Sashe 10
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
THE BIGINING ( TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ [ PAGE___ 4 MASARAUTAR YEMEN a hankali ya ke tafiya cikin wata makekiyar library , ya na sanye da wasu suit white color ma su bala'in kyau da tsada , ya na tafiya a hankali da waya a kunnensa da alamun kira ne ya ke sai da ya karaso wajen wani closet sannan ya tsaya ya na fadin " Junior , ka na son ka ba ni aiki wlh , ina zan samo wannan littafin don Allah ? " " please Bro , ka duba na san za ka same shi a nan saboda marubucin na nan kassar Yemen ne , ka duba mana pleaseeeee " ya fada ya na marairaice murya wani dan karamin tsaki Prince ya yi kafin ya sauko wayar ya meda cikin aljihunsa , ya kai hannu ya zaro wani book , dai-dai lokacin da a ka zari book din da ke gefensa ta daya bangaran idanunsa ba su sauka ko ina ba sai cikin nata su ka yi ido hudu a rude ya zuba mata ido ya kasa gasgata abun da ya ke gani ta na sanye da wata tsadadiyar Gown irin wannan mai budewar nan da ga kassa , ta yafa wani dan karamin veil fari a kanta amma jelar gashinta duk a waje ta ke , duk da ta yi simple make up hakan bai hana shi gane ta ba , kai ka ce ita ce diyar Sarkin Yemen din baki daya a hankali ta juya ta bar wajen ba tare da ta ce mishi komai ba ta na sunkuyar da kai shi kuwa tsaki ya ja kafin ya meda book din , ya bar wajen shi ma , kai tsaye wajen librarian din ke kula da libraryn ya koma murya kassa kassa ya yi mata sallama da kyair ma ta iya jiyo ta da fara'a a fuskar ta ta amsa mishi ta na tambayar ta wacce hanya za ta taimaka mishi wayarsa ya fiddo , ya fara latsa screen din na dan lokaci kafin ya mika mata ya na fadin " wannan littafin na ke nema " ba musu ta kai hannu ta karbi wayar ta na kallon sunan littafin bayan ta karanta ta mika mishi wayarsa ta na fadin " i'm sorry Sir , but duk wani littafi da ya shafi tarihin masarautar Yemen a libraryn Daular a ke kai shi , ba za ku iya samun shi a ko ina ba sai a Daular , i'm sorry " wani dan karamin tsaki ya ja ya na meda wayarsa cikin aljihu ya ce mata " Thanks " a takaice kafin ya juya ya fara takawa zai bar wajen har ya iso bakin kofar fita idanunsa su ka sake sauka saman ta ta na zaune saman chair ta na rike da book kamar wata mutuniyar kirki a hankali ya juya ya fara takawa ya nufi in da ta ke babu ko sallama ya ce " me ki ke yi a nan ? ko yanzu ma kin zo yin satar ce a nan ? " slowly ta dago kai ta zuba mishi ido ba tare da ta ce komai ba sai da ta dauki wajen one minute kafin ta ajiye book din hannunta saman table din , a hankali ta juya ta fara takawa ta nufi hanyar fita ta fice ba tare da ta ce mishi komai ba da kallo ya rakata har sai da ta fita ya kuma kassa ce mata komai a haka har sai da ta fice sannan ya yi saurin bin bayanta dan ya na so ya san ya a ka yi jiya ta riga shi komawa Hotel , me ta ke yi a cen ma bayan yanayin da ya gan ta sam ba ta yi kama da me aiki a irin wannan hotel ba , yanzu kuma sai ka ce ita ce diyar Al-Sayid , ko dai aljana ce ke bibiyar ba shi da labari da wannan tunanin ya fito libraryn amma wani abun mamaki ya na fitowa ya neme ta sama da kassa ya karasa a gaban idon shi ta fito ko ten secondes bai yi ba ya biyo bayanta shi ma ya a ka yi ta bace mishi in one seconde haka , ko dai aljana ce ? ni ma abun nan ya fara damu na , ko dai aljana ce ? duk in da ya je sai ya gan ta , ni dai abun nan ya fara ba ni tsoro ) wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ci gaba da takawarsa ya nufi motarsa ya shiga su ka bar wajen DAULAR YEMEN FADAR AL-SAYID ABDOUL-MUEED Fadar babu kowa a ciki kamar an yi busa , bai su wuce mutum goma cen na hango Al-Sayid zaune saman kujerarsa , fuskarsa babu yabo babu fallasa , kai da ga gani ka san zai yi fara'a sai tattauna su ke da mutanan fadarsa cikin nitsuwa su na a haka na ga wata mata ta shigo fadar ta na sanye da wasu kaya farare , a shekaru za ta kai 40 haka ko fi , da gudu ta karaso tsakiyar Fadar ta Zube saman guyiwowinta ta sunkuyar da kai ta na fadin " Gaisuwa na ke ya ke shugabana , ranka shi dade akwai matsala , na duba part din yan biyu ban gan su ba ranka shi dade , na duba hart part din mai dakin gabas da mai dakin yamma amma duk sun ce tun jiya cikin dare ba su gan su ba " wani dogon nunfashi Al-Sayid ya ja kafin ya daga mata hannu a hankali ya na fadin " za ki iya tafiya ba sai kin damu kan ki ba " ba musu ta tashi ta fice Fadar ta na fita daya da ga cikin mazauna fadar ya ce " ranka shi dade , Gimbiya Aleesherh da Gimbiya Aleenah ba su cikin Daular nan fa , kuma ka ce ta tafi kar ta damu kanta , in wani abu ya same su fa ? " wani dan karamin tsaki ya ja ya na fadin " to ya ke so na yi ? yaran nan ne sam ba su jin maganata , ban san ya a ka yi su ka gano hanyoyin sirrin Daular nan ba , tun da ga lokacin shikenan sun samu hanyar fita , su na cen cikin masarautar su na shirme , ni ban ma san ya zan yi da su na " " ranka shi dade tun da ka kassa , me zai hana ka aurar da su ? " " aure kuma ? to wa ma zai auri wadanan yaran ? yara a ce ba ku da aiki sai wassa , ni da na Samu wanda zai aure sun ni da kyauta ma zan ba shi , saura kadan su saka min hawan jini dan jaraba " a tare duk mutanan Fadar su ka yi dariya , sun san halin Shugaba nasu da yaransa , su kadai Allah ya ba shi , tun su na yara ya yi mugun shagwaba su , ya ke tarerayar su kamar Egg , ai dole yanzu su gagare shi cen sai daya da ga cikin su ya ce " ranka shi dade me zai hana ka bawa yaran Malik Nawfel Hicham Bin Jaabar auren su ba ? a tarihin masarautar Saudiya ba a taba samun Malikat da ga masarautar Yemen ba , me zai hana su kasance na farko , hakan zai kara gyara alakar kasuwanci da ke tsakanin Saudiya da Yemen , ko ya ku ka gani ? " ya fada ya na kallon sauran mutanan fadar wanda ya yi magana da farko ne ya karbe zancen da cewa " haka ne ranka shi dade , ina ga hada Zuri'ar ka da ta Malik Nawfel Bin Jaabar ba karamar daukaka zai janyowa Masarautar Yemen " " in na gane kamar auren yarjejeniya ne za a yi musu ko kuwa ? " Fadin Al-Sayid wani ne ya amsa mishi da cewa " a'a ranka shi dade , babu wanda zai yi wa aurensu kallon auren yarjejeniya ........... " bai qarashe maganarsa ba su ka jiyo sallamar mutum cikin fadar a tare duk su ka juya su na kallon Prince tsaye bakin kofar Fadar cikin rudu Al-Sayid ya ce mishi ya karaso ba musu ya karaso tsakiyar fadar ya tsaya , ya dan sunkuyar da kai ya na fadin " ina mika sakon gaisuwata ga shugaban wannan kassar mai Albarka , tare da dukkanin mazaunan wannan wajen " daya da ga cikin su ne ya amsa mishi da cewa " A gaishe ka dan Saurayi , me ya kawo ka gaban Al-Sayid ? " cikin girmamawa Prince ya ce " ranka shi dade sunana Prince , ina neman Alfarma wajen shugaba " " Alfarma kuma ? ka fadi abun da ya kawo ka " fadin Al-Sayid " ranka shi dade , wani littafi na ke nema a kan tarihin tsohuwar Yemen , na je library da dama amma sai a ce min duk littafan tarihin masarautar Yemen , su na a cikin Libraryn Daular , ranka shi dade zan so a ba ni dama na duba Littafin in har ba damuwa " wani dan karamin murmushi Al-Sayid ya saki kafin ya ce " Na ji dadin ganin har yanzu akwai matasan da su ka damu da sanin tarihin Tsohuwar Yemen , Allah ya yi maka Albarka yaro , Allah ya kara Basira " a tare duk su ka amsa mishi da Ameen kafin Prince ya daura da cewa " Godiya na ke ya shugaba " " Za ka iya zuwa ka duba duk littafin da ka ke so , na ba ka izini " dan rinsinwa Prince ya yi ya na fadin " Godiya na ke ya shugaba , Allah ya ja zamanin mai martaba , Allah ya kare ka da sharin makiya " da Ameen yanzu ma duk su ka amsa mishi , da ga nan ya juya tare da wani dogarin da zai raka shi libraryn su ka bar wajen cikin nitsuwa ya ke tafiya kai a sunkuye ya na latsa wayarsa cikin filin masarautar cen kawai na ga ya tsaya Cak waje guda slowly ya dago kai