← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 61

Sashe 60

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

cikin rasuwar Ammie ? " shiru Malik da Diya su ka yi ba su ce mishi komai ba , musaman Malik shi kadai ya San abun da ya ke tunani ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ga kawai Prince ya mike tsaye ya bar wajen ya nufi part din shi a haka shi ma Junior ya mike ya na fadin " sai da safe Daddy , sai da safe uncle " a tare Malik da Diya su ka amsa mishi , sannan ya fara takawa ya nufi part din Diya ya shiga bangaran su shi dai Malik duk jikinsa ya yi sanyi ya ma rasa abun da zai ce in har da sa hannu Faaz cikin rasuwar MALIKAT INAS to da hannunshi zai kashe shi kafin ya kai ga wanda ya aiko shi yanzu tambayar da ta tsaya mishi a kai ita ce , wa zai aiko Faaz dan cutar da su ? wanene makiyinsa cikin masarautar ? shi dai ya san a halin yanzu ba wanda zai ce ga shi makiyansa , sai dai na Diya , amma kowa ya na da shaidar Diya bai da wani dogon hadi da MALIKAT INAS , to wanene ? gaskiya dole ya san abun shi ma dole ya fara bincike a kan Faaz dan in har maganar Junior ta tabbata, ya na niyar cutar da su ya fara rasa ahalinsa kenan ya yi nisa duniyar tunaninsa ya jiyo Muryar Diya ya na fadin " ya kamata ka je ka kwanta , dare ya yi " gyada mishi kai ya yi kafin ya mike tsaye a hankali ya na fadin " gobe za ka je fada ne ? " " gobe Friday fa , ina ga gaskiya zan yi hutu week-end , na fara gajiya " murmushi mai dan sauti Malik ya yi kafin ya sa kafa ya bar wajen ya nufi part din su da kallo Diya ya raka su har sai da ya yi nisa sannan shi ma ya tashi tsaye , ya na fadin " hakan na nufin duk su na da tantama a kaina ? dole na janye hankulansu da ga kaina har momy ta fada min shirin mu na gaba " da kallo Diya ya raka su har sai da ya yi nisa sannan shi ma ya tashi tsaye , ya na fadin " hakan na nufin duk su na da tantama a kaina ? dole na janye hankulansu da ga kaina har momy ta fada min shirin mu na gaba " ya na gama fadar haka kawai na ga ya koma Faaz lokaci guda a hankali ya juya ya nufi part din MALIKAT INAS ya koma Hakan na nufin tun farko da Faaz ne su ke hira ba su da labari ? yanzu ina Diya na gaskiya ya yi ? kar a je ya cutar da shi ( to ni na ce mi ? yanzu bari mu jira mu ga me Faaz ya ke shirin aikatawa , duk yadda a ka yi ba al'heri ba ne , a yanzu ahalin Malik za su fuskanci wani sabon hatsari , ga Prince kuma ya ce yaga Nayab , a ka je da gaske shi ne amma ya zo musu a matsayin mugu ? ) Yau dai na gama free pages ina Book 1 , me son cigaba mu ha u a book 2 Me bukatar yin magana da ni , zai iya ta o ni ta wannan number +22798999753 *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , 500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP IN* *HAR ZUWA RANAR FRIDAY ZAI KASANCE 300* ________________
Chapter 60 · 0% Book details