← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 61

Sashe 18

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

THE BIGINING ( TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ _ PAID BOOK N500 [ FREE PAGE ___ 7 cikin rudu Junior ya ce mishi " ban gane ba uncle , ba ku waya ne da shi ? " " na ga wayar " Fadin Malik ya na mika mishi hannu ba musu Junior ya ba shi wayarsa daukar kiran Malik ya yi ya kai wayar a kunne ba tare da ya ce komai ba babu ko sallama Prince ya ce mishi " kai don Allah ina ka saka wayarka , tun dazu ina kiran ka sai yanzu za ka dauka ? " ya fada cikin tsare gida matse fuska Malik ya yi kamar ya na gabansa ya ce " ba shi ba ne , Ubanka ne ke magana " " Daddy ! " Prince ya fada da dan karfi dan sam bai yi tunanin Malik na Saudiya ba " ka san Allah ? ka san da ga shi ba wani abun bautar ko ? to duk abun da ka ke ka bar shi ina son ganin ka gobe a Saudiya , in ba haka ba jikinka zai fada maka " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ko jiran amsarsa bai yi ba ya katse kiran sannan ya mikawa Junior wayarsa ya na fadin " ko ya kira ka kar ka dauka , tsaya ma , a ina ya ke ? " wata yar karamar dariya Junior ya yi kafin ya ce " ya na Yemen , wai wani contract ne ya ke so ya yi sign da....... " bai karashe maganarsa ba Malik ya katse shi da cewa " zan ci ubansa shi da contract din , ina ga yaron nan ya fara raina ni zan yi maganin shi , ya dawo dai ya same ni " dariya kawai Junior ya yi ya san yau Prince ya shiga tsaka mai wuya dan ba mai kwatar shi da ga hannun Malik ya na a haka ya ga Malik ya mike tsaye ya na fadin " bari na koma wajen wancen babyn shi kuma " ya fada ya na nufar hanyar komawa parlourn Diya da kallo Junior ya raka shi ya na murmushi kawai , sai da ya shiga sannan ya ci gaba da latsa wayarsa ai ko bai yi two minutes ba Prince ya sake kiransa murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya mike tsaye ya baro part din sannan ya dauki kiran dan kar Malik ya jiyo su ko sallama Prince bai yi mishi ba ya ce " kai don Allah uban wa ya ce ka bawa Daddy waya ? " ya fada da alamun ya na cikin baci n rai dariya Junior ya yi ya na ci gaba da takawarsa cikin harabar masarautar ya ce " to ai ba ni na ba shi wayar ba , karba ya yi da karfi , kuma malam ka shirya gobe ka dawo dan wlh Uncle ya na fushi da kai ba kadan ba , dan haka ka bar contract din nan ka dawo " murya Prince na jiyo ya na jan tsaki kafin ya ce " Wlh ba zan kyale ka ba , jira ni goben , no sens kawai " ya na gama fadar haka ya katse kiran dariya sosai Junior ya yi kafin ya sauko wayar ya meda cikin aljihunsa ya ci gaba da takawa ya nufi part din Malikat Inas , har ya zo shiga part din Faaz ya zo da gudu ya buge shi ya riga shi shiga part din har sai da Junior ya yi gaba kamar zai fadi " kai yi a hankali mana , ka buge ni " Junior ya fada cak Faaz ya tsaya ya juyo ya wurga wa Junior wani muguwar harara sannan ya juya da gudu ya shiga parlourn Malik Inas Baki sake Junior ke kallon sa , ko hararrar me ya ke masa ? tukunna ma da ga ina ye ke ya na wannan gudun ? da wadanan tambayoyin ne ya shigo parlourn MALIKAT INAS ya na sallama cen kassan makoshi nan ya tardo Inaya Zaune tare da Rianna da Malikat Inas , Faaz na zaune saman cinyar Rianna kai ka ce yaronta ne na gaskiya Inaya na ganin Junior ta saki wani cool murmushi ta na fadin " Junior ? na zata ku na tare kai da wance mai shashatar da ba ya zama waje guda " wata yar karamar dariya Junior ya yi kafin ya karaso gefenta ya zauna ya riko hannunta ya manna mata kiss ya na fadin " na ji dadin ganin ki momy " wani dan karamin murmushi ta yi kafin ta kai hannunta saman face din sa , ta matso a hankali ta manna mishi kiss saman forehead cike da kula ta ce mishi " Hope ka na cikin koshin lafiya ? " " i'm fine momy , amma momy ban ga Princess ba , ko ba tare ku ke ba ? " RIANNA ce ta amsa mishi da cewa " no , sai nan da kwana biyu , gobe za ta yi last exams din ta , da ga nan kuma shikenan ita da school sai dai Aiki " wani kyawatacen murmushi ya saki kafin ya ce " wow , momy ki ce mun yi Doctor cikin family " dariya kawai Inaya ta yi ta na shirin magana ta jiyo Muryar Faaz ya na fadin " ni ma zan zama doctor , na yi ta yiwa mutane Allura " wata yar karamar dariya Rianna ta yi kafin ta kai hannu ta ja mishi kumatu ta na cewa " babyna , to ai sai mutum na ciwo a ke mishi allura , ba haka kawai na " " to ni ko ba su ciwo sai na yi musu , kuma da ke zan farawa sannan Ammie , dan ta tsufa " dariya duk su ka yi ban da Junior , ya rasa dalilin da ya sa tun lokacin da Faaz ya shigo Daular ya kassa sake mishi MALIKAT INAS ce ta cewa Faaz " to sannu Likita , wai RIANNA yaushe za ki meda shi school ne ? na ga ai an fara karatu " " next week , zai fara tafiya , yanzu ina son na kammala da maganar admition din sa ne " Fadin Rianna " ina ne school Aunty ? " Faaz ya tambaye ta da murmushi a face din ta ta ce " wajen da za ka zama doctor , tare da sauran yara kamar kai " " hakan na nufin Aunty zan bar gidan nan ? " ya fada ya na zaro idanu " yes am........ " ba ta karasa maganarta ba ya sauka da ga saman cinyarta da gudu ya na fadin " no , ni babu in da zan je " ya na gama fadar haka ya nufi corridor ta gudu ya shiga a hankali RIANNA ta mike ta bi bayansa dan ta rarrashi babynta ta na barin wajen Junior ya mike ya dawo gefen MALIKAT INAS ya konta ya tada kai da laps din ta ya na fadin " Ammie ina da albishir mai dadi " hannu ta kai saman kansa ta fara shafawa ta na fadin " ba ni na sha " " hmmm , Ammie gobe Prince zai zo nan Saudiya " a tare ita da Inaya su ka ce " what ? da gaske ? " bushewa da dariya ya yi har da tapi ya na fadin " da gaske Ammie , yanzu Uncle ya yi mishi magana , ya ce in bai zo nan ba gobe to jikinsa zai yi tsami in su ka hadu " " oh Allah ni Inaya , wlh Ammie na rasa ya zan yi da yaron nan " Inaya ta fada ta na buga tagumi " me zai hana ki yi mishi aure ? ki huta kawai " " aure kuma Ammie ? da wa ? ki na ganin zai yarda ya yi aure kawai dan na ce mishi ? kamar ba ki san halin shalelenki ba " " na sani , duk wannan Rashin zaman nasa dan ba shi da ahali ne , da ya samu familyn da za su bukaci kulawarsa da hankalinsa za ki ga ko ce mishi a ka yi ya tashi ya tafi ba zai iya ba saboda hankalinsa ba zai iya konciya ba in ya tafi , kullum zai dinga tunani wane hali familynsa ke ciki , kin ga aure ne kawai hanyar da za ku yi anfani da shi ya daina wannan yawon da ya ke " shiru Inaya ta yi na dan lokaci kamar mai tunanin wani abu ganin ta yi shiru ne ya sa MALIKAT INAS sakin wani dan karamin murmushin gefen fuska ta ce " ya kamata ki tashi ki koma wajen Malik , karfe 10 fa ta kusa " gyada mata kai kawai ta yi ta na murmushi kafin ta mike ta na fadin " sai da safe Ammie " " sai da safe " MALIKAT INAS ta fada da sauri shi ma Junior ya ce " Good night momy " murmushi kawai ta yi mishi kafin ta sa kafa ta fice parlourn ta na fita Malikat Inas ta ja kunnen Junior ta na fadin " kai ma ban manta da kai ba , yaushe za ka yi auren ? " cikin yar shagwaba ya ce " ashhhhh Ammie da zafi fa , kuma ai kin bari har ta zo ko ? " " shikenan , zan yi wa Malik maganar " da sauri ya mike zaune ya na fadin " noooooo , Please Ammie kar ki fada mishi " " me ya sa ? " girgiza mata kai ya shiga yi ya na fadin " ni dai kar ki fada mishi , zan fada mishi da kaina in lokacin ya yi , please Ammie " ya kai karshen ya na marairaice mata fuska " shikenan ba zan fada mishi ba " " yawwa Ammie na , shi ya sa na ke son ki " ya fada ya na murmushi kafin ya koma ya konta su ka ci gaba da hirar su kamar wasu abokai Ko minene su ke magana a kai , wace magana ce Junior ba ya son
Chapter 18 · 0% Book details