← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 61

Sashe 59

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su ma taba samun yaro me sunan Faaz ba , nan Junior ya tabbatar tabbas maganarta gaskiya ne , duk da haka ba su hakura ba su ka ci gaba da binciken sauran gidan marayun Masarautar ko sun samo wani abu , sai da su ka bincike kab gidan marayun Masarautar ba su samo komai ba , sai a na karshe ne su ka samu wasu information , information din da su ka samu ya tabbatar wa da Junior Faaz tabbas turo shi a ka yi dan ya cutar da su bangaran Faaz kuwa , tun lokacin da ya je Prison wajen Izayn bai sake wani motsi ba , dan gudun kar a kama shi , musaman da Izayn ya ce kar ya sake dawowa wajensa , specially ma yanzu da ya san Aleenah ta saka mishi ido , dole ya kiyaye takunsa wajen aiwatar da aikinsa na gaba yanzu dai Familyn shiru ba abun da ke Faruwa , sai shirye shiryen tafiya Makkah da Malik da Diya su ke yi na watan azumi nan da two weeks MISALIN KARFE 9 NA DARE PRINCE zaune ya ke a parlour , da ga shi sai short , da laptop saman Thigh insa ya na aiki ya na zaune a haka Aleesherh ta shigo parlourn ta na sanye da kayan barcinta , hannunta rike da wani tray cike da fruits da snacks kai tsaye ta karaso wajensa ta zauna a kassa saman carpet , ta ajiye tray din gabanta ta fara ci a hankali ya dawo da kallonsa gare ta , sai cin fruits ta ke cikin nitsuwa bayan yanzu su ka kammala diner kamar cikinta ba ya cika janye laptop din sa ya yi ya ajiye gefe ya sauko kassa ya zauna gefenta ya kai hannu ya janye tray din ya na fadin " wai ke ba ki gajiya ? yanzu fa mu ka yi diner ? " marairaice mishi face ta yi ta na fadin " please Honey , ka ban abuna , wlh yunwa na ke ji , ji na ke kamar ban ci komai ba tun safe wlh " " dubi don Allah har kin fara yin k'iba , kullum sai ci ki ke yi , wai yaushe ki ka fara wannan uban cin ne ? ni dai a sanina ba komai ki ke sakawa a jikinki ba " " ni dai yanzu ka ban Fruits di na na sha " ta fada cikin shagwaba ta na turo dan bakinta bai ce mata komai ba ya mike tsaye ya dauki tray din ya nufi dining table ya ajiye shi sannan ya dawo wajen ta , ya sa hannayansa biyu ya dauke ta cak kamar baby ya nufi corridor da ita da sauri ta ce mishi " ni sauke ni ba in da zan je , ka sauke ni " " shut up ! yaushe ki ka koyo rigima haka wai ? wlh har kin kara nauyi " ya fada ya na shiga bedroom din shi da ita kai tsaye saman gadonsa ya kwantar da ita , sai turo dan bakinta ta ke yi kamar ya ce zai yi mata kiss ya na sauke ta ko ta yi sauri ta juya mishi baya , ta janyo duvet ta rufe jikinta har kai murmushi mai dan sauti ya yi ya na kallon ta , ya rasa ya a ka yi kwanan nan ta koyo rigima , amma ko ba komai ya na jin dadin yar rigimar nan da ta ke yi mishi specially idan dare ya yi sai ta yi zaune ta na zuba mishi shagwaba kamar baby bai ce mata komai ba ya juya ya fice bedroom din , kai tsaye parlour ya koma ya dauki laptop insa sannan ya dauki tray din fruits din ta da ya ajiye saman dining table ya koma bedroom insa ko da ya koma ya ajiye komai saman bedside drawer , ya hau saman gadon ya na fadin " tashi ki sha kayanki " shiru ta yi ko motsi ba ta yi ba a hankali ya kai hannu saman shoulder din ta ya juyo ta nan ya ga Ashe har barci ya fara yin gaba da ita , da alamun ita kanta ta gaji wani dan karamin murmushin gefen fuska ya yi kafin ya kwanta ya kashe lamps din dakin ya kunna bedside lamps , ya zagayo da hannayansa a bayanta ya rungume ta a jikinsa ya na sauke ajiyar zuciya , ya lumshe idanunsa duk da ba barcin ya ke ji ba JUNIOR zaune su ke a garden shi da Diya , yau ya na son zama da Daddynsa sun yi wajen kwana biyu ba su ga juna ba , kullum Diya ya na fada , shi kuma ya fita wajen aikinsa su na zaune su na hira har da dariya kamar wasu abokai a haka Malik ya iso wajen ya na sallama a tare su ka amsa mishi sallamarsa kafin Diya ya ce " lafiya na ga ba ka yi barci ba har yanzu " karasowa gefensa Malik ya yi ya zauna ya na fadin " ganin ku na yi ku na dariya shi ne na taho na ji hirar me a ke yi haka " har Diya ya bude baki zai yi magana Junior ya riga shi cewa " uncle dama ina son mu yi wata magana " ya fada dan ya san in har Diya ya bude baki to tabbas sai ya bar wajen dan ko zaman da su ke yi tsokanar shi ya ke wai ya lura ya yi haske kwana biyu kamar sabon ango cikin nitsuwa Malik ya ce mishi " wace magana kuma ? na ga ai Nailah ta koma part din ka ko ba haka ba ? " wani dan karamin tsaki Junior ya ja ya na kauda kai kafin ya ce " uncle ni ba wannan maganar ba , a kan Faaz ne yaron da ke wajen momy RIANNA , na ji ta ce wai ta na son ta yi adopting shi , ko ta bar maganar ? " " ta ce mu bari har ya samu sauki , ka san kwanan nan ba shi da lafiya har Asibiti ya kwanta , shi ne ta ce a bari har hankalinta ya konta sai a yi abun da ya dace " " amma uncle kun san gidan marayun da ya gudo ? " " ba ta fada min ba har yanzu " dan jinkirtawa Junior ya yi kafin ya ce " gidan marayun Ekhaa , uncle a iya sani na gidan marayun Ekhaa ko bai zo na daya ba ya zo na biyu cikin kassar Saudiya , saboda su na da tsari sosai , su na kuma kula da marayu musaman manyan mutane da ministers ke ba da gudun mawa wajen kula da yaran , na takaice maka a cikin gidan marayun akwai karamar school ta koyar da yaran da su ka kai 8 years , ku na tunanin za su bar karamin yaro kamar Faaz ya gudo da ga gidan marayun ba tare da sun saka an fara cigiyar shi ba ? wajen four months ya na tare da mu amma shiru babu ta in da na ji a na cigiyar yaron da ya gudo da ga gidan marayu " " me ka ke nufi ? ba da ga gidan marayun Ekhaa ya gudo ba ? " fadin Diya cikin nitsuwa ya ce " Daddy sai da na je gidan marayun dan na tabbatar in da ga cen ya ke amma su ka ce min duk yaransu su na nan tun last year har zuwa yanzu ba wanda ya bar gidan marayun ko da sunan adopting , hakan ya sa kawai na ci gaba da binciken sauran gidan marayu kar a je mistake ne a ka samu ba da ga gidan marayun Ekhaa ya fito ba , Daddy baki dayan gidan marayun masarautar Saudiya sai da na bincika amma ban samu abun da na ke so ba , har pic din Faaz na dinga nuna musu amma su ka ce ba su taba ganin shi ba ma , akwai wani tsohon gidan marayun da ke cen fitar masarautar , ba kowa ne ya San da shi ba asali ma yaran da ke ciki ba su wuce 10 ba , bayan na gwada musu pic din Faaz su ka ce min Eh sun taba samun yaron da ke saman pic din , amma a lokacin sunan shi Abdallah , kuma ya yi wajen two years da rasuwa " a tare Malik da Diya su ka ce " what ? rasuwa fa ka ce ? " gyada musu kai ya yi ya na fadin " Yes , ya rasu , Daddy , Uncle , Princess ta jima ta na ce min hankalinta bai kwanta da yaron nan ba , kamar ya na da wata muguwar manufa , amma na kassa yarda da ita saboda a gani na yaro ne ba abun da zai iya yi , amma yanzu ina da tabbacin akwai wani abu a kassa " ya na gama rufe bakinsa su ka jiyo Muryar Prince ya na fadin " ni kaina tun lokacin da na shigo masarautar nan na gan shi zuciyata ta kassa sakewa " a tare duk su ka juya su na kallon wajen da su ka jiyo Muryarsa dama ya jima a tsaye a nan ba su da labari , ya kassa barci ne shi ya sa ya fito , tun lokacin da Junior ya fara magana ya ke tsaye a wajen amma ba su lura da shi ba a hankali ya tako ya zauna gefen Junior , ya na kallon Malik da Diya cikin nitsuwa ya ce musu " ni kaina yaron nan bai kwanta min ba , amma momy RIANNA ta na son shi sosai , idonta ya rufe a kan shi , duk abun da za mu fada mata ba ba za ta yarda ba " " yanzu me ku ke tunani a kai ? " fadin Diya " mu fara sanin abun da ya kawo shi masarautar , abun da ya ke shirin yi , in ma cutar da mu ya ke son yi " fadin Prince " haka ne Daddy , a ka je da hannunshi
Chapter 59 · 0% Book details