← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 61

Sashe 7

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

THE BIGINING ( IN DAI KIN SAN BA KI KARANTA EXILED PRINCE BA , BOOKS 1 , 2 , 3 & 4 , TO KAR MA YI KI YI KOKARIN KARANTAWA DAN BA ZA NI GANE KOMAI BA WANNAN KARAN NA ZO MUKU DA SABON SALON SOYAYYA KAMAR KULLUM BA ZAN CIKA KU DA SURUTU BA , SAI MUN SHIGA CIKIN LABARIN ZA KU GANE , WANNAN KARAN ZAI TASHI KWAKWOLWAR KU KAMAR BOMB TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ [ PAGE___ 3 da kallo ya rakata har sai da ta gama saukar stair din sannan ya juya ya koma cikin dakin dan ya rarrashi dayan babynsa ko da ya shigo ya tardo ta zaune ta yi zaman bokaye tsakiyar gadon , ta hura hanci murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya meda kofar ya rufe ya saka mata security , sannan ya juyo ya nufe ta , kai tsaye saman gadon ya haye ya sa hannu ya kontar da ita ya haye saman ta , ya yi mata runfa da fafadar kirjinsa har ta bude baki ta na shirin ce mishi ya sauka da ga saman ta kawai ya cabko lips din ta ya fara kissing din ta cikin konciyar hankali da farko ta fara kokarin ture shi wai ita fushi ta ke , amma sannu sannu har ta daina , jikinta ya yi sanyi ta fara biye mishi su na kissing din juna i'm happy to see at least abu guda bai sauya ba , a to ni bari na tafi wani bangaran na duniya daban kafin su gama ) MASARAUTAR YEMEN A takaice Masarautar Yemen ta na daya da ga cikin masarautun da ke karkashin jagorancin Daular Saudiya , amma kamar kowace masarautar ita ma wannan da nata Sarkin sai dai sunan ya banbanta dan a nan Al-Sayid a ke kiran Sarkin , Al-Sayid Abdoul-Mueed Bin Ahmed shi ne sarkin wannan masarautar , da matansa biyu Sayida Ahlame ta farko , sai Sayida Fadwah ta biyu , masarautar Yemen babbar masarautar ce dan duk cikin masarautun da ke karkashin Daular Saudiya ita ta fi habbaka , duk wani Gold da a ku samu da ga kudancin Saudiya duk da ga masarautar Yemen ya fito , bangaran economy kuwa ba a magana yadda yanayin fadar Daular Saudiya ya ke haka nata ya ke , a nan ma Sarkin shi ne president din kassar , a takaice dai dan karamin labari a kan masarautar Yemen , duk da ba za mu shiga cikin labarinta sosai ba wata kyakyawar budurwa ce ke gudu tsakiyar ka suwar masarautar , ta na sanye da wata gown off-white , ta zallar auduga kai da ga gani sakar hannu ce , gown din ba ta da wani ado , wuya da hannu kawai a ka fidda , ko wani dan zane ba ta da , ga rigar kuma duk ta jiqe da ga kassa kamar ta shiga ruwa ga shi ko takalmi babu a kananan kafafunta , ta na yafe da wani dan karamin veil fari , amma Jelar gashinta duk ta na waje , ta bazun mata a shoulder har saman face , brown color da ita ta yi wani curly da ga kassa gwanin burgewa yarinyar kyakyawa ce ajin farko , a shekaru ba za ta wuce 18 years ba , fara kal da ita kamar ka taba jini ya fito , ta na da sexy eyes farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma brown ce mai mugun kyau , in ka kare mishi kallo ya so ya dan yi kama da Hazel , ta na dan karamin hanci kamar an ajiye shi tsakiyar fuskarta , da dan karamin bakinta , da wasu lalawsan lips din ta pink color , ba dan kayan da ke jikinta ba da sai na ce d'iyar wani babban dan kasuwa ne a cikin masarautar ko kuma wani na cikin fadar masarautar ta na gudu ta na waigawa bayanta , ta na rike da wata leda a hannunta , ta na juyawa ta ga wasu samari biyu su na biye da ita su na fadin " ku taro ta barauniya ce ! ki tsaya na ce ! " su ke fada da karfi sarai ta ke ji amma ta ki tsayawa haka ma mutanan wajen su na ji amma su ka share dan kowa aikin gabansa ya ke , wasu in su ka ga sun iso wajen su matsawa ma su ke su ba ta hanya ta na a haka kawai ta ji ta bugi mutum da karfi har sai da ta saki wata yar karamar kara ta saki ledar hannunta , nan take apples din da ke ciki su ka zube a kassa fuuuu ta yi baya za ta fadi cikin zafin nama ya kai hannu ya riko kugunta ya taro ta dan ya san in ta yi irin wannan faduwar ba karamin ciwo za ta ji ba har kanta ya fashe wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke jin ba ta kai kassa ba , a hankali ta ware idanunta ba su sauka ko ina ba sai cikin sexy Hazel eyes din sa nan take idanunsu su ka sarkafe cikin na juna , su ka kassa janye su su na a haka har wadanan samarin biyu su ka iso wajen su na fadin " mun gode sir , tun dazu mu ke neman kamo ta amma yarinyar nan ta gudu " ta na jin Muryarsa ta yi sauri ta dago da ga jikinsa ta boye a bayansa shi dai ya na tsaye waje guda ko motsi bai yi ba ya na sanye da trouser blue da wata Shirt white color mai dogayen hannu , da wasu tsadadun fararen sneakers a kafafunsa gaskiya hadada ne , fari kal da shi kai ka na gani ka san balarabe ne , a shekaru zai kai 30 haka , amma ya na da murdaden jiki kamar dan dambe , ga kuma fafadan kirji kai da ga gani wannan ya yi wa mutum kyakyawan naushi sai dai wani ba shi ba kallo daya za ka yi mishi ka san Jinin Malik Nawfel Hicham Bin Jaabar ne dan su na kama tak kamar an tsaga kara , har wadanan hazel eyes din nasa , da darck smooth hair din sa , shi ma ya daure shi a baya ya saki kanana a gaban gashi fuskarsa a daure tamau kai ka ce an aiko masa da sakon mutuwa a hankali ya kai hannu bayansa ya riko nata hannun ya janyo ta ya mikawa samarin nan ita da sauri ta kwace hannunta ta na fadin " no , ku duba wlh na ajiye muku kudin apples din , ku duba saman table din " wani dan karamin tsaki guda cikin su ya fa ya riko hannunta ya fisgota da karfi ya na fadin " mu je fadar Al-Sayid , sai ki fada mishi hakan barauniya kawai " dan zaro idanu ta yi ta na girgiza mishi kai kamar za ta yi kuka ta ce " a'a don Allah kar ku kai ni wajen sa , zan sake biyan kudin don Allah kar ku kai ni " ta na gama rufe bakinta ya tako a hankali ya riko hannunta , ya riko na saurayin ya raba su cike da nitsuwa ya ce " ku kyale ta ni zan biya , nawa ne kudin ? " ba musu saurayin ya fada mishi kudin sai dai ku yi hakuri ni ban san minene kudin masarautar Yemen ba gaskiya hannu ya kai cikin aljihunsa , ya fiddo bandir din Dollars sabi kal , ya na fadin " sai dai ku yi hakuri , Dollars ne kawai a hannuna " ya fada ya na raba kudin biyu ya ba su rabin ya meda rabin cikin aljihunsa a tare samarin nan su ka saki murmushi sun ga kudi , da sauri ya kai hannu ya karba ya na yi mishi godiya , kafin su juya su bar wajen kudin da ya ba su ya yi 100 din kudin Apples din ma ba 10 ba shi ya sa su ka karba su ka bar wajen ya na ganin sun bar wajen ya juyo da Niyyar yi mata magana kawai ya ga babu ita ba mai kama da ita har apples din duk babu komai duk ta kwashe ta bar wajen a rude ya fara bin wajen da kallo , ace just one minute ya ba ta baya a ce har ta gudu , tukunna wacece ma yarinyar nan ya na a haka na ga wani mutum cikin black suit ya karaso wajen , cikin girmamawa ya ce " Sir , motar ta iso " wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya fara takawa , da sauri ya bi bayansa da alamun bodyguard din sa ne a haka su ka ci gaba da takawa har su ka iso wajen fita kasuwar kawai sai ganin na yi ya tsaya cak waje guda , kafin ya juya a hankali ya kalli saitin damar sa nan ya gan ta zaune cikin wani kwango , da wasu yara uku biyu maza daya Mace , su na zagaye da ita , kowane rike a apple guda sai dariya su ke yi su na ci , ita ma ta na dariya ta na kallon su har fararen hakwaren ta na fitowa ya dan dauki lokaci ya na kallon su kafin ya juya ya ci gaba da tafiyarsa sai da su ka fito har kasuwar wajen titi nan na ga wasu manyan motoci guda uku a jere , duk farare kal ma su bala'in kyau , ga wasu bodyguards zagaye da motocin su na ganin shi daya da ga cikin su ya yi saurin bude gidan bayan motar tsakiya ko sannu bai ce musu ba ya shiga motar nan da sauri bodyguard din ya rufe motar su ka shiga sauran motocin , da mugun gudu su ka bar wajen SHEBA HOTEL Kai tsaye makeken Sheba Hotel su ka nufa , a parking space su ka tsayar da motocin da sauri Bodyguards din nan su ka sauko su ka bude mishi kofar motar cike da kwarjini ya sauko da ga cikin motar ya na latsa wayarsa , ya nufi hall din
Chapter 7 · 0% Book details