← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 71

Sashe 37

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gujewa Luba bai hango yanda zai iya auren ta ba. A lokacin daya isa gida haka ya tarar da Aisha da kumburarren ido,da gani taci kuka ta gode Allah tunda suka gano halin da muhasim ke ciki ta ke cikin wanan halin bai iya Mata magana ba ya zub'e akan kujera ya dafe kansa dake Sara masa Yana bakin cikin ganin Aisha a cikin Wanan damuwar. Muryar ta ya katse masa tunanin da ya tafi "Abban Ashraf wlh na kasa daina kukan tausayin muhasim duk Wanda yake da saka hannu a cikin wanan halin da muhasim take ciki Allah ya Hana shi Jin dadin duniya da lahira ga fyade ga ciki ga karkakata Kai wanan wane irin zalunci ne har na koma ga Allah Ina tsinewa Wanda ya mata wanan aika aika" "Ya isa haka Aisha duk abinda ya samu bawa mai kyau ko akasin haka daga Allah ne ya Kamata ki yarda abinda ya sameta a rubuce yake sai ya sameta Yana cikin kaddararta Allah ya bata ikon cinye wanan jarrabawa addua zamu dage mata dashi Allah ya kawo mata karshen wahalar nan bai dace ki matsawa kanki da irin wanan damuwar ba idan kina haka Mai Yaya mustapha da Aunty mamy zasu ce ai sai ki Kara daga musu hankali ke fa ya Kamata kiringa rarrashin su" "Tausayin yayana nake ji kaga yanda ya koma sabida tashin hankali Ina tsoron zuciyarsa ta buga Allah ya isa tsakaninmu da Wanda ya mata haka Allah ya tona masa asiri" "Ya isa haka Aisha ki tashi ki d'auko min abincina ki sausauta wa kanki damuwar nan kafin ki kamu da ciwon zuciya" Aisha mik'ewa tayi ta nufi kitchen tana share hawayen dake zubo Mata Salis kuwa ya hau sallati kasa kasa a zuciyarsa hankalinsa na balain tashi idan yaji Aisha na irin wanan tsinuwar yasan bashida hannu a karkata mata baki amma yasan shi ya mata fyade ta samu cikin ko da ta kawo abincin bai wani iya ci ba dan ya aiketa ne sabida ya kau da maganar. A ranar ko runtsawa bai yi ba Yana ta tunanin yanda zai kaucewa auren Luba da yake ganin bazai iya ba da wane ido zai kalli Aisha yace zai auri Luba taya ma hakan zai yu wane irin kallo mutane zasu masa Luba ta zame masa kaddara da ace yasan Luba zata zame masa balai haka da tun farkon auren sa da Aisha ya rabasu. Tashin hankalin da yake ciki a yanzu sai ya nin ka na baya dan gefe ga Luba gefe gefe daya ga Aisha da yayanta da ya zama silar jefa su a cikin tashin hankali ba abinda ya Kara karya Masa zuciya sama da kukan da yaga Yaya mustapha nayi da hawaye mutum ne shi mai kib'a sai gashi duk ya zub'e sabida tashin hankalin da yake ciki,taya zai so su tab'a sanin shi yayi wa muhasim fyade har ta samu ciki,cikin da kullum yake Addu'a Allah ya kawo sanadin da zai zub'e idan babu rabon ya zub'e Allah yasa abinda muhasim din zata Haifa yazo ba Rai. Sosai ya saki bakin Aljihu yake hidimanta musu duk wani magani ko test shi yake d'aukar nauyin su. Luba kuwa tamkar har ya aureta sabida hidimar da yake yi da ita,kullum a cikin tambayarsa kudi take,ta k'arfin tuwo tasa ya ringa zuwa zance wajenta ya mugun tsanarta amma haka ya daure sabida rufin asirinsa. Abinda ke Kara bashi mamaki da shu'umancin ta yanda take ziryar asibiti har da dan hidimarta,Yana ji yanda Su Aisha da Yan uwanta ke yabon ta. Aisha har wani Kara bashi labarin irin damuwar da luba tayi da larurar da ya samu muhasim take baya iya ce mata komai dan Luba ta daina bashi mamaki yanda ta siye zuciyar Aisha da zai fito yace mata tace tana Sansa karyatawa zata yi. Da Aisha zata nutsu ma ta kalleshi zata san shi ma ba'a hayyacinsa yake ba ko d'akin da aka kwantar da muhasim baya san Shiga dan gani take zata iya bud'e baki ta tona masa asiri. A Haka har aka sallamesu daga asibiti akan larurarta shafan Aljannu ne,Inda ya dan samu kwanciyar hankali katsina akayi da Muhasim sabida Kar kowa yasan cikin dake jikinta,haka Aisha ta ringa zarya daga bauchi zuwa katsina. Lokacin haihuwar Muhasim na karatowa Yana addu'ar Allah yasa abinda zata Haifa Kar yazo da rai A ranar da aka sanar musu anyi mata aiki an cire mata 'ya mace hankalinsa sai da ya kara tashi dan a yanzu gani yake kamar za'a gane yarinyar yarsa ce sai dai cikin ikon Allah bata d'auko kamaninsa ba, a lokacin da Yaya mustapha yace zaa Kai yarinyar gidan marayu ba karamin Dadi yaji ba hakane yasa daya shawarce shi ya bashi goyon bayan a kaita gidan marayun tunda ba'a san waye mahaifinta ba sai dai kwana biyu da dawowarsa sai ga Aisha ta taho da jaririyar wai zata rik'e ta har ga Allah ba haka yaso ba so yayi ya nesanta kansa da jaririyar amma gudun Aisha ta dago shi yasa ya hakura ta hada Nana da Ummi ta ringa shayar dasu,abinda ke dan bashi mamaki bai wuce yanda Aisha ke matukar kaunar Nana ba tamkar tasan nana jininsa ce. Taya zai so Aisha tasan shine mahaifin Nana bazai so ta tab'a sani ba zai auri Luba a matsayin kaddararsa gwara taji labarin aurensa da Luba da taji labarin shine mahaifin Nana. Luba kuwa Kamar mai jiran muhasim ta haihu ta sako shi a gaba akan ya tura gidansu a daura musu aure Kuma ita ba anan take so ta zauna ba Abuja take so ta zauna ta hau gindaya Mai sharruda. Dak'yar ya samu ya shawo kanta akan ta bari a Kara kwana biyu kafin suyi maganar Aure baya so suyi gaggawa ya riga da yace zai aureta ba fasawa zai yi ba. A takaice da kyar ta yarda aka kara wata takwas a wanan lokacin yafi kowane lokaci shiga tashin hankali gani yake Aisha idan taji labarin auren nan zata iya rabuwa dashi,gashi Luba ta dage akan ita bata San munafirci tafiso a fadawa Aisha. Da kudi mai yawa ya samu Kan Luba ta yarda akan zai aureta a b'oye idan an samu shekaru zai fito ya fadawa Aisha a yanzu bazai so Aisha ta sani ba tunda dama Yana aiki a Abuja zai ajiye Luba a Abujan kawai yasan Aisha bazata tab'a sani ba. Dak'yar Luba ta yarda har aka daura musu aure bazai iya lissafa kudin da ya kashe mata a hada lefe ba duk wani Kaya da tasan Aisha na da shi sai da ta saka shi ya siya mata irinsa ban da kudaden da take ta karba a hannunsa. Sosai yake taka tsantsan baya so Aisha ta tab'a gano shi hakane yasa ya mata karyar ayyuka sun masa yawa a can. Luba kuwa ko da ta tare baya iya kwanciya da ita sabida baya Jin kaunarta yasan yayi tsalle tsalle a baya,ba Kuma dan Yana kaunarsu ba Luba ce yake Jin bazai iya kwanciya da ita ba. Karyar rashin lafiya ya ringa shirga Mata ganin an tafi sati daya yasa ta haukace Masa akan sai ya kwanta da ita raina mata hankali yake yi ba abinda yake damunsa ita fa auren da suka yi so take ya gwada Mata soyayya yanda yake gwadawa Aisha idan ba haka ba tona masa asiri zata yi. Abu kadan sai tace zata tona masa asiri sai da ya tilasta wa kansa kwanciya da ita a haka ma sai ya dirkakawa kansa magani yake iya kwanciya da ita,a cikin wata daya har makota sun san ta,da shishigi ta ringa zaryar office dinsa na Abuja har sai da duk abokanansa suka san matarsa ce da makirci take yawan hana shi zuwa bauchi gangar jikinsa ne kawai a Abuja Amma zuciyarsa na wajen Aisha,tunda ya auri luba zuciyarsa kullum cike take da fargaba akan kowane lokaci Aisha zata iya ganowa ya auri Luba a b'oye,hakane yasa yake ta iya k'ok'arinsa wajen ganin ya hana Aisha muamalla da Luba,sai dai ya lura Luba burinta kawai taga ta tona kowa yasan ya aureta. A Haka har Luba ta munafirce shi da ta haihu ta gayyato Aisha batare da yasani ba,Aisha bata cancanci haka daga wajensa ba yasan ko me zai ce mata bazata tab'a yarda ba'a san ransa ya auri Luba ba idan yace zai mata bayani hakan na nufin tonuwar asirin sa da yasa Yama auri luban. A Haka ya samu mahaifiyar sa ta shawo Kan Aishan da tunda daga lokacin da ta gano ya auri Luba ta goge shi a zuciyarsa yayi bankwana da wani farin ciki da Jin dadi kaddara ta Kara shigo Masa da Hindatu rayuwarsa ya aureta shekara da shekaru yana yiwa Luba biyayya sabida kar ta tona Masa asiri shekara da shekaru yana kashewa Luba kudi,shekara da shekaru yana fama da zullumi da fargaban Luba na iya tona Masa asiri a kowane lokaci sai gashi a yau Luba ta tarwatsa masa gida ta hanyar tona Masa asiri agaban Aisha da yayansa,a gaban Aneesa da bata san ma Yana da boyayyen sirri ba. Present "Abba Abba" Yaji muryar Ashraf akan sa Bud'e idonsa yayi a hankali ya sauke akan Ashraf daya tsugunna a gabansa shima kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake. Sai da ya hadiye yawu yace "Abba ka koma cikin daki ka kwanta bana so su ummi suga halin da kake ciki yanzu zan bi bayan Hajiya umma bazan bari ta karasa gidan ba" Da sauri ya ruko hannun Ashraf Yana "Kayi sauri kaje Ashraf karka bari ta fadawa yayanta dan Allah ka shawo kanta mu rufe sirrin nan idan har maganar nan ta fita mutuncin ku Kuma zai zub'e" "Abba kayi hakuri da tambayar da zan Kara ma Dan Allah kana da sa hannu a karkacewar wuyan Aunty muhasim" "Ashraf wlh wlh banida sa hannu a abinda ya same ta da Ina da sa hannu tunda asirina ya Riga da ya tonu Zan fada ma gaskiya amma wlh banida sa hannu a abinda ya same ta nine dai mahaifin Nana " Ashraf gyada kansa yayi Yana "Bari na bi bayanta Abba" Yayi hanyar waje Salis ya mik'e jiri na dibansa yayi hanyar dakin Aneesa tamkar karamin yaro haka ya zube
Chapter 37 · 0% Book details