Sashe 66
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Luba ke tsaye ya tsaya suna fuskantar juna. Sai da Alhaji Salis yayi rantsuwa akan zai Fadi gaskiya magatakarda ya koma ya zauna Ashraf ya tsaya a gabansa ya dago suka hada ido da Aisha da tayi saurin kau da kanta. Karo na biyu da ya Kara tsintar kansa cikin tsananin kunyar abinda ya aikata sai yaji a ransa gwara ya Fadi iya gaskiyar abinda ya sani. ASHRAF kuwa dakewa yayi Kamar ba mahaifinsa ba dan a binciken da yayi zai Kara wanke Salis ne a fyaden da yayi wa muhasim a wajen Aisha da Yaya mustapha. "Alhaji ko zaka iya fada mana wane danganta ne tsakanin ka da wacce ake Kara"? "Tsohuwar matata ce kawar kuma matata uwar yayana" "Naji kace kawar matar ka ce Kuma ka aureta,shin Auren soyayya kuka yi ko kuma dai Auren ta kayi sabida ta rufa maka Asiri game da zargin da ake ma akan kayi wa yarinya fyade?zaka iya gayawa kotu yanda aka yi Kuka yi Aure"? Ya Kuma akayi kayi wa muhasim fyade"? "Ita dai Luba kawar matata ce zan iya cewa Aminiyarta ce a lokacin da muka yi aure ita batayi ba sai daga baya,ni Kuma a lokacin bata jima da auren ba na samu scholarship na fita waje Kara karatu. Ta silar matata na santa matata na mugun santa da har nake ganin bata kaunar b'acin ranta akan nawa,daga baya ma na lura ita kawartata ba matuniyar arziki bace ba sabida halayensu ma bai zo daya ba,tana da san kai da san abin duniya,a lokacin da ta kashe aurenta sabida mijinta bashida hali naso rabata da matata dan duk Wanda zai rabu da kai sabida babu ba mutumin arziki bane ba. Koda na nemi matata ta rabu da ita k'i tayi a san na faranta mata na rabu da ita badan Raina naso ba dan gani nake yau da gobe zata iya sawa matata ta canja hali itama. Tiryan tiryan Salis ya bada labarin yanda Luba ta hau bibiyarsa yana wulakanta ta sabida bazai iya auren cin amana ba har zuwa yanda Suka tare a sabon gida ta saka masa magani a ruwa ya Kara da "ta karfi da yaji takeso na aureta ko ta halin Kaka ko a yanzu inada gajeran recording din abinda ya faru a d'akina dan nasa k'aramin recorder a saman d'akina,idan kotu na bukata zan iya kawowa sabida aga shaidan yanda tazo d'akin nawa,tunda ga lokacin na Kara tsanarta na matsawa matata akan ta rabu da ita amma tak'i rabuwa da ita" dan har ta gwammaci b'acin raina da na kawarta haka ta cigaba da zuwa office dina tana nacin sai na aureta a irin wanan yanayin na wayi gari cikin tsananin bukata da har fita nake a hayyacina idan ban samu nutsuwa ba,a haka watarana Ina tsaka da aiki abin ya motsa min nazo gida Koda nazo sai ban samu matata ba Allah shine shaidata bansan mai ya faru ba sai da na dawo hayyacina naga Ashe muhasim na nema da tana da bakin da zatayi magana da kotu tayi mata tambaya, tundaga lokacin na rasa kwanciya hankalina na rasa mai yake min Dadi,yarinya tabar gidana dan dama a gidana take zaune. Wata biyu a tsakani tazo ta sameni akan bata ga Al-adarta ba naso ta zubar da cikin dan abin kunya ne ace ni da kaina nayiwa Yar yayan matata ciki,sai tak'i bani hadin kai a zubar da cikin a lokacin Kuma Luba ta matsamin da zuwa office dina A takaice tiryan tiryan Salis ya bada labarin komai bai boye komai ba har yanda Luba tazo ta same shi akan tasan shi yayiwa muhasim ciki ya Kuma yi mata fyade Inda tace Masa idan bai aureta ba sai ta tona masa asiri ya Kara da "Ni nasan ba wani shakuwa suka yi da yarinyar ba sai idan tazo gidana ma take ganin yarinya bansan ya akayi tasan mai ya shiga tsakanina da yarinya ba,naso na zargi ko tana da sa hannu a halin da na tsinci kaina na yawan bukata tunda ta tab'a saka min magani sai Kuma na cire zargin haka a raina amma Allah shine shaidata baa cikin hayyacina nayiwa muhasim fyade ba zan iya dafa al Qur'ani na rantse" "A lokacin da ta ringa bibiyar ka tana sanka har ta saka maka magani a ruwa a ranar da kuka tare a sabon gida shin ka fadawa matarka abinda ya Shiga tsakanin ku?sanan Ina matar taka take a ranar da batasan duk abinda ya faru ba"? "Ban fada mata ba dan gani nake bazata tab'a yarda Luba zata ci amanarta ba dan ta bata yarda dari bisa dari sanan a ranar da ta fara saka min magani a ruwa ta bawa muhasim ta kawo min a ranar muka tare a sabon gida da yan uwan matata da yawa a gidan hakane yasa tace min zata kwana cikin Yan uwanta a ranar ba a dakina ta kwana ba" Ashraf gyada kansa yayi yace zai iya komawa ya zauna ya juya ya kalli alkali Yana "Ya mai girma mai Sharia inaso kotu ta nazarci maganar wacce ake Kara da shi Alhaji Salis daga abinda ya faru zaa gane dole wacce ake Kara tana da hannu a cikin abinda ya samu yarinyar dan yarinya bata da wani kusanci da ita,da zata ringa zuwa wajenta tana fada Mata halin da take ciki,na biyu idan har dagaske yarinya ce ta fada mata shi Alhaii ya mata fyade idan ba dama tana da wani manufa a zuciyarta ba ya Kamata ace ta sanar da kawarta halin da yarinyar take ciki sai bata sanar da ita ba,daga maganin da ta saka wa Alhaji a ruwa sabida ya sadu da ita kotu zata gane zata iya yin komai domin ta samu cikar burinta dan haka inaso kotu ta sake bani dama zan kira Hajiya Aisha na mata wasu tambayoyi" "Kotu ta baka dama" Aisha tunda taji labarin duk abinda ya faru daga bakin Salis tayi mutuwar zaune ta ringa komawa baya tana tuna duk yanda Luba ta ringa sintirin zuwa gidanta da irin kallon da take bin Salis dashi a hankali komai ya fara dawo Mata na yanda Salis ke iya k'ok'arin sa wajen ganin ya rabasu. Jiki a sanyaye ta mik'e ta nufi wajen da ake tsayawa ta tsaya tana kallon Luba da ta jike da gumi tana mata wani irin kallo,ko kad'an bataji ta wani tsorota ba tasan Ashraf bashida shaidan komai, idan har ta kafe akan karya yake ba yanda za'ayi kotu ta Yanke mata hukunci har sai an samu shaida. Bayan Aisha tayi rantsuwar zata Fadi gaskiya ASHRAF ya tsaya a gabanta Yana "Hajiya Aisha ko Zaki iya fada mana mai alakarki da wacce ake Kara"? tiryan tiryan Aisha ta kwashe komai ta fadawa kotu daga alakarta da Luba har zuwa lokacin da ta wayi gari ta aure mata miji ta Kara da "A duk abinan dake faruwa bata tab'a nuna min tasan Wanda yayi wa muhasim fyade ba,bata tab'a nuna min ma tasan muhasim nada ciki ba, shiyasa a yanzu da naji tana cewa tasan har muhasim nada ciki har muhasim taje wajenta kaina ya kara daurewa, dan a gidana take ganinta su gaisheta tunda aurenta ya mutu bata tab'a zuwa gidan yayana ba a gidana dai muke had'uwa har a wane lokaci ta samu kusanci da yarinyar da zata ringa zuwa wajenta tana fada mata halin da take ciki ya mai girma mai Sharia Ina rokon kotu ta taimaka wajen bincikar ta dan Muhasim nasan bazata tab'a tararta ta fada Mata halin da take ciki ba sai dai idan ba dama tasan abu ya Shiga tsakanin muhasim da mijina ba har ta Kuma gano tana d'auke da juna biyu ba" Aisha ta karashe tana share hawaye dan a yanzu ta yarda Luba tana da hannu a abinda yasamu muhasim. "Ya isa hajiya Aisha kotu zata miki adalci insha Allahu tambayar da zan miki a yanzu shine shin kafin ku gano anyiwa muhasim fyade dagaske ne akwai lokacin da mijinki ya tsinci kansa da yawan bukata da sai ya samu nutsuwa yake dawowa daidai" "Eee hakane Rana daya na wayi gari naga yana yawan bukata har yakan dawo gida sau biyu haka ko sau uku" "Dama can haka yake ko Rana tsaka ya wayi gari a haka"? "A gaskiya ba haka yake ba dan daga ni har shi lokacin muna ta mamakin yanda akayi ya tsinci kansa da yawan bukata"? "Kuma baki zargi ko wani abu yaci ko ya sha dayasa shi wanan bukata ba"? "Aisha shiru tayi ta tafi tunani mintuna a tsakani tace "Wlh bazan iya tunawa ba nadai san a ranar yaci tuwo daya dawo gida daga ya Shiga sama yayi wanka ya birkice min" "A ranar kinyi bakine kafin ya dawo"? "Aa Luba ce dai tazo gidan a ranar Tama dage min sai ta tayani girki,baa san raina ba nabarta tayi girkin dan Salis baya yarda yaci girkin da ba nawa ba" "Kina nufin a ranar da kika fara ganin canji a wajen mijin naki Luba ce tayi girkin da yaci batare shi yasani ba".? "Eee a ranar ita tayi min girkin" Ashraf ya gyada kansa cikin gamsuwa Aisha ta hada tambayoyin da ya mata ta Kara tuna a ranar da Luba ta dage zatayi girki a ranar Salis ya canja ta gwalo ido tana kallon Luba tare da nunata da hannu tana "wlh ita tayi girkin da yaci a ranar har ya canja sai a yanzu na tuna innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" "Zaki iya komawa ki zauna" Ashraf yace Yana "ya mai girma mai Sharia iya hujojin nan ya isa yasa kotu ta gane hajiya Luba tana da hannu dumu dumu a cikin abinda ya samu muhasim dan sai da taje gidan tayi girkin da shi Alhaji Salis yaci ya zama mabukaci sosai,Wanda kila tayi hakane sabida ta Kara samun damar da zai kusanceta sai Allah baiyi ba har abin yazo da tsautsayi yayiwa Muhasim fyade na biyu duk yanda take da Hajiya Aisha da sintirin da take yi a gidan ko a fuska bata tab'a nuna mata tasan anyiwa muhasim fyade har ta samu ciki ba,Kuma bata da kusanci da muhasim da har zata saki jikinta da ita ta fada mata halin da ake ciki idan ba