Sashe 8
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga hotel din , bodyguards na biye da bayansa duk inda ya wuce sai mutane sun juya su na kallon shi dan ba karamin burge su ya yi shi kuwa ko ta kansu bai bi ba , ya nufi hanyar room din sa da ke bangaran VIP , musaman bangaran VIP da ke a floor na farko duk ya biya kudin yadda ba wanda zai iya shigowa wajen dan ya takura mishi shi dama ba mutum ne da ba ya son hayaniya , shi ya sa ya ke rayuwarsa shi kadai a haka bodyguards din sa na biye da bayansa har ya su ka karaso wajen room din sa , ya shiga su kuma su ka tsaya da ga waje ko da ya shiga , ya ajiye wayarsa saman gadon , ya sa hannu ya fara cire button din rigarsa , har sai da ya kammala ya cire ta ya ajiye saman gadon sannan ya zauna bakin gadon ya cire sneakers din sa ya rabe su gefe , kafin ya mike tsaye ya sa hannu ya zame belt din trouser din shi har ya riko trouser din sa zai yin kassa da shi ya ga an turo kofar dakin an shigo a na sallama irin wannan matan ne ma su kula da dakuna, ni dai gaskiya ban san me a ke kiran su da shi ba wlh a to ta na rike da wani tray da towel farare kal a sama , sai tsintsiya a hannunta za ta share wajen ta na shigowa idanunta su ka sauka saman shi wata irin muguwar bugawa zuciyarta ta yi ba ta san lokacin da ta saki tray din ba da kara a tare a dubu dari ya meda trouser din sa ya na fadin " Are you mad ? Get out ! ! ! " ya fada da karfi har wani runtse ido ya ke dan ba karamin haushi ta ba shi ba , at least da sai ta yi mishi knocking , da yanzu ya kai ga cire trouser din shikenan ta gama sanin sirrinsa ko motsi ba ta yi ba da wajen ta sulale a kassa sumamiya ya na ganin haka ya ja wani dan karamin tsaki ya juya ya nufi toilet taku daya ya yi ya tsaya cak , ya na zaro idanu lokaci guda ya juyo ya na zuba mata ido cikin rudu , ya kassa ganewa , ya a ka yi yarinyar da ya bari yanzu a kasuwa har ta riga shi zuwa hotel , Hotel din ma ba karamin Hotel ba a ce kuma server ce , to me ta ke yi a kasuwa cikin tsohin kayan cen ? abun ya tsaya mishi a kai wani dogon tsaki ya ja kafin ya kai hannu ya dauki wayarsa ya fara latsawa na dan lokaci kafin ya tilla ta saman gadon ya juya ya shige toilet ya medo kofar ya na shiga ko wani bodyguard ya shigo , ya na sallama kai tsaye yarinyar nan ya nufa ya sa hannayansa biyu ya dauke ta ya saba a kafada ya fice After one hour ya fito da ga cikin toilet din ya na Sanye da bathrobe white color , gashin kansa na jike da ruwa duk ya bazun mishi a saman shoulder hanyar dressing room ya nufa ya shiga jim kadan ya fito sanye da wasu Tracksuit ash color , babu takalmi a kafafunsa , ya daure wanan smooth hair din sa a baya sai tashin qamshi ya ke kai tsaye bed din ya nufa ya na shirin zama dai-dai lokacin da wayarsa ta fara ringing sai da ya zauna sannan ya kai hannu ya dauki wayar , ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na sallama cen kassan makoshi a daya bangaran Muryar wani saurayin na jiyo ya na amsa mishi sallamar cikin nitsuwa ya daura da cewa " Prince , How are you ? " a takaice Prince ya ce mishi " fine , ya ka ke ? ya jikin uncle ? " " jiki da sauki , har ma mun medo shi gida , yanzu dai fada min yaushe za ka zo ? uncle ya ce gobe su na kan hanya " wani dogon nunfashi ya ja ya na saukewa a hankali kafin ya ce " i think nan da one week , tukunna ba mu samu mun yi meeting din ba , may be Friday na dawo " ya ke fada cike da nitsuwa kai ka ce an yi mishi dole ya yi maganar " okay , zan tafi ka kula min da kanka " " in sha Allah , ka gaishe min da uncle , da Ammie " " okay " ya fada a takaice kafin ya katse kiran Prince na jin ya katse kiran ya sauko wayar a hankali kai tsaye ya ajiye saman bedside drawer , ya dauki laptop din sa da ke sama ya medo saman cinyoyinsa ya bude ya na bude ta ko ta kunnu , sai saman pic din Inaya da Malik ya na rungume da ita sai murmushi su ke saki a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya kai yatsunsa biyu saitin bakinsa kamar ya manna kiss saman ya sauko yatsun ya daura saman pic din cikin sanyin murya ya ce " i really miss my pleasures , in sha Allah next week zan dawo , na san kuma ku na kewa ta sosai ,,,,,,,,,,,,,,, but ba laifina ne ba , aikin da na zaba ne ba ya bari na zauna tare da ku amma in sha Allah komai ya kusa kammala " ya na gama fadar haka ya shiga latsa laptop din sa U.S.A ( WASHINGTON DC ) MALIK konce ya ke tsakiyar gadon su , da ga shi sai short da singlet , ya bubude hannayansa ya zubawa ceiling ido babu ko kiftawa ya na a haka Inaya ta fito da ga cikin toilet ta na sanye da bathrobe sai wani dan karamin towel a hannunta ta na goge gashinta idanunta na sauka saman shi ta san ya na cikin damuwa ajiye towel din hannunta ta yi saman dressing mirror sannan ta tako a hankali ta zauna bakin gadon ta zuba mishi ido a haka har su ka yi mintina amma sam bai motsa ba kamar ba ya nan cikin sanyin murya ta ce mishi " Baby , tunanin me ka ke yi haka ? " wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lumshe idanunsa slowly ya bude su , sannan ya juyo ya kalle ta na dan lokaci kafin ya saki wani cool murmushi ya na fadin " Nothing my Cutie " tsuke fuska ta yi ta na matse gera ta ce " ka san ba abun da za ka iya boye min ko ? fada min me ke damun ka ? " " na sani amma na ce miki ba komai My Cutie , kar ki matsa please " turo mishi dan bakin nan nata ta yi ta na marairaice fuska kamar za ta yi kuka wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " shikenan , kar ki min kuka " cike da shagwaba ta ce " to fada min me ke damun ka ? " a hankali ya juya ya na kallon ceiling ya ce " ba komai , kawai ina tunanin halin da Diya ke ciki ne , har ya yi paralyze a kassa samun wanda zai kira na ya fada min , Cutie i think ban yanke shawara mai kyau ba dawowar mu US baki daya , ko ba komai da na tsaya ina taimaka mishi , in wani abu ya same shi gaskiya ba zan iya jurewa ba , shi kadai ya yi min saura a duniyar nan " ya fada murya a dan raunace ajiyar zuciya ta sauke kafin ta riko hannunsa cikin nata , ta matse cikin sigar rarrashi ta ke fadin " baby , duk shawarwarin da yanke duk ma su kyau ne , kawai ka yi abun da zuciyarka ke fada maka ya dace ne " " No Cutie , da yanzu a ce shekarun baya ban sauka da ga kan kujerar Malik ba da Aymane ba zai taba hawan ta ba har ya yi abun da ya yi , a ce lokacin da mu ka samu cikin Twins ban matsa miki a zubar da shi ba na San da yanzu shi ma Nayab ya na tare da mu , ina sane da illar da stress ke haifarwa mace mai karamin ciki amma na yi ta jefa ki cikin damuwa , har ya yi sanadiyar Nayab tun kafin ya shigo duniya , da a ce ban nada Diya ba a madadi na da yanzu bai k.......... " ba ta bari ya kai karshen maganarsa ba ta daura hannu saman bakinsa ta katse shi cikin sanyin murya ta ce " ya isa haka baby please , ya isa , ka daina tuna abun da ya wuce , duk abun da ya faru kaddara ce , Allah ya riga da ya rubuta mana hakan , kuma in sha Allah ba abun da zai samu Diya , dan haka ka kontar da hankalinka please " ta karashe maganar ta na marairaice mishi fuska bai ce mata komai ba ya fiddo tongue din sa ya fara yi mata tafiyar tsutsa a tafin hannunta wata yar karamar dariya ta yi kafin ta janye hannunta ta na fadin " ya isa haka , yanzu konta ka yi barci ba ka ga dare ya yi " ta fada ta na kokarin sauka da ga saman gadon da sauri ya riko hannunta ya na fadin " ke kuma ina za ki je ? " " kaya zan je na saka " a hankali ya janyo ta jikinsa kafin ya dago kai ya kawo fuskarsa dab da face din ta , cikin rada ya ce mata " yau ki ka saba kwana da bathrobe ? zo ki konta kawai " murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta haye saman jikinsa , ta na faman turo dan bakin nan nata kamar ya yi mata dole hannunsa ya kai cikin jelar gashinta ya fara yi mata wassa da shi ya na fadin " kin san wani abu ? gaskiya zan so