← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 61

Sashe 38

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

THE BIGINING https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ____________________________ _ PAID BOOK *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , 500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP [ PAGE ___ 16 Jim kadan ta fito sanye da bathrobe , ta shiga dressing room ta shirya cikin kayan barcinta white color , sannan ta fito har yanzu bai motsa ba da ga zaman da ya yi a hankali ta karaso gefensa ta zauna sannan ta kontar da kanta saman shoulder din sa wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo a hankali ya kalle ta ya ce " me ya faru ? cikinki har ya daina ciwo ? " " no har yanzu ya na yi min ciwo " " to tafi ki konta , karfe 12 fa ta yi " " na sani , ina son na tambaye ka wani abu " " minene ? " ya fada ya na meda kallonsa kan wayarsa ya ci gaba da latsawa sai da ta dauki lokaci kafin ta ce mishi " ina so ka fada min yadda zan yi na mallaki zuciyarka " " ni ma ban sani ba " ya fada a takaice " please Baby , ka fada min mana " ta cikin yar shagwaba shiru ya yi bai ce mata komai ba , shi kansa bai san abun da zai ce mata ba , da ya san amsar da zai ba ta da ya fada mata , asali ma shi abun da ya ke ji cikin zuciyarsa har yanzu ya kassa tantance shi , tabbas ya na jin ta cikin zuciyarsa shi ya sa ma ya iya banbanta su cikin sauki ita da Aleenah , kuma ya ke sake mata su na magana , amma shi har yanzu ba ta yi wani abu ba da zai ce son ta ne ya ke cikin zuciyarsa saboda wannan abun , shi dai kawai ya san ya damu da ita saboda amanarta a ka ba shi ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji kawai ta janye kanta da ga saman shoulder din sa , a hankali ta ida Hayewa saman gadon ta konta ta juya mishi baya ta saki kuka kassa kassa ya na jiyo sautin kukanta ya saki wani dan karamin tsaki cikin zuciyarsa ya na fadin " shikenan yanzu ni an hada ni da wani aikin " a hankali ya juyo ya na kallon ta ya ce " kukan me ki ke kuma ? " " to ba kai ne ba na tambaye ka ka kyale ni " " okay , zan fada miki yanzu daina kukan nan " da sauri ta mike zaune ta na murmushi ta ce " shikenan na daina " ta fada ta na kai hannu ta na goge hawayenta sai da ta zauna sannan ya ce mata " okay , abu na farko da ya kamata ki sani shi ne ba na son takura , dan haka duk shirmen da za ki yi ki ka ce za ki takura min zan bar miki gidan, kuma ko Cutie da Daddy ba za su san in da zan je bare ma su ce na dawo " nan take murmushin da ke saman face din ta ya bace jin ya kira sunan Cutie kamar za ta yi kuka ta ce " wai wacece Cutie ? har yanzu ba ka fada min ba " " Cutie is My momy , Cutie shi ne sunan da Daddy ke kiran ta da shi har mu ma mu ka dinga kiran ta da haka , shikenan ? kin ji dadi ? " wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyada mishi kai , sai yanzu ta tuno lokacin da su ka tafi wajen Malik ta ji ya furta sunan Cutie , to hankalinta bai kawo ba ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryarsa ya na fadin " yanzu konta ki yi barci " noke mishi kafada ta yi ta na fadin " no , ka bar ni na ci gaba da kallon ka mana , wai an taba fada maka ka na da kyau ? " " an sha fada min " ya fada ya na fara latsa wayarsa ci gaba da magana ta yi ta na fadin " har so na ke safiya ta yi domin na ci gaba da kallon kyakyawar fuskarka mai yaye dukkan kuncin da damuwar ruhina , please ka juyo ka kalli da fararen idanunka ma su sheqi da haske kamar wani sashi na wata " shi dai bawan Allah ya yi zaune ya na sauraron ikon Allah , har ya fara tambayar kansa anya ba wani abu ta ke sha ba ? yadda ta ke zaune ta na irin wadanan kalaman ko tsoro ba ta ji , ko shi ne ba zai iya ba kai tsaye haka , ta wani bangaran kuma ya na jin dadin kalamanta ya na ga kamar yabon sa ne ta ke yi haka dai ta yi zaune sai zuba ta ke mishi, shi kuma ya na aikinsa da wayarsa , bai da labari har barci ya yi gaba da ita sai da ya ji wajen ya yi tsit ya tabbatar to barci ya yi gaba da ita a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalle ta , ta na barci cikin konciyar hankali , jelar gashinta ya bazun mata saman face a hankali ya kai hannu ya janye mata gashin ya zubawa face din ta ido , in kowa ganin ya ke su na kama ita da Aleenah shi ba ya ganin wannan kamar bai san me ya sa ba , sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta kafin ya tashi a hankali ya kashe lamps din dakin ya kunna bedside lamps sannan ya fito dakin ya janyo mata kofar ya tafi tashi bedroom din INAYA bayan ta baro part din MALIKAT INAS kai tsaye nasu part din ta koma , a nan floor na uku ta tardo Malik , ya na konce cikin bedroom din su , sanye da kayan barcinsa ya zubawa ceiling ido kamar mai tunanin wani abu wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta tako a hankali ta nufi toilet ta shiga wanka ta yi ta fito daure da towel a kirjinta ta na rike da wani dan karamin towel ta na goge gashin kanta har yanzu shi dai ya na yadda ta bar shi ko motsi bai yi ba nan take jikinta ya ba ta akwai abun da ke damun sa ajiye towel din hannunta ta yi saman dressing mirror sannan ta tako a hankali ta zauna bakin gadon ta kai hannu saman face din sa wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ya na lumshe idanunsa a tare ya daura hannu saman nata cikin sanyin murya ta ce mishi " baby , tunanin me ka ke yi haka ? " wani cool murmushi ya saki kafin ya ware idanunsa ya kalle ta ya ce " nothing , just ina tunanin jarabar da Prince zai yi wa yarinyar nan kafin ya fara sake mata , na san za ta sha wuya " wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " kar ka damu ba wata azabar da za ta sha , saboda ya na son ta , ni fa da ita da Twins din ta kassa gane su na yi , shi kuma kallo daya ya yi musu ya gane wacce ce matarsa " wata yar karamar dariya shi ma ya yi kafin ya ce " kamar ba ki san halin Prince ba , ko ya na son ta ba zai yarda da hakan ba , hannu ta kai ta fara shafa kansa ta na fadin " ai halinka ya dauko , kar ka damu in dai ba ta cika kunya ba cikin sauki za ta shawo kansa , kuma kai ma ka san halin Prince abu guntu ke jan hankalinsa , bare in sanyi ya kama shi ko ba ya so sai ya neme ta " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya dariya shi ma ya yi kafin ya kai hannu ya janyo ta jikinsa ta fado saman chest din sa , ya na kallon cikin idanunta ya ce " wane sanyi kuma ? ki ba shi kwana biyu kadai , zai fara .. " ya kai karshen ya na dago kansa a hankali ya manna mata kiss a wuya wata yar karamar dariya ta yi ta kai hannu a hankali ta fara balle button din rigar barcinsa , sannan ta ida Hayewa gadon ta konta a gefensa wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya juyo su na fuskantar juna , nan take labarin ya sauya a ka hau sabon wassa ni kuma na dauki takarduna na fito dan barci na ke ji ) WASHE GARI ALEESHERH da addu'ar barci a bakinta ta farka da ga barcinta , slowly ta ware idanunta ta fara bin dakin da kallo , ta ga ita kadai ce cikin dakin wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta sauko da ga saman gadon , nan ta ga wayarta ajiye saman bedside drawer cikin rudu ta kai hannu ta dauke ta dan ita ta na tune ta bar ta a part din MALIKAT INAS kunna wayar ta yi ta ga karfe 7 da mintina 12 wani cool murmushi ta saki kafin ta fara takawa a hankali ta nufi curtain din da ke fuska kofar shigowa dakin , ta janyo curtain na gefen dama ta rufe rabin glass din , dan wajen ya rage haske , sannan ta nufi toilet ta shiga Jim kadan ta fito sanye da bathrobe ta tsaya gaban dressing mirror ta fara kallon Lotion din da ke sama , ta zabi guda ta shafa sannan ta shiga dressing room after some minutes ta fito sanye da wata gown pink colour mai kyau , ta sha ruwan stone , ta saki gashin kanta har tsakiyar baya , da wasu dan kanana sun zubo mata a gaban goshi , sai tashin qamshi ta ke kai tsaye bedroom din ta fito ta fara bin wajen da kallo , kofofi shidda ne ta gani a wajen kuma duk su na rufe , kawai sai ta nufi hanyar fita corridor din ta fito ta
Chapter 38 · 0% Book details