Sashe 34
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
maganarta sannan ya daga mata gera guda ya na fadin " kin iya sarrafa kalaman ki , amma ba za su isa ba dan mallakar Zuciyar Prince Nayel Nawfel Hicham bin Jaabar " wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " na sani , zuciyarka ta fi dutsen diamond tsada mallakar ba zai zama karamin abu ba , amma na shirya yaki da dukkan makamaina dan mallakar ta , in har za a ba ni dama " gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya sunkuya ya dauki wayarsa ya mike tsaye ya nufi parlour ya konta ya saman sofa ya ci gaba da aikinsa wani cool murmushi ta saki kafin ta ida Hayewa gadon ta konta dan gaskiya barci ta ke ji , ba jimawa ko barci ya yi gaba da ita haka shi ma WASHE GARI misalin karfe 8 su ka shirya za su bar garin , amma Aleenah ko da ga cikin bedroom din ta ba ta fito ba ko rakiya , ta na a haka Aleesherh ta shigo ta fada mata tare za su tafi kuma Al-Sayid ya amince , ba karamin farinciki ta yi ba dan har kukan farinciki ta yi shikenan ba abun da zai raba ta da yar uwarta Al-Sayid ya so ya raka su har airport amma Prince ya matsa ba sai ya biyo su ba , ba dan ya so ba ya hakura ya zauna a nan Daular , su kuma su ka shiga motocin Junior da ta Prince su ka nufi Airport ko wane zuciyarsa duk ba dadi sun rabu da familyn su ita kanta Sayida Ahlame sai da ta yi kuka amma ko ba komai ta na farinciki yarinyarta za ta tafi tare da mijinta sai da su ka yi nisa da Daular sannan Prince ya kira Inaya kamar dama jira ta ke , ko ringing biyu kiran bai yi ba ta dauka ta na fadin " Babyna , wai har yanzu ba ku iso ba ? " " No , kuma ni ba yanzu zan dawo ba , may be sai gobe " ya fada cikin nitsuwa ita dai Aleesherh ta na zaune gefensa ta na jin abun da ya ke fada cikin rudu Inaya ta ce mishi " kamar ya sai gobe , matar taka fa ? kai ma ka san mahaifinka ba zai ji dadin hakan ba ko ? " " please my Cutie , wai ya ku ke so na yi da rayuwata ? kun matsa sai na yi auren nan yanzu na yi , at least kun bari na kammala aikina ko ? ba guduwa zan yi ba " Aleesherh na jin ya ce my Cutie ta dago kai ta na kallon shi , kenan last time da ta je tashe shi ba ita ba ya kira da Cutie ? to wacece Cutie ? ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryarsa ya na fadin " please Cutie , ki yi mishi magana , i promise karfe 10 na yi ina cikin masarautar , it's very important for me please " " shikenan na ji , amma ka na dawowa zan kai ma ka matarka part din ka gaskiya " Inaya ta fada sai da ya ja tsaki sannan ya ce " shikenan , na ji , that's why i love you so much my Cutie " wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " hum na ji Sarkin dadin baki , Allah ya kiyaye hanya " da Ameen ya amsa mata kafin ya sauko wayar ya katse kiran ya na sauko wayar ko Aleesherh ta ce mishi " wacece Cutie ? " sai da ya juyo ya kare mata kallo da kyau kafin ya juya ya ci gaba da latsa wayarsa sannan ya ce " she is my first love " dam ta ji gabanta ya buga har zaro idanu ta ke ta na kallon shi , nan take idanunta su ka ciko da ruwa , hakan na nufin kenan ya na da aure , ita ce ta biyu a hankali ta meda kanta ta sunkuyar , murya a disashe ta ce " your first love ? it means she is your first wife ? i'm the second ? " maganarta har ta so ta ba shi dariya kenan da gaske kishi ne ya gani a idanunta , ya so ya fada mata gaskiyar wacece Cutie kai tsaye amma wata zuciyar kawai ta ce mishi ya yi hakan ya ji abun da za ta ce sai da su ka iso airport bai ce mata komai ba , ita kuwa sai ruwan hawaye ta ke yi kanta na sunkuye ya na jin motarsu ta tsaya ya ce " No , you're my first & Only wife , Cutie is my first love , my mother , idan kin je ita za ta tarbe ki " ya na gama fadar haka ya bude kofar motar ya sauko sannan ya zagayo ya bude mata kofar da kansa ya mika mata hannu sai a lokacin da sa hannu ta goge hawayen face din ta , ta mika mishi hannu ta sauko da ga saman motar a hankali ta yi mamakin ganin su a parking space ba kai tsaye ba cikin airport din , ta ga bodyguards din sa sai fiddo kayansu su ke yi su na shiga da su cikin airport din cikin airport din ya nufa , Junior da Aleenah na biye da bayansu sai da su ka iso reception sannan ya saki hannunta ya na fadin " tare da shi za ku tafi , ni sai gobe zan zo , akwai aikin da zan yi a nan " ya fada mata murya kassa kassa kafin ya juya ya kalli Junior ya ce " karfe 10 ka je dauka ni a airport , ba zan wuce 10 ba " da to kawai Junior ya amsa mishi kafin su rungume juna na dan lokaci sannan ya sake shi , ya nufi kofar fita ya yi tafiyarsa da kallo ya rakata har sai da ya fita , ba ta da labari sai jan hannunta Aleenah ta ke yi su tafi sai da ya fita sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta bi Aleenah da Junior , cikin Private Jet din sa su ka shiga , ko 30 minutes ba su yi ba ya daga ya nufi Saudiya kamar ta fashe ta ke ji , ita har yanzu amsar da ya ba ta a kan Cutie ba ta gamsar da ita ba , me ya ke nufi , ita ta kassa gane mishi Bari mu leko Saudiya kafin Jet din su ya sauka MASARAUTAR SAUDIYA INAYA zaune ta ke cikin parlourn MALIKAT INAS da RIANNA da Nesrine da MALIKAT INAS wannan har da Tesnim , tun shigowa ta masarautar sai yanzu na hadu da ita , kullum mu na samun sabani ni da ita , amma yau na yi nassara ta na nan Inaya baki ya ki rufuwa sai murna ta ke yau babynta ya yi aure saura babyn Malik , yanzu dai Sun tafi shopping ita da Azmat da Pretty na manta ban fada muku ba , Pretty ita ke auren Sakin masarautar Ottoman wato nephew din Diya , yaron yayansa na biyu me bin Aymane , Ghalib Hishmat Bin Abdoul Mujeeb , sannan Abdoul da Tesnim sun sake samun baby boy wanda ya sakawa sunan malam wato Ibrahim , yanzu 20 years ne da shi kuma ya na karatu a Seoul ( Korea ) bayan sun gama waya da Prince ta ce wa MALIKAT INAS " Ammie wai ya ce shi sai cikin dare zai zuwa , akwai aikin da ya tsaya yi " " to matarsa fa ? , kin san dai ba za ta iya tare wa a part din sa ba ita kadai , in wani abu ya same ta ? " MALIKAT INAS ta tambaye ta Nesrine ce ta amsa mata da cewa " ta zauna a nan mana har zuwa lokacin da zai zo , ko ya Ammie ? " " shikenan , amma part din su ya na gyare ko sai an gyara ? " wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " No kar ku damu , ya na gyare , Malik kuma ya shirya mishi surprise a ciki " " surprise ? wace irin surprise ? " Tesnim da RIANNA su ka fada a tare yanzu ma sai da ta yi dariya kafin ta ce " ni dai bai fada min wace irin surprise ce , Ammie bari na je na dawo kafin Jet din su ya sauka " ta fada ta na mikewa tsaye da to kawai MALIKAT INAS ta amsa mata kafin su ci gaba da hirarsu cike da annashuwa Faaz ya na konce gefen RIANNA ya na sauraron hirarsu sai da Inaya ta fita sannan ya mike ya na fadin " Momy barci na ke ji " ya fada a sanyaye da murmushi a face din ta ta ce " shikenan , tafi ka konta " gyada mata kai kawai ya yi kafin ya tashi ya shiga corridor , su kuma su ka ci gaba da hirarsu bayan ya shiga bedroom din sa , ya meda kofar ya sa security sannan ya dawo tsakiyar dakin , ya zube saman guyiwowinshi , ya lumshe idanu ya fara wani karatu mara dadin ji a hankali Lamps din dakin su ka fara mutuwa su na kunnuwa da alamun Queen ce ya ke kira ya yi wajen one minute a haka kafin lamps din su mutu baki daya , ya ware idanunsa a hankali sannan ya mike tsaye ya nufi mirror ya na isa ko inuwar Queen ta bayyana a kai a dan sunkuyar da kai ya yi ya na fadin " ina mika sakon gaisuwata ga shugabata " da wannan Muryarta mara dadin ji ta ce " me ya faru ? " dago kai ya yi a hankali ya ce " Momy , Prince ya yi aure , ni ma yanzu na ji RIANNA da MALIKAT INAS su na maganar , ba ki ganin Aurensa zai iya janyo mana matsala ? " " matsala guda zai janyo mana shi ne ya samu baby kafin Big bro din ku ya