← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 71

Sashe 13

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na rufeni yarana duk suka yanyameni. Har da Nana da Ummi Aunty Mamy kuwa duk ta daka musu tsawa akan su bar kaina ta cigaba da tambayata lafiya ta gani haka dan duk Wanda ya gani yasan ba lafiya ba. A daidai lokacin da naji muryar yayana Yana "Mai ya samu Aisha"? Present Alhaji Salis zuciyarsa cike take da fargabar auren da zaiyi a yanzu da lokaci ya matso sai yake Jin zuciyarsa cike da fargaba dan ya nunawa Iyayen Aneesa matansa basuda matsala duk zasu rik'e Aneesa da Amana. Duk da sunje katsina sunyi jeren dan a cikin gidajensa daya gina na siyarwa ya zabi daya ya gyara dan Aneesa ta zauna kafin yasan yanda zai fadawa su Luba. Aisha ma ko ta kansa bata bi ballantana yace ta damu da auren da zaiyi. Sai dai abinda ya daga Masa hankali bai wuce mahaifiyar Aneesa da tace tanaso taje gidansa ta damka wa matansa amanar Aneesa ba,taya mahaifiyar Aneesa zata je gidansa bayan Aisha ce kawai tasan zai Kara Aure. Har aka Shiga satin bikin zuciyarsa cike take da fargaba Yana ta tunanin yanda zai bullowa Mahaifiyar Aneesa dan tace da ita za'a kawo Aneesa ya lura mahaifiyar Aneesa ba san auren take ba. A haka har aka fara shagalin biki Sam baiso wani shagali ba dan shi kansa yasan ya girma da haka amma yaga Kan Aneesa na rawa dan dak'yar ya samu ya k'aucewa pre wedding din da ta dage masa suyi dan yana gudun Luba ta gani. A haka har aka daura Auren shi da Aneesa ranar jumaa akan za'a kawota ranar littinin. Washegarin daurin auren Alhaji Salis ya nufo katsina zuciyarsa cike da fargaba dan dole ya fada Luba da Hindatu Auren da zaiyi idan ya tuna tashin hankali da Luba tayi a auren shi da Hindatu sai yaji wani sabon tashin hankali ya rufeshi idan Kuma yak'i fada mahaifiyar Aneesa Suka kawota fa yasan halin Luba dambe za'ayi da ita. A lokacin daya iso gida Luba har wani cancada ado tayi dan itace da girki. Shima Alhaji Salis ranar ya saki fuskarsa Yana ta janta da hira dan yafi jinta akan Hindatu Luba kuwa sai falli take tana kyakyata dariya sabida ta kunsawa Hindatu bakin ciki ta kuwa ji Dadi tana jinta tana tsaki a Palo tana kananan maganganu. Shi dai Alhaji Salis har da yan adduoinsa a zuciyarsa kafin ya ruko hannun Luba da ta wani narke tana "Alhaji nawa Ni kadai" Ya saki murmushin karfin hali cikin dauriyar da ta zo masa yace "kinsan bawa bai isa ya k'aucewa kaddararsa ba ko Kamar dai yanda kike fada,auren nida ke Allah ya rubuta sai munyi Tom yanzu Allah ya kara kaddara min sake Aure a yau aka daura min Aure da wata yarinya Aneesa" "Kutumar uba Mai kace maimaita min naji"? Luba tace tana karkada kunnenta..... INGANTACCEN MAGANIN SANYI TOILET INFECTION MAI WANKO DUK DATTIN MARA KOWANI IRIN SANYI NE ZAI MAGANCE SHI DAYARDAR ALLAH SHIN KINAFAMA DA RASHIN SHA AWA? RASHIN NI IMA RASHIN GAMSUWA SHIN KINYI SHEKARA DA SHEKARU KINA NEMAN HAIHUWA RIKICEWAR JINI CIWON JIKI CIWON MARA YAYIN AL ADA DUKA WANNAN MAGANIN YANA WARKARWA ME CIKI BATA SHAN MAGANIN SANYI NA 4K YAKE INA KATSINA INA AIKAWA KO INA A FADIN KASAR NAN HARDA KETARE MAZA DA MATA MAGANIN SANYI MAI GYARA MU AMALAR AURE AUNTY ZEE MOM MUJAHID 08162859027 KATSINA *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* *Page 8* Luba Ta mik'e da sauri tana "Alhaji kaga idan Wasa kake min ka daina banaso kai yanzu ko sadakar mace aka Kara baka Kamar yanda aka baka waccan basumudiyar zaka yarda ka karba ne"? Salis ya had'e rai yana "Luba inaga ban tab'a miki zancen Wasa ba ko karki manta ba ke kadai ce matata ba yanda kike takamar ke matata ce kina Kuma so da kishina haka sauran ke sona Aure dai an daura min jiya ranar litinin za'a kawo ta aure dai da na Kara inaga ba haramun bane tamkar lokacin da kike fada da na aureki akan Karin Aure ba haramun bane tom inaso wanan waazin da Kika min a yanzu sai kiyi wa kanki Yarinya na aura baza'a samu matsala da ita ba idan Allah ya yarda" "Wlh kaci karya Salisu ka wulakantani har ni zaka cewa an daura ma Aure ka Kara cin amanata a Karo na biyu wancan jakar kace min tilasta ma ita akayi yanzu kuma baka ji kunya ba kace min an daura ma Aure ba ma neman auran kake ba sai da aka daura kazo kana fadamin bayan a yarjajeniyar da muka yi da Kai ba Karin Aure daga ni sai Aisha zaka zauna damu" "Ba inda muka yi yarjajeniya dake akan bazan sake Aure ba luba na gaji da tashin hankali da kukeyi a gidanan ke da Hindatu Kun k'i ku sama min nutsuwa Karin Aure Yana cikin kaddara ta ban isa na kaucewa kaddara ta ba nidai na fita hakkinki dan ban munafirce ki ba tunda it Aisha a lokacin da na aureki bama tasani ba har aka shekara da haka nayi mi ki sai kice naci amanarki na munafirceki dan haka ranar litinin za'a kawota banasan tashin hankali" "Idan ka isa Allah ya tsine min ka rasa lokacin da zaka Kara aure sai da na manyanta zaka auro yarinya karama ko kunya baka ji ba dan masifa ka ajiye mata har uku amma sai ka Kara auren ta hudu,a Ina kaga kwarin rik'e mata hudun mu ukun ma da cutuwa nakeyi ko gamsar da mutum baka iya yi kana daya zaka baje ka hau bacci inaga ka karo ta hudu,? idan su basa gamsar da Kai baka isa kace ni bana gamsar da kai ba dan rabin kudina a gyara suke tafiya, wlh Alhaji idan kana san zaman lafiya a gidanan ka janye auren nan idan ba haka ba wlh tallahi ruwa ma bazaka iya sha a gidanan ba Kuma ka jawowa Yar mutane balai dan wlh dukanta zan tayi har sai ta koma gidan iyayenta. "Wlh baki isa ki hanani Aure ba luba ba'a aurowa aka auroki a lokacin da kikeso na aureki ta karfi da yaji wane irin wa'azi ne baki min akan Karin auren ba? wane irin magana ne baki min ba dan kawai na aureki? Ashe Aisha ita ba mutum bace sai ta yanki jiki ta Fadi tunda ke kawarta ce na aureki ba kuma ki tab'a Jin komai ba kina ganin ma ai ba wani abu bane sai dan yanzu na Kara aure zaki min hauka. Wlh wlh Luba abinda na dauka a baya bazan dauka ba ayanzu kinji na rantse miki sai dai duk abinda zai faru ya faru" Ya mik'e fuuu yayi waje Luba ta bishi tana "Na rantse da Allah kuwa kayi auren nan sai na baka mamaki abinda nayi nima a baya kadan ne akan wanan da zanyi banda jarraba kana da manyan samari zaka Kara aure,kake hadani da jakar matarka ita tasan ciwon kanta ne nida ita ba daya bane wlh sai na baka mamaki wanan karon abinda kake gudu wlh sai ya faru ka Kara auren kagani" Alhaji Salis kuwa ko kallonta bai Kara yi ba yayi kwanciyarsa a dogon kujera Luba a ranar kwana tayi tana balai ko runtsawa Salis baiyi ba har sai da Hindatu ta fito taji labarin abinda ke faruwa itama ta kadu da Jin labarin aure zaiyi sai gashi itama ta hau masifa dan ita zaa yiwa kishiyar nan amma Luba ta fita Jin zafi. Aisha tana daga dakinta tana juyosu hayaniyar su, k'arfi da yaji sun hanata bacci sai tsaki take daga dakinta Allah yasan da tana da halin barin gidanan da ta bari dan wlh zaman dole take yi duk tsawon lokacin nan, tana mamakin Halin Luba da Hindatu ko gajiya basa yi da masifa. Karfe uku nayi ta mik'e ta daura alwala daga lokacin da Salis da luba suka saka mata hawan jini ta koyawa kanta samun nutsuwar zuciya ta hanyar mik'awa Allah lamarinta. Sai da taji fitar Salis massallaci taji sun daina hayaniyar. Salis bai dawo gidan ba sai da gari ya waye,ya mugun hade rai, yana Jin zuciyarsa na ingiza masa da ya Shiga d'aki ya rubutawa kowace saki uku ya huta kawai ya gaji da halinsu wani zubin sai yaga Kamar ya shake luba har sai ta daina numfashi. Ko kallon ita da Hindatu da suka hade kai suna kananan maganganu baiyi ba bai tab'a ganin sun hade Kai suna magana ba sai da ya kara Aure. Kasan zuciyarsa Kuma Yana fargabar su yi wani Abu su zubar Masa da mutunci a wajen dangin Aneesa su san irin zaman da yake yi dasu shi Kam da Yana da yanda zaiyi da ya hana zuwan mahaifiyar Aneesa da yasan da biyu takeso tazo gidan nasa. D'akin Aisha ya shiga da sallama bata d'akin Yana Jin motsinta a bandaki Hakane yasa ya zauna a gefen gadon Yana Jin inama ita kadai ce matarsa inama Yana da damar da zai maida hannun agogo baya,sai ya runtse idonsa yana tuno baya, tunanin daya tafi yasa kirjinsa nauyi Yana Jin tamkar a yanzu Luba ta shigo office dinsa ta canza masa rayuwa ta shigo cikin rayuwarsa daya kasa yakice ta har yau. Motsinta da yaji yasa ya bud'e jajjayen idonsa akanta. Inama Aisharsa ta dawo masa tamkar da ya rasa wancan Aishar wanan yanzu zuciyata ba komai Yana Jin karayar zuciya idan yaga yanda Aisha ta maida shi bashida bambanci da hoto a wajen ta har yau. Bai tab'a tunanin yanda yasanta da Hakuri zata yi irin wanan rikon ba. Sai da ta zura doguwar rigar ta tayi gaban mudubi da ido kawai yake binta tana nan a yanda take kyaun jikin da take dashi yasa ba mai yarda ta ajiye su Ashraf ko kad'an bata da kib'a shi har yau bai ga canjawarta ba rabon da yaga dariyarta kuwa har ya manta. Mik'ewa yayi ya nufi wajenta dan bata nuna tasan dashi a d'akin ba manta kawai take shafawa Yana zuwa ya rungumeta ta baya tare da runtse idonsa sai ta cire hannunsa daga jikinta ta,ta fara k'ok'arin barin gaban mudubin yayi sauri ya ruko hannunta "Aisha har tsawon wane lokaci zamu cigaba da zama a haka Aisha
Chapter 13 · 0% Book details