← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 61

Sashe 12

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

THE BIGINING ( TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ [ PAGE ___ 5 ya na fitowa parlourn ya tardo Inaya da Nesrine rungume da juna a hankali ya karaso wajen ya na fadin " Cutie , mu tafi zuwa anjima sai mu dawo " a hankali ta raba jikinta da na Nesrine , cikin sanyin murya ta ce mata " je ki kula da shi , zuwa anjima na dawo " gyada mata kai kawai Nesrine ta yi kafin ta juya ta nufi corridor ta shiga Inaya kuma ta bi bayan Malik dan tun lokacin da ya yi maganar ya fice ta na fitowa ta hango shi ya na takawa a hankali ya nufi part din MALIKAT INAS da sauri ta kamo shi ta riko hannunsa , ta na fadin " shi ne za ka taho ka bar ni ? " " ba na son takura miki ne shi ya sa " ya fada ba tare da ya kalle ta ba murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta kontar da kanta saman shoulder din sa su ka ci gaba da tafiyarsu a haka duk inda ya wuce sai dogarai sun gaishe su cikin girmamawa , wasu har rako su su ke yi dan ba karya su na jin dadin ganin Malik cikin masarautar kowace shekara wani abu da ban fadi ba , bayan mutanan da ke cikin Daular Saudiya , duk mutanan masarautar ba wanda ya san Diya ne a kan kujerar Malik , kowa a tunaninsa Malik ne , dan duk lokacin da za su yin wani taro inda a ke bukatar Malik da Rawani Diya ya ke tafiya , kuma wani lokacin ya na sanye da medical glass shi ya sa su ka kassa gane shi da sallama a bakinsu su ka shigo parlourn MALIKAT INAS su na zaune ita da RIANNA , cen na hango wani dan karamin yaro da ba zai wuce 8 years ba , ya na zaune gefen RIANNA da tray din fruits a gabansa cikin nitsuwa shi kuma ya karaso cikin parlourn ya na kallon yaron dan shi a iya sanin sa RIANNA ba ta taba haihuwa ba to wanene wannan yaron ? da sauri ita ma RIANNA ta mike ta nufi Malik ta rungume shi ta na fadin " na yi kewar ka sosai Akhie " " ni ma na yi kewar ki over " ya fada ya na rungume ta shi ma , a haka har MALIKAT INAS ta mike ta rungume su a haka sai da su ka gaji sannan su ka raba jiki MALIKAT INAS na ce wa Malik ya zauna " a'a Ammie , zan wuce part di na , na gaji sosai wlh " ya fada murya a sanyaye " shikenan " Fadin MALIKAT INAS a takaice kafin ta juya ta na kallon Inaya da ke tsaye ta zuba wa yaron ido wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " to ba za ki gaishe ni ba ? wai tsaya ma , ina ku ka baro min Twins di na ? " Malik ne amsa mata da cewa " Princess ta na US , exams gare ta shi ya sa ba ta biyo mu ba , amma in ta kammala za ta taho , Prince kuma......... ni kaina ban san inda ya ke ba " a tare MALIKAT INAS da RIANNA su ka zaro idanu , har su na hada baki su na cewa " kamar ya ba ka san inda ya ke ba ? " " Ammie , Aunty RIANNA , Prince fa ba baby ne ba , ya na da hankalin kansa , kuma na san duk in da ya ke ya na cikin koshin lafiya " Fadin Inaya da ke tsaye a bayansu cikin rudu MALIKAT INAS ke cewa " ni fa ban gane me ku ke nufi ba , ina Prince di na ya yi ? " " Ammie na fada miki , ni kaina ban san in da ya ke ba , wajen three months rabon da na saka shi a idona , ni ko waya ma ba mu yi , Sai dai ya turo mana letter ya ce wai ya na cikin koshin lafiya , yanzu dai zan tafi , Cutie let's go " ya fada ya na mikawa Inaya Hannu ta na tsaye ta zubawa yaron nan ido babu ko kiftawa , shi kuwa sai sunkuyar da kai ya ke ya na ja da baya a hankali ta dago kai ta kalli MALIKAT INAS ta ce " Ammie , wanene wannan yaron ? " wani kyawatacen murmushi RIANNA ta saki kafin ta koma ta riko hannunsa , ta mikar da shi tsaye ta na fadin " sunansa Faaz , last month ne security su ka kama shi cikin kitchen din Daular , ya na satar abinci , za su hukunta shi ne na iso wajen , na ce su kyale shi yaro ne , kuma yunwa ya ke ji , da ga nan na sa a ka ba shi abinci , bayan ya ci na ke tambayar shi ina ne gidan su a mayar da shi , ban ya ke ce min wai da ga gidan marayu ya gudo , kuma ba zai koma ba saboda ba su da kirki wai ko abinci ba su ba shi , kullum su na tsangwamar shi , shi ne kawai na ce ya zauna tare da ni , Faaz , wannan Auntynka ce , kanwata ce , ina fatan za ka girmama ta kamar yadda ka ke min ? " gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya matso a hankali ya mikawa Inaya hannu ya na fadin " ni sunana Faaz , za ki zama abokiyata ? " kallon hannunsa ta yi kafin ta dago nata a hankali za ta riko nashi su gaisa ko one seconde ba ta yi ba ta janye hannunta da sauri cikin rudu Faaz ya ce " Aunty lafiya ? me ya faru ? ba ki son zama abokiyata ? " ya fada ya na marairaice fuska kamar zai yi kuka da sauri RIANNA ta riko shi ta na fadin " no ba haka ba ne , na san ta gaji ne ta na son ta je ta huta , baby ya kamata ku je ku huta , zuwa yamma mun yi magana " ba musu Inaya ta gyada mata kai kafin ta tako a hankali ta riko hannun Malik da ke tsaye tun dazu ya zuba mata ido da ga haka su ka yi wa MALIKAT INAS sallama su ka fice part din su na tsaka da tafiyarsu Malik ya ce mata " me ya faru na ji jikinki ya yi sanyi ? " ya fada dan ya lura tun lokacin da Faaz ya ba ta hannu su gaisa jikinta ya yi sanyi wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " ba komai kawai na gaji ne " " na dauka yunwa ki ke ji ....... " cikin nitsuwa ta katse shi da cewa " in yunwa na ke ji za ka shirya min abinci ? dan gaskiya ina dan jin yunwa " ta qarashe maganar ta na dan marairaice mishi fuska sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " no , amma zan ba ki madara ki sha , ko ba ki so ? " wata yar karamar dariya ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba a haka har su ka karaso building din sa wanda marigayi Malik Hicham ya gina mishi da ya ke dama MALIKAT INAS na sane da zuwan su , tun lokacin da su ka yi waya ta sa a ka gyara part din , duk da ma kullum a gyare ya ke ko yanzu ma kayansu direct nan a ka yi da su ko da su ka shiga part din kai tsaye floor na hudu ya wuce da ita tun a parlour ya fara ya fara zuba mata love , har su ka isa bedroom din su nan ma sai da su ka mori juna har sai da su ka gaji sannan su ka shiga yin wanka Ni kuma na dauki takarduna na nufi Yemen dan na ga abun nan nasu ba me karewa ba ne ) MASARAUTAR YEMEN DAULAR YEMEN tafiya ya ke cikin harabar masarautar kai a sunkuye ya na duba littafin hannunsa , jiya da ya zo daukar wa Junior littafin da ya saka shi nema ya ga wani littafin da ya ja hankalinsa , shi ya sa ma ya dawo dan zai so ya karanta shi ya na sanye da wasu suit khaki , ma su bala'in kyau sun yi mugun kabar shi kuwa ya na a haka kawai ya ji ya bugi mutum har sai da book din hannunsa ya fadi wani dan karamin tsaki ya saki kafin ya dago kai , nan ya gan ta tsaye , ta na sanye da wata gown white color da Alkyaba blue da ga sama , babu ko dan kwali a kanta , gashin kanta duk ya na waje ya bazun mata saman shoulder , ta dafe forehead da hannu guda ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka " ba ki kallon gabanki ne ? " ya fada ya na tsare gida ba tare da ta bude idanunta ba ta ce " kai ma ba ka kallon gabanka ? dubi don Allah ka ji min a forehead , wlh sai na fadawa Daddy , na ce a rataye min kai " ta fada ta na kukan shagwaba dan tabe baki ya yi ya na kallon ta wai a rataye shi , to shi in ya yi niyya har Daddy nata sai ya sa a rataye shi kuma a zaune lafiya bare ita karamin aiki , da hannu guda ma zai sa sai dai wata ba ita ba sai da ya bari ta gama maganarta sannan ya ce " to Daddyn naki da kansa zai rataye ni ko kuma ke zai sa ki rataye ni ? " " you , you , you are mad , sai na c......... " ba ta karashe maganarta ba sakamakon bude idanunta da ta yi , ba su sauka ko ina ba sai cikin nasa ko , nan take
Chapter 12 · 0% Book details