← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 71

Sashe 58

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195 Call:08064532391 Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida tested nd trusted Natural/organic *WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN* *+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA* *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *PAGE 32* Luba Matar da dan acaba ya kai ta wajen ta, kwana biyu kawai tayi ta fara masifar yaushe zata tafi duk da biyayyar da take mata tana bauta mata ta hanyar yi mata aikace aikace wai duk dan kar ta gaji da ita,abincin ma kanzo take zubo mata,haka yaranta zasu ta mata rashin kunya a yau ma tana rabe a gefe wani dan ta yazo yabi takan kafarta ya wuce olu taji tana kiransa dashi da gangan ya taka ta dan yaran matar duk basu da tarbiya sabida bata Jin turanci suke ce mata aboki ta lura hausawa suke cewa aboki,tuni taji zuciya yazo mata bata san sanda ta mik'e tsaye ta jawo shi tare da gaura masa mari ba ya tsalla wani uban ihu har sai da matar ta fito daga dakin ta da gudu da harshen turanci tana waye ya tab'a shi,sai a lokacin Luba tasan ta kwafsa ita da ake taimaka wa mai ya kaita tab'a dan masu gida. Da turanci da hausa ta hau bayanin dan ta kare kanta a lokacin da matar tayo kanta tana masifa da turanci akan daga taimako zata zo har tana jibgar mata d'a,kafin ta Ankara ta kwasheta da mari,karshe sai da suka yi mata taron dangi da yayan suke jibgeta tare da watso da ita waje. Luba haka ta hau neman taimako tana kuka zuwanta legas bai zame mata alheri ba sai sharri gashi dan acaban da ya kawota bai cika alkawari ba wajen waiwayarta. Duk yanda taso samun wajen kwana da taimakon mutane bata samu ba haka ta cigaba da dab'awa a kafa duk da bata san Inda zata je ba,tasan dai ta fito kamar cikin gari sabida wajen da ta b'ullo akwai yawaitar jama'a a wajen,Yan acaba tagani kaca kaca a wani karkashin gada,ga masu siyar da abubuwa da yawa haka kawai taji sanyi na ratsa zuciyarta dan ta fara hango yan uwanta hausawa a karkashin gadar da sauri ta tsallaka duk da batasan wajen wa zata je ba taje ta samu inuwa ta zauna tana huta gajiyar tafiyar da ta sha a k'afa dan ta kusa fin awa tana tafiya a zaunen da take tana ta karewa masu siyar da abinci kallo rabin su ma hausawa ne da alama zaman legas yasa Suka koyi turancin broken da yarabanci. Wata ce tafi d'aukar hankalinta dake ta hada hadan siyar da abinci Yan acaba sun mata rubdugu suna ta siyan abinci,bere taji suna ta kiranta ta basu abinci na kaza ta basu abinci na kaza,Kamar ita kadai ke siyar da abinci a wajen sai da mutane suka ragu sosai,Luba ta mik'e ta nufi wajenta "katuwa ce Yar lukuta mazuanan ta kamar ba na mutane ba,sabida girma duk tabi ta cika kujeran,lebbenta bakine sosai Kamar mai Shan sigari. Luba gefenta taje ta hau gaisheta cikin sakin fuska ta juyo tana amsawa tana mai za'a Baki"? Luba labarin yanda ta gamu da tsautsayi ta bata ta bata labarin komai tare da fashewa da kuka tana "Ni a yanzu Wanda zai bani kudin mota na koma garin mu nake nema wlh bazan iya rayuwa a garin nan ba Hajiya idan da akwai yanda zaki taimaka min dan Allah ki taimaka min ni ko wanke wanke ne na ringa miki har na tara kudin komawa garin mu" Dariya matar ta saka tana "Ba kince kudi kika zo nema ba sabida me Kuma zaki hakura ki koma garin ku?ai legas gidan kazo nazo kenan legas gidan bariki idan baka iya bariki ba ka Shiga uku zan taimaka miki idan Allah ya yarda ba sai ma kin min wani wanke wanke ba a yanzu dai bari na zuba miki abinci kici" Luba washe baki tayi ta hau yi mata godiya rabon da taci abinci mai yawa da dadi haka zata iya cewa tun tana gidan Salis dan har nama ta saka Mata. Koda ta koshi haka matar ta hau janta da hira kamar irin ta santa dinan,abinda ya d'an daure Mata Kai da ita bai wuce yanda take tafawa da maza har wasu na kai mata duka duwawunta ba,haka dai suka zauna duk da abincinta ya Kare bata tashi sun tafi ba ta cigaba da hira da maza ita dai Luba wani irin rayuwa take gani da bata saba gani ba dan matar ta manyanta bai dace ta ringa Abubuwan da take ba. Bacci kawai take ji ga fitsari da ya matseta da kaikaiyi bata ga alamar akwai wajen da zata iya fitsari ba gashi dai ta gama siyar da abincin amma tak'i tashi su tafi,sai nunawa maza take ita tana ga kanwarta nan. A takaice basu bar wajen ba sai wajen Sha biyu na dare ita ta taimaka mata ta d'auki wasu kayayakin ta ta d'auka ko zasu hau acaba sai taga da kafa suka ringa takawa basuyi wani tafiya mai nisa ba suka iso wani katon gate da tun kafin su karasa taji kida na tashi Luba ita dai zare ido kawai take tana kalle kalle har suka shiga ciki dan bata Jin ma gidane dan da suka shiga wawakeken fili ta hango da speakers wasu na tsakiyar fili suna rawa ita dai sakin baki tayi tana kallo matar da ta biyo da taji ana cewa bere ta ringa yiwa maza magana ita dai sam bata gane Inda ta kawota ba dan bata ga alamar gida ba so take mata tambaya amma tana tsoro ita kam taga rayuwa da mutuncin ta da komai sai gashi ta jawowa kanta garari a titi da kila bata yi haukan da tayi ba da kila tana can gidan Salis tana zuba mulkinta san ranta. Duwawunta da taji an kaiwa duka yasa ta waiga da sauri taga wani ne kato ta bayanta hannunsa d'auke da sigari yana "Bere wanan cikar fa"? "Kai bakuwata ce bana san iskanci ku ba dama kuga bakon fuska kizo ki wuce mu tafi kinji" "Hajiya duwawuna ya kawowa duka fa wanan wane irin iskanci ne da Aurena da komai" "Au kina da Aure dama"? "Inada Aure mana hajiya" "Toh mai kikazo yi a legas" "Kudi nazo nema hajiya dan mijin nawa baya nan guduwa yayi ya barni" "Kuma garin ku bai isheki Neman kudi ba kika taho legas,ai shikenan biyoni muje" Luba bin bayanta ta fara yi har lokacin tana ta mamakin matar ita dai taga Kamar dai matar Yar duniya ce duk da ta manyanta ta Ina zata soma irin wanan rayuwar da girman ta da komai. Wani irin kumbul kumbul dakuna Suka ringa wucewa ta baya ko kad'an bata kawo wai akwai wajen Zama a wajen ba har sai da suka zo gaban wani daki da aka kulle da kwado. Ta sauke farantin kanta ta d'auko mukuli daga cikin jakarta ta bud'e tana "Bismillah" Luba binta tayi cikin d'akin bashida wani girma sosai sai tarkacen kaya da katifa da aka saka a kasa. "Nan shine dakina anan yawanci irin mu masu Neman kudi muke haya sabida bashida wani tsada ni a kyauta ma nake zaune dan haka kafin kisan Kan komai Zaki zauna anan kafin ki Saba da komai" "Hajiya naga Kuma ana ta kida a gidan" "Toh ai gidan drama ne nan ta baya aka bada haya ai bazan iya Kama gida a legas ba nan shine daidai karfin talaka kowa rayuwarsa kawai yake anan ba ruwan kowa da kowa karki wani damu a hankali Zaki Saba" Luba shiru tayi badan ta gane bayaninta ba a karantar dai da tayi matar ba matuniyar arziki bace daga ma yanda ta ringa cin Karo da maza da Mata. "Kwanciya zakiyi ko zaki dan watsa ruwa"? "Da zan samu na watsa ruwan da naji dadi dama ko sallah banyi ba" A takaice ita ta rakata wajen bandakin da ba rufi sai k'ofar kwanu duk da ta kulle k'ofar a tsorace take da sauri sauri ta ringa watsa ruwan dariyar da taji a saman katangar bandakin yasa ta dago da saurinta wani ne ya mata kuri ta katangar Yana kallonta kamar ya samu tv,da sauri ta jawo zaninta ta rufe jikinta tana "Allah ya isa uwarka kake kallo bani ba" Dariya tya kyalkyale dashi har ta fice daga bandakin da gudu a hanya ma sai da ta hadu da wani ya dumbula mata nono da gudu ta karasa d'akin tana Shiga ta fara "Hajiya dan Allah ki rufa min asiri idan akwai wajen da Zaki maidani ki maidani wlh bazan iya wanan rayuwar ba da girmana da komai da manyan yarana ake biyoni ana tab'a ni wani har da lekena hajiya nidai ki taimaka min dan Allah bazan iya ba" Dariya bere ta saka sai da tayi mai isarta tace "ikon Allah ni yanzu ban miki k'ok'ari ba ban sanki ba nayi niyyar taimaka miki naga kuma kina Kara neman wani taimakon legas kika zo fa banida wajen daya wuce nan a hankali ma zaki Saba idan kika ga bazaki iya ba Kuma nayi iya k'ok'arina zaki iya saka kayanki ki tafi" "Kiyi hakuri hajiya banida mai taimaka min amma Ina neman arziki ki musu magana kice musu ni matar aurece" Dariya ta saka tana "idan kikace kina da auren nan dariya
Chapter 58 · 0% Book details