Sashe 35
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigo masarautar , kun san yadda yayanku ya ke in har da baby a gabansa cikin sauki za su gane shi dan ya tsani baby , in har Nayel ya samu magaji kafin yayanku ya hau kujerar Malik to tabbas akwai matsala babba , duk abun da zai faru ki tabbatar wani abu bai shiga tsakaninsa da matarsa ba " Fadin Queen , da ga haka ta bace bat lamps din dakin su ka kunnu baki daya wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya janyo chair ya zauna ya buga uban tagumi ya na sauke nunfashi a hankali cen sai ya ce " shikenan yanzu ba zan samu Prince ba ? da a ce Big bro bai min kallon kanwarsa da na so shi amma sister din sa ta jini ya dauke ni , Prince din ma da na yi tunanin zan samu wannan yar iskar ta zo ta kwace , ni zan so na ga wace mara sa'a ce ta shigo gona ta , in dai ina cikin masarautar nan ba zan taba bari ta mallaki zuciyar Prince " ya na gama fadar haka ya bushe da dariya shi kadai ( IN NA GANE KENAN KUJERAR MALIK SU KE HARI SU MA ? TO ALLAH YA BA DA SA'A , NI NA BI BAYAN INAYA INAYA da Sallama a bakinta ta shigo parlournsu da ke floor na uku , Malik na zaune shi da Diya su na hira cikin nitsuwa wani dan karamin murmushi ta saki dan ba karamin dadi ba ta ji ganinsu a haka ba karasowa ta yi ta na fadin " Malik yau kuma kai ne a part din namu ? " wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " Babyn malam , ga wanda ya janyo ni nan cewa ya yi wai na daina zama a waje guda shi ya sa na biyo shi " sai da ta karaso ta zauna gefen Malik sannan ta ce " ya yi gaskiya , in ka na takawa za ka ji sauki da maza , kuma kai ma za ka ji dadin hakan " " hmmm , ki na dai son kare mijinki , shikenan bari na tafi " ya fada ya na kokarin mikewa da sauri ta taro shi da cewa " a'a koma zauna ni ma shigowar tsaye ce na yi , ina son na je airport na tarbi Matar Prince " ta fada ta na dawo da kallonta kan Malik da ya tsare ta da ido tun lokacin da ta zauna a wajen _________________________________________ [ FREE PAGE ___ 15 da sauri ta taro shi da cewa " a'a koma zauna ni ma shigowar tsaye ce na yi , ina son na je airport na tarbi Matar Prince " ta fada ta na dawo da kallonta kan Malik da ya tsare ta da ido tun lokacin da ta zauna a wajen sai da ya kare mata kallo da kyau kafin ya ce " ba tare Prince za su zo ba ? " girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " no , ya ce shi sai wajen karfe 10 zai shigo Saudiya , akwai aikin da ya ke son ya gama a cen " " kira min shi " ya fada cikin tsare gida ya na matse gera dafa hannunsa ta yi ta na fadin " please ka kyale shi , tun da ya ce zai zo ka bar shi mana , na ga ka na son matsa mishi dayawa " " ba matsa mishi na ke ba , ba ya jin magana ne shi ya sa , ta ya zai raba yarinya da familynta sannan ya kassa kawo ta cikin tashin familyn da kansa , at least da sai ya biyo ta in ta sauka sai ya koma , ba ma ya tsoron wani abu ya same ta " " in ya dawo ya san ba za ka bar shi ba ya koma " " Cutie , na ga alamun ke ki goya mishi baya ya na duk abun da ya ke so " " kamar kai da Princess ba " ta fada ta na ware mishi kananan idanun nan nata wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya " na ji shikenan , amma zai dawo ya same ni " dariya ta yi kafin ta matso a hankali ta manna mishi kiss saman kumatu ta mike tsaye ta na fadin " sai na dawo " ta kai karshen ta na fara takawa ta koma cikin lift shi dai Diya ya yi zaune ya saka su a gaba ya na kallon dramar su gwanin burgewa da ga ji ka san su na son junansu fiye da komai bayan ta baro part din part din MALIKAT INAS ta koma su ka ci gaba da hirarsu , After one hour Junior ya kira ta ya ce sun sauka da ga nan ta tashi da kanta ta je airport dan tarbar sirikarta bayan ta je airport a nan reception ta ci karo da su zaune saman chair su na jiran ta Junior na ganin ta ya yi sauri ya mike ya rungume ta ya na fadin " momy " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " sake ni na ga daughter di ta " sai da ya yi dariya shi ma sannan ya sake ta ya dawo gefenta ya tsaya kallon su da kyau Inaya ta yi cikin rudu , ita mutum biyu ta ke gani ya hakan ta kasance amma sai ta shanye abun da ke cikin zuciyarta ta kalli Junior ta na daga mishi gera a hankali ya kai bakinsa a kunnenta , cikin rada ya ce " sunanta Aleesherh , dayar twins din ta ce Prince ya ce mu taho da ita " wani dan karamin murmushi ta saki sai yanzu ta gane abun da ke faruwa cike da kula ta kira sunan Aleesherh slowly ta dago kanta ta kalli Inaya nan take Inaya ta ga hawayen da ke konce saman face din ta duk da ta wanke face din ta cikin jet wani dan karamin murmushi Inaya ta saki kafin ta mika mata hannu ba musu ta karaso ta riko hannunta sannan ta kalli Aleenah ta ce " ke kuma ya sunanki ? " ita ma kanta na sunkuye ba ta dago shi ba ta ce " Aleenah " " Aleenah , yanzu mu tafi gida ko ? " ta fada ta na mika mata hannu ita ma ba musu ta matso ta riko hannunta , da ga haka ta juya su ka baro airport din , su ka shiga mota guda ita da Aleesherh , Aleenah kuma ta shiga tare da Junior saman hanyarsu Inaya sai bin Aleesherh da kallo ta ke yi , amma ta sunkuyar da kai ko sannu ba ta ce ba wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta kai hannu ta riko hannunta , cikin sigar rarrashi ta ce mata " na san abun da ki ke ji , kar ki damu za mu kula da ke saboda ke ma d'iyar mu ce , ki kontar da hankalinki ba abun da zai faru da ke in sha Allah , ko akwai wani abu da ke damun ki ? " ta fada dan ta ga yanayinta sam ba ya kama da na yar uwarta ta na gudun wani abu Prince ya fada mata da ya karaya mata zuciya gyada mata kai Aleesherh ta yi a hankali alamun Eh cike da kula Inaya ta ce mata " fada min minene ? " sai da ta hadiye yawu kafin ta ce " ku yi hakuri in har abun da zai fada bai yi muku dadi ba " " kar ki damu fadi maganarki kawai " " don Allah wacece Cutie a wajen Prince ? , ina so na sani in ya taba yin aure kafin ni " wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " me ya ce miki a kan Cutie ? " " she is His first love ya ce min " ta fada idanunta na sake cikowa da ruwa yanzu ma dariya ta yi kafin ta ce " kar ki damu , wassa ne kawai ya ke miki , Prince bai taba ko girlfriend bare aure , ba wani First love , na san ya fadi hakan ne kawai dan ya ga in ki na kishi ne ko ba ki yi , na kuma ji dadi da ki ka yi min wannan tambayar , hakan na nufin ki na kishin shi , kenan ki na son shi , right ? " shiru Aleesherh ta yi ba ta ce komai ba , ita har yanzu ba ta samu amsar tambayarta ba , ba ta ji wacece Cutie ba , tun da har Prince ya bude baki ya ce ya na son ta hakan na nufin ta na mahimanci a wajen sa fiye da ita ganin ba ta amsa mata ba kawai ya yi shiru , ba wanda ya ce udan har su ka iso cikin Daular Saudiya ba karamin mamaki Aleesherh da Aleenah su ka yi ba ganin wannan uwar Daular , duk da Daular Yemen na da girma amma ta Saudiya ta yi ukun ta wajen Girma har kyau kai tsaye Inaya ta kai Aleesherh building din su dan za ta so ta gabatar da ita ga Malik sai da su ka iso bakin kofar part din sannan motarsu ta tsaya , ta sauko sannan ta zagayo da kanta ta bude wa Aleesherh ta na mika mata hannu saukowa da ga cikin motar ta yi sannan ta riko hannun Inaya su ka shiga cikin part din , Aleenah kuma Junior ya tafi da ita part din MALIKAT INAS sai da su ka shiga lift sannan Inaya ta sa hannu ta janyo hular Alkyabarta ta rufe mata kai su na nan dai shi da Diya kamar yadda ta bar su da sallama a bakinta ta shigo parlourn ta na janye da Aleesherh a tare shi da Diya su ka saki wani dan karamin murmushin gefen fuska Malik ya na furta Alhamdoulilah cikin zuciyarsa sai da ta karaso tsakiyar parlourn sannan ta ce " Malik , Baby , ina son gabatar muku da sirikarku , Aleesherh " a