Sashe 31
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na kira uncle na hada maka karya da gaskiya , kuma ka fi kowa sanin halinsa dan haka tashi ka tafi , it is just for ten minutes , ba ka san awa nawa ta share ta na shirya maka abincin nan ba , kuma ka ce ba ka zuwa , ka yi mata adalci ? " tsaki Prince ya ja kafin ya sauko da ga saman gadon ya karbi jacket din ya saka , ko sannu bai ce wa Junior ba ya sa kafa ya fice bushewa da dariya Junior ya yi kafin ya zauna wajen da ya tashi ya dauki laptop din ya ci gaba da aikinsa Prince kuwa, kai tsaye hanyar garden ya nufa tun da ya shigo ya fara hango ta zauna saman chair ta na rike da wayarta ta na latsawa , gabanta wata table shinfide da wani farin tissu , table din ta na cike da abinci , da fruits da juice wajen ya na zagaye da lamps white color ma su mugun kyau , wajen dai ya yi tsab kamar so romantic da sallama a bakinsa ya iso wajen hannayansa na cikin aljihun jacket ba tare da ta dago kai ba ta amsa mishi sallamarsa ta ce mishi " sannu da zuwa , bismillah " ta kai karshen ta na ajiye wayarta ba musu ya zauna ya zuba mata ido ba tare da ya ce komai ba " what ? bari min irin wannan kallon ni ma matsa min a ka yi na shirya maka abincin nan " " kenan ba da son kanki ki ya yi wannan abun ba ? " ya tambaye ta sai da ta dauki lokaci kafin ta ce " Eh , why zan dauki lokaci kan wanda bai damu ba ? na fada maka ? ni wlh auren nan matsa min kawai a ka yi na yi shi ba dan haka ba ni zuciyata na da wanda ta ke so " dan tabe baki ya yi kafin ya ce " do you know what's love ? " sai da ta saki murmushi sannan ta ce " no , ban san minene so ba , a kansa na san minene so , ni mutunce mai karancin yarda da mutum ko a school Aleenah ce kadai friend's di ta , amma shi , tun lokacin da idanuna su ka sauka cikin nashi na ke jin kamar na mallaka mishi rayuwata baki daya , shi ne namiji na farko da zuciyata ta amince da shi , duk abun da ya ke burge ni ya ke da ga yanayin maganarsa har zuwa Tafiyarsa komai burge ni ya ke , ni kaina ban san ya a ka yi na kamu da son shi haka ba , na yi kokarin fada mishi abun da ke cikin zuciyata amma ya nuna min ya fi karfin soyayyata " ta qarashe maganar ta na daukar plate ta fara serving din sa shi dai ya yi zaune ya zuba mata ido ya ma rasa abun da zai ce , da ga gani ta na fama da soyayya amma ko wane ? kenan shi ya sa ta ke ja da baya da shi akwai wanda ta ke so , in haka ya kamata ta yi wa Al-Sayid magana kar a aura mata wanda ba ta so sai da ta gama serving din sa ta ajiye mishi plate din gabansa sannan ta dauki wayarta ta fara latsawa bai fara cin abincin ba , ya ce mata " me ya sa ba za ki fada wa Al-Sayid ba akwai wanda ki ke so ? " " na fada mishi , ya ce min na kawo shi ya gan shi , da na je fada mishi abun da ke cikin zuciyata ya koro ni , na koma na tarda ya bar garin ma , that's why ma na hakura " https://chat.whatsapp.com/DWOwxaJuwFcGR1BPqBgf0s _______________________________________________ [ FREE PAGE ___ 13 jin abun da ta ce ya tuno mishi abun da ya faru lokacin da ta je bedroom din sa a hotel ta na ce mishi ya saurare ta amma ya ki ji , har ya kore ta a fusace , ba dai shi ta ke so ba ? ya tambayi kansa cikin nitsuwa ya ce mata " zan iya sanin ko wanene wanda ki ke so ? " wata yar karamar dariya ta yi ba tare da ta kalle shi ba ta ce " in na fada maka za ka sa ya so ni ne ? ko in na fada maka zai sauya gaskiyar da ba ya so na ? na fada maka ko kar na fada maka duk ba abun da zai anfanar " bai ce mata komai ya fiddo hannu da ga cikin aljihun jacket din sa , ya dauki spoon ya fara cin abincin ta na ganin ya fara ci ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayarta gefe , amma kafin ta ajiye sai da ta saka musu music irin slow music haka sannan ta ajiye wayar , ta yi serving kanta ita ma ta fara ci cikin nitsuwa ta yi nisa duniyar tunaninta ta dago kai a hankali ta kalle shi , nan ta ga hannunsa sai rawa ya ke da kyair ma ya ke iya rike spoon din ta na shirin magana ta ga ya saki spoon din , ya kankame kansa waje guda da sauri ta mike ta nufe shi ta na fadin " are you okay ? ba dai allergy gare ka ba ? " a rarrabe ya ce mata " no , sanyi na ke ji ? " " sanyi kuma ? to ai nan ba wani sanyi a ke yi ba , ko dai ba ka da lafiya ? " ta kai karshen ta na kai hannu saman kumatunsa nan ta ji jikinsa ya yi mugun zafi har sai da ta janye shi da sauri a rude ta ce mishi " ka san ba ka da lafiya me ya sa ka taho , ai sai ka min text ka ce ba ka da lafiya zan gane " " na san kin dauki lokaci wajen shirya wannan abun , in ban zo ba , ba za ki ji dadi ba " maganarsa ba karamin dadi ta yi mata ba cikin zuciyarta , hakan na nufin ya damu da ita ? dafa shoulder din sa ta yi ta na fadin " shikenan , tashi mu koma ciki ka konta " kassa amsa mata ya yi kawai mikewa tsaye ya yi a hankali ya na dafa table , har rawar jiki ya ke riko hannunsa ta yi ta taimaka mishi su ka koma cikin kai tsaye part din su ta meda shi , Junior na ganin su ya yi sauri ya mike ya na fadin " Prince , me ya faru ? " Aleesherh ce ta amsa mishi da cewa " sanyi ya ce ya ke ji , kuma jikinsa ya yi zafi sosai " " i'm sorry " ya fada ya na riko hannun Prince ya taimaka mishi ya konta saman gadon ya janyo duvet ya rufe shi har zuwa wuya dama shi ya tafi ya kwatantawa Aleesherh ba zai iya zuwa ba , cikin sauki sanyi ke kama shi a hankali ta karaso ta tsaya bakin gadon ta na fadin " bari na hada maka hot chocolate , za ka ji sauki da ga baya " girgiza mata kai ya yi ya na fadin " no , kar ki damu kanki , na gode " ya na gama fadar haka ya janyo duvet din ya rufe jikinsa baki daya ya konta saman shoulder cikin sanyin murya Junior ya ce mata " don't worry , nan da five minutes zai dawo dai'dai , za ki iya tafiya dare ya yi , sai da safe " a sanyaye ta ce mishi " sai da safe " da ga haka ta juya ta fice sai da ta fita sannan Prince ya fiddo kansa ya na kallon Junior ya ce " duk laifinka ne , sai ka tafi ka kawo lemon " bushewa da dariya Junior ya yi kafin ya zagayo daya gefen ya konta ya na fadin " ya a ka yi ma ku karaso nan da sauri haka , na zata sai ka zuba mata love sannan ku dawo " tsaki kawai Prince ya yi kafin ya meda kansa cikin duvet din har ya fara nadamar bin maganar Junior ya tilla ALEESHERH bayan ta baro part din su Prince kai tsaye part din su ta koma ta na sakin murmushi ita kadai ta na shigowa ta tardo Aleenah konce saman gadonsu sanye da wata yar karamar rigar barcinta pink color karasowa Aleesherh ta yi cikin dakin ta nufi toilet ta shiga ta yi wanka, Sannan ta fito ta shirya ita ma cikin irin rigar barci irin ta Aleenah amma ita white color ta karaso bakin gadon ta konta gefen yar uwarta ta na fadin " Aleen , barci ki ke ? " " No " ta fada a takaice wani dan karamin murmushi Aleesherh ta sakin mishi mata kafin ta ce " kin san wani ? yau Prince ya nuna min ya damu da ni shi ma , da ga yanzu ki ma zan nuna mishi na damu da shi ,may be da ga haka har ya fara so na " shiru Aleenah ta yi ba ta ce mata komai ba ta zuba mata ido kallon ta Aleesherh ta yi ta na fadin " lafiya ki ka yi shiru ? ko ke ma ba ki da lafiya ? , na lura kwana biyu duk yanayin ya yi sanyi " " Alee , na san ki na farinciki da wannan auren za ki auri wanda zuciyarki ke so , kuma ina farinciki da hakan sosai ma , just ina tunanin abun da zai faru in a ka yi aurenku , hakan na nufin za ki tafi ki bar ni , ban san ya zan yi ba in ba ki nan " ta kai karshen kamar za ta yi kuka nan take Aleesherh ta ji jikinta ya yi sanyi , ita duk ta manta da wannan maganar , yanzu in a ka yi auren dole ta rabu da Aleen din ta , ba ta san ma in za su sake haduwa