← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 71

Sashe 12

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lafiya kuwa kinsan baa nan take aure ba. Nidai abu daya danasani boye miki da yayi bai kyauta ba abin na ta damuna taya zaace a boye miki kinsan bana boye miki komai shiyasa na yanke fada Miki wlh sabida halin rayuwa baa san gawan fari ba yazo ya Fadi ya mutu ke bakisan da auren ba Yan uwansa basu sani ba azo rabon gado ace baa san zance ba wlh shiyasa na fada miki dafatan hakan bazai saka wai mu yanke kawancen mu ba kawai mu rungume mijinmu mu faranta masa" "Luba baki kyauta min ba baki min adalci ba Luba da ace nasan abinda zakimin kenan wlh da bansoma yarda da aurenki ba yanzu da wane ido kikeso na kalli Aisha wane bayani zan mata ta gane Aisha fa kawarki ce karki manta" "Ikon Allah wai haramune auren nawa ka isa ka aureni ne idan ni din ba matarka bace wlh bana Jin dadin abinan da kake yi kamar kana tsoron Aisha magana ce fa ta fatar baki kayi abu kamar namiji Mana idan bamuyi aure ba Ina zaka Kai rabon dake tsakanin mu zata hana abinda Allah ya hallata ne kaga mallam nidai ka zaunar da ita ka kara.mata bayani kai ya Kamata kayi mata magana ka barni da mata magana Haramun muka aikata kake ta sallati naga dai sai da ka bada sadaki aka daura mana aure kamin lefe ka aureni da daraja to na me a yanzu zaka ringa kame kame agabanta mtssss nidai na baku waje kuyi magana bari na sa a kawo mata abinci. Ta nufo wajen k'ofa ta karkata ta wuce dan a bakin k'ofar na daskare a tsaye kallon Salis kawai nake Yana ganin ta fita yayi sauri ya juya bayansa duk da duk abinan bai dago mun hada Ido ba sai sallati da yake Yana Aisha kiyi hakuri dan Allah nasan ban kyauta ba dan Allah kiyi hakuri" Zuciyata wani irin kunna take na kasa gasgata wai Salis da ya balain tsanar Luba shine yau a matsayin mijinta wai har ya mata ciki ta haihu ashe duk tsawon lokacin nan ninkeni baibai suka yi soyayya sukeyi a gaban idona yake nuna Mata kiyayya kawata aminiyata da ba abinda bata sani akaina ba itace Salis ya Aura a matsayin kishiyata,ashe dadewar da Salis yake yi a Abuja sabida auren Luba da yayine yana nan da kawata Yana Shan soyayya sai ya mata sati biyu uku ya dawo wajena na tafi kunshi nayi ado nayita girke girke Ina murnar tarbar mijina Ina tunanin yanda nake dokin kasancewa dashi haka yake dokin kasancewa dani sabida an dade baa hadu ba,idan ya iso kuwa jikina yayi ta rawa kawo wanan d'auko wancan ni ga mijina ya dawo sai dare yayi yace min a gajiye yake likis cikin tausayi zan raba dare Ina masa tausa dan nasan duk sabida nida yarana yake Neman kudi ashe baccin gajiya da kawata ta tara masa yake, sabida kaunarta da yake ya kai ta abuja sabida ma Kar tayi nisa dashi. Na d'auke kallona daga kan shi na maida Kan jaririya Wai Salisu ne yayi wa Luba kawata ciki,na runtse idona hawaye na gudu a fuskata kirjina kuwa kamar ya fado Ina Jin numfashi na min wahalar shak'a,na runtse idona dana tuna lodin magungunan da na bata da Sunan ta jiyar da mijinta dadi har tana cemin a waya mijinta ya isheta da jarraba sabida kyan maganin ko aiki yaje sai ya dawo yayi, Ashe Salisu ne ya isheta da jarraba Ashe Salisu take bani labarin yanda yake santa kamar ya hadiyeta har Ina Jin na raina san da nawa mijin yake min. A daidai lokacin da Luba ta dawo d'akin da farantin abinci ta ajiye a gabana tana "baki gaji da tsayuwa bane ki zauna mana nan ma fa gidanki ne kin kwaso gajiya kici abinci sai ki watsa ruwa kizo kiga diyar taki. Sai Kuma ta sunkuya ta d'auki abincin da bansan wane kala bane dan wlh a yanzu tsananin mamakin Luba Kuma nake tana ta abu Kamar irin ba komai dinan ta nufo gabana dashi tana "kawata wai me haka dan Allah" Har lokacin hawaye kawai ke zubomin kalmar kawata da tace yasa na Kara Jin kirjina yayi nauyi kawata Luba dai itace yanzu matar salis har suka haihu tare magangaunta suka Kara dawo min "wlh karka sake cewa baa san ranka ka aureni ba da san ranka sarai ma,dan da baka sona da bazaka kwanta dani har na haihu ba sai na runtse idona tare da cije lebbena da baka sona bazaka kawoni Abuja wajen da kake aiki sabida Kar na nisance ka ba" Sai naji hannunta saman hannuna "zoki ci abinci nidai matan abokanan Salis suna ta jirana Kinga ba dadi na barsu su kadai" Sai na fusge hannuna daga nata hawaye sai gudu yake a fuskata na ma rasa Mai zance mata na bud'e bakina da kyar Ina "Luba mai na miki dana cancanci irin wanan cin amanar daga wajenki Luba duk mazan duniyar nan ki rasa Wanda zaki aura sai Salis mijina Luba"? Idan shi baiji kunya ba bai san ana barin halak dan kunya ba ke Sai ki biyeshi ki aureshi kina matsayin kawata aminiyata Luba ki auri mijina shekara guda batare da nasani ba"? Duk maganar da nake hawaye kawai nake muryata na rawa Sai ta turo dankwalinta gaban goshinta tana "Tambaya daya zan miki ki bani amsa, Haramun ne dan kawa ta auri mijin kawarta?idan har Kika kawo min Inda aka haramta auren mijin kawa ni Kuma na Miki alkawari Zan saka ya sakeni Aisha dama haka kike ke yanzu wani abune dan mijinki ya aureni"? Bansan ya akayi ba na ciri hannu na d'auketa da mugun mari kafin ta dawo daidai na kara d'auketa da wani marin kafin na sauke hannuna naji tayi sama dani ta makani da kasa a daidai lokacin da naji duhu na neman rufemin ido numfashina na k'ok'arin d'aukewa naji sallatin Salis sama sama ban Kara sanin Inda kaina yake ba. Sai bud'e ido nayi na gani a gadon asibiti da Karin ruwa a hannuna sai da na dau tsawon mintuna kafin na tuna abinda ya faru na maida idona na rufe Ina Jin bugun kirjina da kuguna dake min ciwo inaga bugani da kasa da Luba tayi ya haddasa min ciwon. "Sannu Aisha kin farka"? Naji muryar Salis a kaina banasan ganinsa haka yasa ban bud'e idona ba" Ina jinsa ya zauna a gefen gadon murya na rawa ya hau magana "dan Allah dan Annabi kiyi hakuri Aisha wlh nasan ban kyauta ba amma wlh tallahi bana kaunar Luba kaddara ce tasa mu kayi aure wlh baa san raina ba kwanciyar da take magana wlh magani ta saka min a lemo wlh wlh bana kaunarta kinsan bazan tab'a cin amanarki ba,wlh tunda na aureki ban tab'a kallon wata mace naji Ina santa ba bayan ke wlh matsayinki daban yake a zuciyata ki yarda dani matata kar ki bari shaidan ya rabamu wlh burin Luba taga mun rabu dan Allah kiyi hakuri na yarda ki min kowane irin hukunci. Wlh kamar feshin wuta haka nake Jin maganganunsa a kunnena daga lokacin da na saka kafa a d'akin na hangosa a d'akin na tabbatar da zargina naji sansa na ficewa daga zuciyata tsananin tsanarsa na mamaye min zuciya babban burina yanzu nagani a gidan yayana dan wlh na gama auren Salisu. Ban tabbatar da muryata zata fita ya jini ba nace "Allah ya isa tsakanina da Kai Salisu wlh har duniya ta nade bazan yafe maka ba duk matan duniya ka rasa wacce zaka Aura sai Luba da kasan kawata ce Aminiyata ySalisu ka aureta ka b'oye min har tsawon shekara guda ka daukota ka kawota Abuja baka Santa kayi mata ciki ta haihu kayi taro tare da gayyatar abokanan aikinka da matansu,ashe Sabida ita ne baka zuwa wajena sai ka shafe sati biyu ko uku baka zo ba,na maka maganarta ka zageta Salisu kawata fa wanan wane irin cin Amana ne Wlh bazan yafe ma ba" Na fashe da wani irin kuka zuciyata na min k'unna Hakuri ya cigaba da bani ko muryarsa banaso naji na saki ihu akan ya fita banaso na gansa. Ina jinsa ya tashi. Rashin kwarin jiki yasa ban fusge ruwan daga hannuna ba dan burina yanzu naga na bar garin. A takaice washegari wani likita yazo dubani Ina kallon Salis a rabe a jikin kofa. Tun jiya wlh hawaye bai tsaya min ba idan na tuna irin cin amanar da Salis da luba suka min. Koda likita ya gama dube dubensa naga ya cire min robar ruwan da Ina tunanin na Sha ya kai biyar mik'ewa nayi zaune cikin muryata da bata fita sosai nace "Likita ka sallameni tafiya zanyi" "Hajiya ai baki warke ba ya kallo Salis dake bakin k'ofa Ina tunanin dai asibiti daya suke aiki. Ni kuwa ban bi takan likitan ba na Mik'e zaune Ina dube dube duk ji nake kamar iska ya d'aukeni Ina ganin mayafina na d'auka tare da cije lebbena sabida kaina da naji ya Sara min. "Aisha Dan Allah ki bari kiyi hakuri bakida lafiya ki bari gobe sai na Kai ki gida da kaina jininki fa ya hau Aisha dan Allah ki koma ki kwanta. Kafata ba takalmi inuwarsa ma basan kallo nake ba nayi hanyar wajen. Ya sha gabana da sauri kallon da na masa yasa ya bani guri nayi waje Ina jinsa a bayana Yana "Aisha ba inda kika sani a Abuja kizo muje gida Dan Allah dan Annabi gobe sai mu tafi. "Inzo muje gidan Luba ko Salisu"? Sai yayi shiru Na girgiza Kai na cigaba da tafiya duk da nasan bansan ma Ina ne Tasha ba amma dai matambayi baya bata. A takaice taxi na tare akan ya kaini Tasha. Ina Hawa Salis ya Shiga shima Yana ta magiya. Shattar mota na dauka ni kadai duk yanda Salis yaso bina na hana driver daukarsa. Wlh dauriya kawai nake dan har yanzu da zazzabi a jikina kaina kamar ya rabe biyu. Tafiyar awani ya kawoni garin katsina bai zame dani ko Ina ba sai gidan yayana Koda na Shiga kudin Mai motar kawai na karba na bashi na baje a kasan kafet din palon wani sabon zazzabin
Chapter 12 · 0% Book details