Sashe 16
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baki murya har kerma ta ke ta ce " don Allah ka tsaya ka saurare ni , ina son mu yi magana , please " cikin bacin rai ya tako gadan gadan gare ta ta na ganin ya fara takowa ta fara yin baya ta na girgiza mishi kai har sai da ta kurewa bango ya isowa ya kai hannu ya damko wuyanta , ya na kallon cikin idanunta ya ce " zan rufe ido , na kirga zuwa biyar , in har ba bude ido na gan ki cikin dakin nan , sai na yi miki abun da sai kin tsani kanki da kanki , sai kin mutu ki na nadamar hada hanyarki da ni , so get out tun kafin raina ya baci " ya na gama fadar haka ya saki wuyanta , ya kai hannu ya bude kofar dakin ya lumshe idanunshi ya fara kirge da ga 0 kuka ta saki hawaye na zubo mata bibiyu , kafin ta juya jiki a sanyaye ta fice dakin dai'dai lokacin da ya kai 5 ya na bude ido ya gan ta tsaye bakin kofar dakin ta juyawa kofar baya da karfi ya meda kofar ya rufe ya na jan tsaki , kafin ya cusa hannu cikin gashin kansa dan ta na neman ta tayar mishi da hankali wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya juya ya na kallon fruits din da su ka zube cikin dakin duk wajen ya baci wani dogon tsaki ya ja kafin , ya karaso bakin bed din sa ya dauki laptop din sa , da wayoyinsa sannan ya bude box din bedside drawer , nan na ga wajen cike da magnetic card har wajen goma ko fi duba su ya fara yi daya bayan daya har ya samu wadda ya ke so , sannan ya dauka ya nufi kofar fita dakin ya fice ya na fitowa ya nufi room din da ke fuskantar wadda ya fito ya na ce ma Bodyguards din shi " Gobe ku medo kayana cikin wannan bedroom din " ya fada dai-dai lokacin da ya shige cikin dakin ya medo kofar ya rufe DAULAR YEMEN ALEESHERH ta na konce tsakiyar bed din su , ta yi rub da ciki sai kuka ta ke yi kamar ranta zai fita ita dai Aleenah ta na tsaye ta zuba mata ido, tun dawowar ta ta ke kukan nan , ta tambaye ta lafiya amma ta ki fada mata wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zauna bakin gadon ta ce mata " ya isa haka kukan , ki fada min me ya faru a cen , ko bugun ki ya yi ? " girgiza mata kai Ta yi a hankali ba tare da ta ce komai ba " to minene matsalar ? sai kuka ki ke kamar wadda uwarta da ubanta su ka mutu " ta fada ta na dafa shoulder din ta " Aleenah , i think i'm crazy " ta fada ta na kukan a hankali Aleenah ta kai hannu ta tallabo ta , nan ta ga fuskarta a bushe ko digon hawaye babu wani dan tsaki Aleenah ta ja ta na janye hannayanta ta ce " kin san Allah , in ba ki bude baki ki ka fada min abun da ke faruwa ba ba zan kara taimaka miki ba , sai dai ki san yadda za ki yi ke kadai " wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi har da daga kai sama kafin ta sauko shi ta ce " Aleenah , this guy is so handsome , Allah in ban same shi ba ina ga kashe kaina kawai zan yi , kin san yadda na ke , ba na saurin sakin wa mutum face , amma wlh lokaci guda ya tafi da zuciyata ban san ya hakan ta faru ba , ina jin sa har cikin zuciyata Aleenah " tsaki kawai Aleenah ta yi , ita abun Aleesherh ya na neman ya ba ta haushi ma , sai ka ce a kanta a ka fara soyayya mikewa tsaye ta yi ba tare da ta ce komai ba ta shiga toilet ta medo kofar ta rufe ta na shiga Aleesherh ta saki wani cool murmushi ta dauki pillow ta rungume ta na fadin " minene sunanka ? zan so na san abun da ka ke boyewa bayan wannan zuciyar taka , ban san ya a ka yi na kamu da son ka lokaci guda haka , amma na san wani abu guda ,,,,, ina son kasancewa tare da kai , har abada har bayan mutuwa " ta karashe maganar ta na kara matse pillown a jikinta to fa da Alamun wata ta fada tarkon Prince, yanzu ya za ta kasance tsakanin su ? za ta iya fada mishi abun da ke cikin ranta ? zai amince ko kuwa ? ) DAULAR SAUDIYA MALIK zaune ya ke cikin parlourn part din Diya , ya na Sanye da jallabiya white color ya daure smooth hair din sa a baya duk da ba wani yawa ne da shi ba a yanzu Diya na zaune gefensa , ya na sanye da jallabiya shi ma amma darck blue , ya na rike da wayarsa sai faman latsawa ya ke cikin nitsuwa Malik ya ce mishi " please sauke wayar nan ka ci abinci nan ka sha magani " murmushi mai dan sauti Diya ya yi kafin ya ce " ka ga ni fa ba yaro ba ne , ka kyale ni " " na sani , amma na zo nan ne dan na kula da kai , ba zan bar wajen nan ba sai ka cinye abincin nan ka sha magani ka konta sannan zan tashi na tafi " dago kai Diya ya yi ya kalle shi ya marairaice fuska ya ce " please i'm not a baby , tafi ka kula da Cutien ka , ni fa i'm okay " tsuke fuska Malik ya yi ya ce mishi " za ka ci abincin nan ko sai na yi maka da karfi ? " wata yar karamar dariya ya yi , ya na shirin magana wani saurayi ya fito da ga cikin corridor din part din , ya na sanye da Short da t-shirt ash color ma su kyau , ya na kama tak da Diya kamar an tsaga kara kuma ya na jinin Nesrine sosai , a shekaru zai kai 30 haka ko fi ma , ya na murdaden jiki a haka har ya karaso cikin parlourn ya mikawa Diya wasu drugs ya na fadin " Daddy , please ka cinye abincin nan ka sha magani , dubi har ya yi sanyi fa " matse gera Diya ya yi kafin ya dago kai ya kalle shi ya ce " kai Junior ni tsaran wassan ka ne , ka koma in da ka fito da maganin nan ba abun da zan sha , ku kyale ni don Allah kun wani saka ni a tsakiya sai ka ce baby , ni yanzu aiki na ke ku bari har na kammala " marairaice fuska Junior ya yi kafin ya ce " Daddy , i say please , wai me ya ba ka damu da lafiyarka ba ne ? in ba ni ko momy mu ka ba ka magani sam ba ka damu ka sha ba , so ka ke mu koma Asibiti ne ? " hannu Malik ya kai ya kwace wayar Diya ya tilla saman sofar bayansu ya ce mishi " Diya , ci abincin nan , now ! " tsaki Diya ya ja , kafin ya kai hannu ya dafa sofar ya na neman tashi amma ina kawai sai komawa ya yi ya fadi da sauri Junior da Malik su ka kai hannu su na neman taro shi " please ku bari , i'm okay na ce muku " Diya ya fada ya na tare su kafin ya koma ya zauna ya na sauke ajiyar zuciya cikin bacin rai Junior ya watsa drug din hannunsa a kassa ya na fadin " okay , na kyale ka , yi yadda ka ke so " ya na gama fadar haka ya nufi kofar fita ya fice da sauri Diya ya shiga kiran sunansa , sarai jiyo shi amma ya share shi ya sa kafa ya fice sai da ya fita sannan Diya ya kalli Malik ya ce mishi " please je ka yi mishi magana " gyada mishi kai Malik ya yi kafin ya mike ya na fadin " zan dawo gare ka " ya fada ya na takawa ya bi bayan Junior a cikin Harabar part din ya tardo shi zaune saman wata chair ya na rike da wayarsa ya na latsawa cikin nitsuwa Malik ya karaso wajen ya dafa shoulder din sa ya na kiran sunansa ba tare da ya dago kai ba ya amsa mishi " me ya faru ka ke fushi ? " " nothing uncle " ya fada a takaice a hankali Malik ya zauna gefensa ya na fadin " Nawfel , please tell me , ko sai kai ma ciwon zuciyar ya kama ka na yi jinya biyu ? " " uncle ka na fa ganin abun da Daddy ke yi , sam ba ya kula da kansa ka duba fa abinci ma ya ki ci bare ya sha magani , ta ya zai warke a haka ? " " please ka daina tada hankalika , Daddynka fa in ya na ciwo sai an yi hakuri dan wlh ya fi baby jaraba , kuma ina ga mu na matsa mishi dayawa , mun saka shi a gaba sai d'ura mishi magani mu ke shi ma zai gaji " " to in bai sha magani ta ya zai warke ? kawai na lura ba ya son rayuwarsa ne , ya gaji da ganin mu ne shi ya sa " ya fada ya na kauda kai gefe dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " wa ya fada maka ya gaji ku ? ba zai taba gajiya da ganin ku ba a tare da shi , kawai mu kyale shi ya kula da kansa kamar yadda ya ke so , na san ya na tunanin kamar mu na ga ba zai iya yin komai ba ba da taimakon