indai Luba ce da girki d'akin Aisha suka nufa da suke cewa Hajiya Umma Kamar yanda Suka Saba sai da suka gaisheta suka fito Suka nufi kitchen Inda suke Jin motsin luba iya yayanta ta amsawa gaisawar ko kallon Afrah da yayan hindatu batayi ba a daidai lokacin da hindatu ta fito daga dakinta tana "Kuzo ku wuce ku tafi karku yi latti dan jarraba bazaa fito da wuri a dorawa yara abinci su ci su tafi dashi ba har sai sun makara" Ta ja hannun kananan Suka yi hanyar waje duk sai da ta bisu da manyan biscuit ba Wanda ta ware dan ita bata kishi da yara kamar yanda Luba keyi sai da driver ya jasu suka tafi ta koma ciki. A Palo tayi zamanta tana Jin luba na kanana haibaice habaice itama tana daga palon ta daga muryarta yanda Luba zata jita tace "tsabar kwadayi da san zuciya wata ta Kashe aurenta ta baro yayanta tazo ta auri mijin kawarta tur wlh da wanan cin amana ace " Fitowar Alhaji Salis daga d'akin luba yasa Hindatu yin shiru a daidai lokacin da Luba ta fito fuska a had'e tana "Alhaji wlh kayiwa hindatu gargadi ta fita daga harkata" Ko kallonsu baiyi ba ya nufi d'akin Aisha bashida burin daya wuce ma ya bar gidan daga luba har hindatu kaddara yasa ya auresu da tunda ya auresu yayi bankwana da wani abu Wai shi farinciki . A hankali ya tura k'ofar dakin Aisha da sallama har a yau da aka tafi shekaru nauyinta da kunyarta yake ji. Yana ji ta amsa sallamar ciki ciki har ya isa gefen gadon ta ya zauna ita Kuma ta cigaba da gugan da take. Yasan ko zasu shekara a haka bazata tab'a ce Masa komai ba Yana bakin cikin yanda ya zama bakon karfi da yaji a wajenta tamkar ba Aisharsa Mai kaunarsa ba. "Anjima zan tafi Abuja sai nayi sati uku kafin na dawo" "Allah ya kiyaye hanya" Shiru ne ya ratsa d'akin Alhaji Salisu yace "Aisha dan Allah dawo nan zamu yi magana" Sai a lokacin ta dago ta kalleshi suka hada Ido ta d'auke kanta tana "Ina jinka daga nan" "Aisha Abu baya wucewa ne a wajenki dan Allah kiyi hakuri nasan na miki ba daidai ba shekara goma tsakani da Allah kin kasa cire abinda ya faru a ranki" Murmushin takaici tayi tana "Alhaji wai nikam kaji na fito na ce maka da wani Abu a zuciyata Kai kadai kake kidanka kake rawarka ni ba komai a raina" "Wlh da wanan abin da kike min gwara ki fito kimin fada ki zageni kimin koma mene da ki kawo ido ki zuba min kin maidani tamkar hoto ki Kara nesanta kanki daga wajena wlh bana Jin dadin irin rayuwar da muke tunda yanzu har da zuria a tsakani an tasa Kuma ai sai ki cire komai a ranki" "Ba komai a raina Kai kake damun kanka a yanzu banida wani damuwa nikam" "Hmmm Aisha kenan to ni zan tafi na damka amanar gidana a hannunki dan Allah kisa min ido Kar suyi min hauka da suka saba,wlh sabida ke nake dawowa gidanan amma matan nan caza min Kai suke" "Allah ya kiyaye" Mik'ewa yayi ya ajiye mata kudi a gabanta Yana sai ya kirata a waya Yana fita taja tsaki batasan mai yasa ko kadan bata ganin farinsa ba duk kuwa abinda zai Mata. Yana fita ya ci Karo da luba a bakin k'ofa ta cika tayi fam "Ranar girkin nawa ma Alhaji sai anci amanata tsakani da Allah ran girkinta kana zuwa dakina ka dade haka"? "Dan Allah bani hanya na wuce" Ya bangajeta tabi bayansa tana masifar Shiga d'akin Aisha da yayi ya dade ita dai idan amanarta akaci bata yafe ba hindatu kuwa na zaune a tsakiyar palon sai dariya take kasa kasa dan sosai take ganin haukar Luba ko lissafi ma bata dashi ai ko kwana zaiyi a d'akin Aisha a ganinta ko A bai dace tace ba. D'akin Luba ya shiga dan ya dauki akwatin kayansa Luba kuwa ganinsa da akwatin Kaya yasa tayi turus tana "Alhaji ya naganka da akwati gafa abincinka nan a palo" "Zanyi tafiya ne zuwa Abuja akwai aikin da zanje nayi sai nayi sati uku kafin na dawo" "Alhaji yanzu tsakani da Allah ka rasa ranar da zakayi tafiya sai ranar da kake dakina" "Luba bani hanya na wuce banida lokacin kananan surutu " ya fice daga d'akin. Yana fita ya tsaya a tsakiyar falon fuska a had'e Yana "Luba bana San tashin hankali Hindatu na hadaku da girman Allah karku min hauka a gida ku ba Yara bane ba,ku daina zubar min da mutunci a unguwa wlh idan dai har a ka kirani aka fadamin kun min hayaniya a gida wlh zan dauki mumunan mataki akan ku kunji na rantse muku" "Nifa idan bata Shiga harkata ba wlh ko kallo bata isheni ba Alhaji ni iskanci ne kawai bazan d'auka ba dan ba dan ita kadai aka yo ka ba, bata da burin daya wuce taga ta mallake ka ita kadai wanan ne dai bata isa ba" Hindatu tace tana hararar Luba Luba kuwa tayi kwafa dan ji take Kamar ta shako hindatu ba wacce ta mata Karen tsaye a rayuwa sama da hindatun har a yau burinta taga ta raba ta da Alhaji. Alhaji Salisu bai Kare ce musu komai ba yasa Kai ya fice