← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 71

Sashe 56

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daya kusa fasa masa kwakwalwa tuni yaji tunaninsa ya rabu gida biyu duk da bai ji zai iya ba haka zainab ta ringa kwadaita masa da kad'an kad'an ya fara harkar cocaine din har shima kudade suka fara shigo masa ta hada shi da masu kudin gaske. A haka watarana zainab ta kamashi da wata kawarta sukayi kaca kaca da ita dan har maganar Aure take masa wanda ko mahaukacin Kare ne ya cije shi ba abinda zaiyi da ita. Koda ya dawo gida Nigeria a haka ya cigaba da sana'arsa a boye ba Wanda yasani da larabawan nan da Zainab ta hadasu,a hankali suka fara masa maganar ya musu hanyar da zai na turo da Yan mata da samari zasu rubanya kudin da suke bashi. Tuni ya fara tunanin ta yanda hakan zai yu batare da an tab'a gano shi ba hakan yasa ya Nemo wata Hajiya fauza wata bazawara ya bata wanan kwangilar akan ta ringa musu hanyar zai na bata manyan kudi. Ita ta bashi shawaran ya bud'e gidan marayu su fake da taimakawa marayu da marasa gata idan yaso sai su fake da turasu kasar waje karatu suna turasu wajen larabawan. Da haka Salis ya hada kazaman Sanaa guda biyu idan Suka tura Yara waje da Sunan karatu wajen hajiya jidda da ta silar zainab yasanta a wajenta yaran ke sauka ita ke musu aikin daga can shima Salis na biyan ta John ke jigilar kai su yaran da suke kaiwa basa tab'a sanin ba karatun aka tura su ba sai sunje daga can shima sai an kwana biyu. Shi dai Salis direct shi ake turowa kudin. Kasa bud'e idonsa yayi a lokacin da ya gama bawa Ashraf labari Yana Jin Ashraf na sheka sallati shi kansa a zaunen da yake ji yake kamar kasa ta bud'e ya shige sabida kunya taya zai so mutane su san ba dan Allah ya bud'e wanan gidan marayun ba sai a yanzu yake matukar nadama da bai tsaya iya safarar cocaine din ba. Fitar Ashraf daga d'akin da karar rufe masa k'ofar da yayi yasa ya bud'e idonsa a hankali yasan a yanzu Ashraf ya tsane shi sai yaji Kuma Yana daya sanin bashi labarin. Luba Bata tab'a zuwa Lagos ba tasan dai garin akwai nisa ba kadan ba tun tana kalle kalle tana tunanin sun kusa isa Lagos har sai da tazo bacci ya d'auketa a motar karar bindiga da taji kamar a mafarki yasa ta bud'e idonta hankalinta a balain tashe duk fasanjojin motar su rude da ihu motarsu zagaye da kattin maza duk hanunsu rik'e da manyan bindiga har wasu ma sun shigo cikin motar duk fasinjojin sun durkusa akan gwiwarsu sun daga hannayensu sama yanda Luba taga sunyi itama haka tayi tana sallati tana "Allah karka Basu ikon ganin akwatin nan Allah ka rufamin asiri iya kudin nan da gwalagwalan su kadai nake dashi ya Allah ka rufamin asiri" Bata ma san a fili take adduar tana kuka ba sai da suka dora mata bindiga aka tayi saurin yun shiru suka cigaba da caje motar tsabar bata san ma a rabata da akwatin Bata yarda sun ajiye mata boat ba agaban ta ta ajiye akwatin. Jikinta rawa kawai yake a lokacin da suka fara k'ok'arin jan akwatin a sabida dukiyar nan ta kashe Asabe taya lokaci guda zata bari su rabata dashi. Rik'e akwatin tayi tana "Kumin rai dan Allah na baku Rabin kudin nan karku rabani da akwatin nan" na!!! Gindin bindigar Suka buga Mata akai bata Kara sanin Inda kanta yake ba,bata san tsawon lokacin da ta d'auka a sume ba sai da ta farfado ta ganta a wani waje kamar tasha idonta ya sauka a saman rubutun da akayi a wajen da take zaune this is Lagos shine your eyes" Zumbur ta mik'e ta fara dube duben akwatin ta har lokacin a cikin motar take amma ita kadai ba kowa da alama sun iso Lagos din. Ihu ta kwalla tana "Ina akwatina" Wani wada ne ya leko motar da broken yace "you Don wake up" (kin tashi" Since yesterday we Don reach Lagos since you Don wake up come down come dey go your house (tun jiya muka iso Lagos tunda kin farka sauko ki tafi gidanki) "Ina jakata"? Luba tace a haukace tana cigaba da dube duben motar ko ciwon da taji kanta nayi bataji ba haukace musu tayi da kuka da ihun sun bata Jakarta ita bazata sauka ba. Tuni mai motar ya watso da ita daga motarsa wayarta ma sun d'auke hannu ta dora aka ta fara kuka wiwi tana asirinta ya tonu... Naceba Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195 Call:08064532391 Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida tested nd trusted Natural/organic Ayiri yiri kuna Ina mata matafa nake nufi bamuna mataba A&Z COLLECTION takawomuku ingantatun supplement Muna da supplement na Infection Munada da supplement na gyaran jiki Wanda zaisa jikinki yayi kyau fata tai laushi da sheki munada na gyaran breast succiko su tashi tsaf gwanin Sha awa munada na matsi dazai matsaki ciki dawaje bawai ki iya farkoba kuma yasaukarmiki da ni ima Muna da na gyaran gashi Wanda zaifitomiki da gashi Dawanda zakiyi haske duka jikinki bawai fari na bleaching ba A&Z dealer ce kayanmu suna da sauki sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayanmu cikin sauki alhmdulillah Ga kadan daga ciki 1 Royal jelly karami 2500 2 Juliet Eve 8500 3 Amirna 8k 4 Vitamin c 2500,2300 5 vt e 2k 6 collogen + glutathione 2k 7 whitening gummies 2200 8 surga wanita 2500 9 khusus 3500 10 majakani 2500 Price din sari nasan kodaga haka zaku gane A &Z gidan sauki ne Masu siyan daidai kuma bambancin kadanne Muna garin Kano Dan neman Karin bayani Kira ko whaspp 09037870422 Karku manta muna tura Kaya duk garin dakuke inkiyi siyayyama dayawa muyi Miki free delivery yan Kano kayanku har kofar gida cikin aminci *WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN* *+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA* *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *PAGE 31* Luba Ba Wanda ya bi ta kanta haka aka ringa wuceta tana kuka wiwi sarkokin asabe sun kai guda biyar da ta d'auka ko iya su kawai sun isheta rayuwa kudi kuwa zasu yi Dubu dari shidda sabida kudin ta kashe Asabe sai gashi tashi daya barayi sun rabata da komai daga ita sai hijabin jikinta da atamfar jikinta,duk kukan da take tana birgima ba Wanda ma ya tsaya ya tambayeta mai ke faruwa ballantana ta sa ran zata samu taimako a wajen wani, hasali ma wani ma tsawa ya daka mata a akan ta koma gefe ta zauna a bakin hanya da ace tasan haka legas yake da bata soma zuwa ba da tasani ma Abuja ta tafi,wanan wane irin rashin saa ne. Haka ta koma gefe tana cigaba da kuka da kalle kalle bata San daga Ina zata fara ba wajen wa zata dosa ba wanda ta sani a Legas ballantana tace zataje ta nemi taimako Rabin mutanen ma da take gani duka yarabanci suke sai turanci,bata ga alamar bahaushe dan uwanta ba. Tsawon awa shidda tana zaune ga kaikaiyin da ya dameta,ga mugun ciwon Kai,sai a yanzu take nadamar ma kashe Asaben da ta sani ta rufawa kanta asiri ta cigaba da mata wanke wanken tana jurewa,da ta sani ma iya kudin ta kwashe ta kulle Asabe a bandakin da kila duk bata tsinci kanta a cikin wanan balain ba. Mik'ewa tayi tana cije lebbenta sabida kafafunta da taji suna mata ciwo zaman waje daya bazai kareta da komai ba gwara ta bazama neman taimako ko zata dace. Fitowa tayi daga tashar tana cigaba da dube dube garin Legas din ma a hargitse ta ganshi kowa ta kansa yake tasan da ace wani garin taje da an samu mutanen da zasu tambayeta Mai ya sameta take kuka haka. Tafiya kawai take batasan ma Inda zata dosa ba motoci da babura ma kamar sunfi mutane yawa haka take gani. Wani waje ta hango da ake siyar da abinci ta nufi wajen tana Addu'a Allah yasa bahaushiya ce mai wajen,Koda ta isa da muryarta data dashe ta hau sallama. Sai dai ba Wanda ma ya dago ya kalleta Yan Mata ke ta kaiwa suna kawowa da abinci suna sallamar mutane duk da ga shigarsu tasan ba hausawa bane ba Kuma musulmai bane dan guntun skirt suka saka. Sai da ta Shiga ciki daya daga cikin Yan matan ta waigo tana tambayarta mai zaa bata da harshen turanci. Luba bata iya turancin sosai ba amma duk abinda zaace tana ji "Taimako nake nema Dan Allah Ina Mai wajen take"? Wani irin kallo yarinya ta mata da tasan ilham yarta ma zata girmeta Da turanci tace mata idan ba abinci zata siya ba ta fita ta bata waje ta barta a tsaye. Duk abinan wayanda suke wajen suna cin abinci ba Wanda ya dago wai ya kalleta ballantana su san taimako take nema Kuma ko magana zasuyi yarabanci sukeyi. Tana ji tana gani Yan matan nan suka koreta gashi magriba ta kawo kai yanzu ta inda zata kwana kafin ta san nayi take dan legas ba wajen zamanta bane gwara ta nemo taimako
Chapter 56 · 0% Book details