← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 61

Sashe 23

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

THE BIGINING TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ _ PAID BOOK N500 [ FREE PAGE ___ 9 sai da su ka dauki lokaci a haka kafin su raba jiki , Inaya ta ce mishi " tashi ka tafi wajen Daddynka , ya na part din Uncle " yamutse fuska ya yi ya na fadin " no Cutie , gaskiya a gajiye na ke zan so na tafi na yi wanka na huta " " ka na so kara wa kanka laifi , amma ba ruwana tashi ka je " ta fada mishi ba musu ya mike ya fara takawa zai fita da sauri RIANNA ta ce mishi " yanzu kenan Prince ba za ka rungume ni ba ? " ko sannu bai ce mata ba ya sa kafa ya fice parlourn sai da ya fita sannan Inaya ta ce mata " sorry Aunty RIANNA , kin san halin yaronki da mugun kishi , may be dan ya ga Faaz ne a jikinki ne ya sa ya miki fuska " kallon Faaz RIANNA ta yi ta na cewa " yanzu ka yi min adalci , ka hana ni tarbar babyna ? " cike da shagwaba ya ce mata " momy kenan ni ba babynki ba ne ? " ya fada kamar zai yi kuka wani dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " no , kai ma babyna ne , just na jima ban gan shi ba , na yi kewar sa sosai , amma ka ga saboda kai ya min fushi ko kula ni bai yi ba " " yi hakuri momy , bari na je na ba shi hakuri " ya fada ya na raba jikinsa da na RIANNA ya tashi da gudu ya fito part din ba ta yi kokarin tsayar da shi ba sai ma murmushin da ta ke yi sai da ya fita sannan Nesrine ta mike ta na fadin " Ammie zan koma part di na " gyada mata kai MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " shikenan , ki kula da mijinki , sannan ki tabbatar ya sha maganinsa " wata yar karamar dariya Nesrine ta yi ta na cewa " Ammie wlh ina fama dan kamar karamin yaro ya ke , magani ma sai na matsa mishi ya sha " " sai kin hada da hakuri " MALIKAT INAS ta fada a sanyaye murmushi kawai Nesrine ta yi mata ta fara takawa ta nufi kofar fita har ta karaso bakin kofar Faaz ya shigo da gudu ya na kuka ya dafe kumatunsa na dama da hannu kai tsaye RIANNA ya nufa ya fada jikinta cikin rudu RIANNA ta shiga tambayar shi lafiya ya na kuka cikin kukan nashi ya ce mata " momy , Uncle ne , na je na tambaye in zai zama abokina kawai , kawai sai ya mare ni , momy uncle ba shi da kirki , he is wicked " rungume shi RIANNA ta yi ta ma rasa abun da za ta dan ta rarrashe shi ba ita kadai ba har MALIKAT INAS da Inaya musaman Inaya , ta san halin yaronta ya na da zuciya kuma ba ya son takura amma abu me wuya ne ya ce zai daga hannu ya bugi mutum , bare ma dan karamin yaro kamar Faaz , gaskiya zuciyarta ta kassa yarda da Prince ya mare shi a hankali ta mike tsaye ta na fadin " Ammie ina zuwa " da sauri MALIKAT INAS ta ce mata " no , koma zauna kyale shi zai dawo ya same ni " " No Ammie ba wajen sa zan je ba , yanzu ina zuwa " ta fada ta na nufar kofar fita ta fice ta bar RIANNA da MALIKAT INAS su ka shiga rarrashin Faaz PRINCE bayan ya baro part din MALIKAT INAS kai tsaye part din Malik ya nufa dan dama cen a ka kai kayansa ko da ya isa a floor na uku ya wuce ya shiga bedroom din sa , ya sa hannu ya fara rage kayan jikinsa , sai da ya rage da ga shi sai short sannan ya nufi toilet sai da ya yi wajen one hour a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunshi , ya karaso wajen dressing mirror daukar lotion din sa ya yi ya fara shafawa , bayan ya gama ya shiga dressing room jim kadan ya fito sanye da kayan barcinsa white color ya saki wannan lalawsan gashin kansa irin na Malik , kai tsaye gadon ya nufa ya Haye ya konta rub da ciki kafafunsa ko ida Hayewa gadon ba su yi ba , a haka har barci ya yi gaba da shi INAYA bayan ta baro part din MALIKAT INAS kai tsaye part din Diya ta nufa dan ta san Malik na cen a wannan lokacin ta ko yi sa'a , su na zaune a harabar part din , har da Abdoul wani cool murmushi ta saki kafin ta karaso wajen ta na yi musu sallama a tare duk su ka amsa mata , har Abdoul ya bude baki zai yi magana wata kyakyawar budurwa ta fito da ga cikin parlourn Diya ta na sanye da wata gown pink color babu ko veil a kanta , ta saki wani golden hair din ta mai mugun laushi kai da ga gani ka san a na kashe mishi kudi ta na kama tak tak da Junior da Diya , a shekaru za ta kai 18 years haka , fara kal da ita jinin larabawa kamar ka taba jini ya fito , Azmat kenan , autar Malik Diya karasowa ta yi wajen babu ko sallama ta ce " Daddy , ka cewa Big bro ya ba ni bank card di ta , shopping na ke " dafe forehead Diya ya yi ya na fadin " Ya Salam , wai da wane zan ji ?rigimar Junior ko taki ? tafi bedroom di na ki dauki tawa bar shi wannan " daga kafa ta yi ta buga a kassa ta na fadin " No ! ni tawa na ke so , ka ce mishi ya ban abuna tun da ba shi ya ban ita ba " ta fada cike da shagwaba a hankali Inaya ta matso in da ta ke tsaye ta daura hannu saman kanta ta na fadin " Azmat , har yanzu ke ma ba ki daina wannan rigimar ba ? shikenan mu je na karbo miki " " yawwa momy mu je ki ja mishi wadanan manyan kunnuwa nashi " ta fada ta na jan hannun Inaya su ka koma parlourn tare sai da su ka bar wajen sannan Abdoul ya ce wa Diya " Diya ina ga ya kamata ka yi wa babynka aure yanzu " " ko na ce na yi mata ita da momynta ba za su yarda ba , sai da na yi mata maganar amma ta ce wai mu bari har ta kammala karatunta " haka dai su ka ci gaba da hirarsu har zuwa lokacin da su ka fara jin kiran sallat Malik da Abdoul su ka tashi su ka nufi part din su dama Inaya ta jima da tafiya Malik Kuwa a floor na uku ya tsaya ya nufi corridor ya shiga har ya wuce kofar bedroom din Prince ya tsaya ya juyo a hankali dan ya ga haske na fitowa a hankali ya shiga bedroom din ya na sallama kassa kassa nan ya ga Prince konce rub da ciki sai sharar barci ya ke gaskiya ba karamin sanyi ba ya ji cikin zuciyarsa ganin yaronsa har wani cool murmushi ya saki kafin ya tako a hankali ya zauna bakin gadon ya kai hannu saman kansa wani dogon nunfashi Prince ya ja ya na mika sannan ya ware idanunsa slowly , sai saman Malik ko su ka sauka " sannu agogo Sarkin aiki , sai yanzu a ka samu lokacin hutawa ? " Malik ya fada cikin sigar zolaya a hankali Prince ya matso ya kontar da kansa saman laps din Malik ya na fadin " Daddy , tun yaushe ka ke nan ? " " yanzu na shigo , tashi ka yi wanka mu tafi Mosque lokacin sallat ya yi " " uhm " ya fada a sanyaye kafin ya sauke kansa da ga kan laps din Malik ya sauko da kafafunsa kassa ya mike tsaye sai tangal tangal Ya ke kamar zai fadi mikewa tsaye Malik ya yi ya riko hannunsa ya na fadin " what happened ? " " nothing Daddy " ya fada ya na kai hannu saman ido ya na murza wa wani dan karamin murmushi Malik ya saki kafin ya fara jan hannunsa ya nufi toilet da shi kamar wani karamin yaro sai da su ka iso bakin kofar sannan ya saki hannunsa ya ce " shiga ka yi wanka ina zuwa " ya kai karshen ya na juyawa zai bar wajen da sauri Prince ya ce " Daddy ? " cak Malik ya tsaya ya juyo a hankali ya na daga mishi gera alamun minene kawai rungume shi Prince ya yi ya na fadin " na yi kewar ka sosai Daddyna " rungume shi tsam Malik ya yi ya na sumbatar kumatunsa , sai da su ka dan dauki lokaci a haka kafin Prince ya raba jikinsa da na Malik kawai ya juya ya shiga toilet ba tare da ya ce mishi komai ba haka shi ma Malik juyawa ya yi ya fice ya shiga bedroom din sa ya na shiga nan ma ya tardo Cutien sa , konce saman gado sai barci ta ke , bai yi kokarin tashe ta ba kawai ya shiga toilet MASARAUTAR YEMEN AL-SAYID zaune su ke cikin parlournsa tare da familynsa, Sayida Ahlame da Sayida Fadwah su na zaune saman sofa guda Aleesherh da Aleenah kuma su na zaune a kassa saman carpet sun sunkuyar da kai cikin nitsuwa Al-Sayid ya ce " abun da ya sa na kira ku nan , a kan maganar auren ku ne da na bawa Malik din Saudiya , kuma ya karba hannu bibiyu ya kuma ce in sha Allah gobe yaronsa za su zo nan masarautar in ya so Next week a yi auren , mai dakin Gabas da
Chapter 23 · 0% Book details