Sashe 15
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
THE BIGINING TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ [ FREE PAGE ___ 6 Dum ta ji zuciyarta ta buga a dubu dari ta mike tsaye ta na fadin " Daddy , aure ? why ? ni gaskiya ba na so " cikin nitsuwa Al-Sayid ya ce mata " koma ki zauna ! " ya fada cike da isa sam ba wassa a tare da shi ba dan ta so ba ta koma ta zauna ta na sunkuyar da kai " Aleenah , Aleesherh , ba shawara na ke ba ku ba , umarni ne , na riga da na turawa Malik Letter dangane da maganar , dan haka ku jira amsar sa sati me zuwa ki fara shirye shirye " nan take Aleesherh ta saki kuka ta na fadin " amma Daddy me ya sa za ku yi mana haka ? ni ban shirya aure ba gaskiya , kuma kuma.......... " katse ta Sayida Ahlame ta yi da fadin " kuma me ? Aleesherh na lura ke sam ba ki jin magana , ki na neman ki fi karfin mu , dubi Aleenah ko kalma daya ba ta ce ba , kenan ke ki ke da bakin magana ? gwara ki tafi gidan mijinki ko shi zai iya gyara miki zama " kuka Aleesherh ta saki ta na fadin " amma Daddy akwai wanda na ke so , akwai wanda mu ke soyayya da shi , don Allah Daddy ka janye maganar nan , wlh ba zan iya rayuwar aure in ba da shi ba " da alamun ta manta gaban wa take dan duk abun da ke cikin zuciyarta kawai ta ke fada kallon juna Al-Sayid da Sayida Ahlame su ka yi kafin su juya su kalli Aleesherh cike da rudu " ina ya ke shi wanda ku ke soyayyar , ya sunansa ? a ina kuma ya ke ? " Al-Sayid ya jero mata tambayoyin wasu yawu ta hadiye kafin ta kai hannu ta fara goge hawayenta , karyar da ta yi ta na neman ta juye mata , to ita ina ta san sunansa , bare wajen da ya ke zaune har in da ya ke aiki ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryarsa ya na sake tambayar ta wasu wahalalun yawu ta hadiye kafin ta ce " um Daddy , yanzu ba ya cikin masarautar , ya tafi UK wajen aikinsa , kuma bai fada min yaushe zai dawo ba " " okay , ki fada mishi ina son ganin sa , in kuma Magajin Malik ya riga shi zuwa sai dai ku yi hakuri da ke da shi dukka ku " da sauri ta gyada mishi kai ta na sakin wani dan karamin murmushi ta saki " Eh Daddy zai zo " gyada mata kai ya yi kafin ya ce " shikenan , Aleenah , ke kuma fa ? akwai wanda ki ke so ko babu ? " ya tambayi Aleenah ya na kallon ta girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " a'a Daddy babu " ta fada murya cen kassan makoshi " okay , za ku iya tafiya , sai da safe " " Sai da safe Daddy " su ka fada a tare kafin su yi musu sallama su ka tashi su ka koma part din su kai tsaye part din su su ka koma sai sauri Aleesherh ta ke kamar za ta tashi sama ko da su ka shiga part din su ta riko hannayan Aleenah ta na fadin " please Aleen , ki fada min a wane hotel ne ya ke zaune , wlh in ban samo shi ba Daddy auren dole zai yi min , ni kuma wlh ina son sa har cikin raina " ta fada kamar za ta yi kuka har ruwa ke cikowa cikin idanunta kwace hannayanta Aleenah ta yi , cikin sanyin murya ta ce " ko na fada miki ba abun da zai anfane ki da shi , saboda ba son ki ya ke ba , ta ya ma za ki kawo shi gaban Daddy matsayin wanda ku ke soyayya ? ki na tunanin zai amince ? a ka je kuma akwai wadda ya ke so ? " " ni dai don Allah ki fada min , ni na san yadda zan yi , kenan kin fi son ya aura min wani cen wanda ban sani ba ko son sa ba na yi ? " " kin dai ji fa ni da ke ya ce , ba ke kadai ba ya ce " " na sani amma ai ke ba wanda ki ke so , kuma ai Malik yaro guda ne da shi , please ki ceci rayuwar yar uwarki guda , wlh in a ka yi auren nan kashe kai na zan yi " ta fada murya a sanyaye kamar za ta yi kuka ta na marairaice fuska shiru Aleenah ta yi ba ta ce mata komai ba , ta san tabbas Malik yaro guda ne da shi , kuma dole Al-Sayid babbar cikin su zai fara ba shi , in har Aleesherh ta samu abun da ta ke so to tabbas ita za a bawa yaron Malik , yanzu zaba za ta yi tsakanin rayuwarta da ta Aleesherh , tun da har ta ce sai ta kashe kanta in har a ka yi auren nan to tabbas sai ta kashe kanta dan ta san yar uwarta da cika magana wani dogon nunfashi ta ja kafin ta ce " a Sheba hotel ya ke , floor na farko , VIP room 3 " wani kyawatacen murmushi Aleesherh ta saki kafin ta rungume ta tsam ta na fadin " na gode sosai my lovely sister , that's why i love you so muchhhhh " wani dan karamin murmushi Aleenah ta yi kafin ta rungume ta sun dan dauki lokaci a haka kafin Aleesherh ta sake ta ta juya da sauri ta na fadin " ina uniform din ki ya ke ? " dan zaro idanu Aleenah ta yi kafin ta riko hannunta ta na fadin " ke Aleesh , da hankalinki kuwa ? cikin wannan daren ki ke son tafiya ? in a ka kama ki fa ? please ki bari har zuwa safe " " Aleenah ba zan jima ba , please ki kyale ni na tafi , wlh rayuwata ce ke cikin hatsari in har ban je ba " wani dan karamin tsaki Aleenah ta ja kafin ta saki hannunta ta nufi hanyar dressing room jim kadan ta fito rike da uniform din ta irin na ma su aikin Sheba hotel ta mikawa Aleenah ta na fadin " rike , amma wlh duk abun da ya same ki ba hannun Aleenah a ciki " ta fada ta na komawa bakin gadon ta zauna ta na nade hannayanta a kirji ta kauda kai wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi kafin ta karaso gefenta ta zauna , ta na fadin " ba abun da zai same ni saboda kyakyawar Twins di ta ta na nan , ke za ki taimaka min na fita ba tare da kowa ya sani ba , yanzu in an tambaye ni ki ce ina barci , in ban dawo ba nan da one hour ki je nema na , byeeeeee " ta fada ta na mikewa da gudu ta shiga dressing room da kallo Aleenah ta raka ta har sai da ta shiga sannan ta ce " Aleesherh sai kin sa an kashe ni wata rana , wajen neman soyayyarki yanzu za ki saka rayuwata cikin hatsari " ta na gama fadar haka ta saki wani cool murmushi ta ce " Allah ya sa ni ma na samu wanda zan iya jefa rayuwata cikin hatsari dan kwatar soyayyarsa , kyakyawa mai kyakyawar zuciya " ta na zaune a nan ita kadai har Aleesherh ta fito sanye da uniform din , kuma gaskiya sun yi mugun zauna mata fiye da Aleenah dan ta fi Aleenah cika da shape abun dai Masha Allah bare da ta saki curly hair din ta har tsakiyar baya gaskiya ba karamin kyau ta yi ba a haka har ta karaso gefen Aleenah ta manna mata kiss saman kumatu ta na fadin " sai na dawo " ta na gama fadar haka ta nufi wani closet na books da ke cikin parlourn ta na isa ta sa duk karfinta ta tura closet din nan na ga wata yar karamar door a baya bude door din ta yi ta shiga , duk da wajen duhu ne amma sam ba ta ji tsoro ba dan sun saba bi ta nan SHEBA HOTEL VIP ROOM 3 konce ya ke tsakiyar gadonsa , da Laptop saman laps din sa ya na faman latsawa da ga shi sai short da t-shirt blue color , ya saki wannan smooth hair din nashi ya bazun mishi a shoulder sai tashin qamshi ya ke ya na zaune a haka ya ji wayar landline din dakin ta fara ringing hannu ya kai ya dauki wayar ya kai ta a kunne ba tare da ya ce komai ba cikin nitsuwa ya nijo Muryar wani matashin ya na fadin " Sir , ga fruits din nan an kawo muku , za ku iya bude mata kofa ? " " okay," ya fada a takaice kafin ya mayar da wayar , ya sauke laptop din da ga saman cinyoyinsa ya sauko kassa ya nufi kofar hannu ya kai ya bude kofar sannan ya juya ya na fadin " za ki iya ajiyewa saman table " ya fada ya na nufar toilet ba musu ta karaso cikin dakin ta na sallama da wata siririyar Muryarta cak ya tsaya dan ko cikin duhu zai iya gane wannan Muryar a rude ya juyo ya na zaro idanu ya na kallon ta tsaye tsakiyar dakin rike da tray din fruits " what are you doing here ? ! " ya fada da dan karfi har sai da ta saki tray din hannunta dan ba karamar razana ta yi ba , ga shi dama ba wani kayan kirki ne a jikinsa wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " please Get out ! " wasu yawu ma su daci ta hadiye kafin ta bude