← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 61

Sashe 51

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka ke yi min ? " " No , ba wassa na ke ba , please ki daina kallon abun wani iri , na ga ai akwai aure tsakanin mu , kuma ni ina son ki , I love you more than you think , please ki yarda ki aure ni " iska ta furza da ga bakinta kafin ta mike tsaye ta na shirin barin wajen dan ita a ganinta ta yi wa Junior tsufa gaskiya , ba ta taba tunanin zai bude baki ya yi mata irin wannan tambayar ba watarana ba ta yi taku biyu ba ya riko hannunta ya tsayar da ita da cewa " please kar ki tafi ba ki ba ni amsa ba " juyowa ta yi a hankali ta kwace hannunta ta ce " me ka ke so na ce maka ? ta ya za ka min irin wannan maganar ? kuma ni gaskiya ba zan iya auren ka ba , na yi maka tsufa " " and so what ? na ga ba laifi ba ne dan ka auri wadda ta girme ka ba , kuma na ga shekarun mu guda , asali ma na ba ki wata hudu , kuma kar ki manta , Annabi Muhammad ( S.A.W ) matarsa ta farko ta girme shi , why mu ma ba za mu yi koyi da shi ba ? please accept to marry me " kauda kai gefe ta yi ta furza iska da ga bakinta , ba ta ma san abun da za ta ce mishi ba , da ga gani tsakani da Allah ya ke yi mata maganar nan riko hannayanta dukka biyu ya yi , ya matso kusa da ita , a sanyaye ya ce mata " Princess , you don't love me ? " " I love you , but like my brother " ta fada ta na dawo da kallonta gare shi " it's not a problem , tun da har ki na so na a matsayin dan uwanki , cikin sauki son zai juya ya koma soyayya ni ma dan haka na fara , ko ba ki jin dadin zama da ni ? akwai wani abu da na ke da ba ki so ? na yi miki alkawari ko ma minene zan gyara kawai ki amince " " Junior , ko ni na yarda ka na ganin Daddy zai yarda da auren mu ? na sani ba za su taba yarda " " Daddy da Uncle duk sun yarda , kuma kafin na fara yi miki maganar nan sai da na yi musu ita kuma sun amince , kawai ba su fada miki ba ne saboda su ba ni dama na shawo kanki da kaina " shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba na dan lokaci kafin ta ce " yanzu me ka ke so na ce ? " " kin yarda za ki aure ni " ya fada ya na sakin murmushi murmushi mai dan sauti ta saki kafin ta ce mishi " amma ai ka san ba haka a ke neman mace aure ba ko ? " cikin rudu ya ce " kamar ya ? " " ka yi kneel down mana " wata yar karamar dariya ya yi kafin ya saki hannayanta ya zube saman guyiwowinsa , ya mika mata hannu ya na fadin " ki yi hakuri ban sayo ring ba , but i promise gobe ina sayo miki , Nailah , za ki aure ni ? " nade hannayanta a kirji ta yi ta na sakin murmushi ta kauda kai gefe " pleaseeeee my Princess " ya fada ya na marairaice mata fuska ya na gama rufe bakinsa ya jiyo Muryarta ta na fadin " Faaz ? " " Faaz ? " ya maimaita sunan shi ma kafin ya ce mata " me ya faru Baby ? " da sauri ta ce mishi " Junior , look , Faaz ne ya ke kokarin fita masarautar " ta fada ta na nuna mishi Faaz da ke ta biyar bango ya nufi hanyar fita masarautar a hankali ya mike tsaye shi ma ya na kallon shi riko hannunshi ta yi ta na fadin " mu bi bayansa " " what ? no ki nari har ya dawo mu tambaye shi ina ya je , ba ki ga dare ya yi ba ? " " please ba abun da ya faru , don Allah mu bi bayansa " ta fada ta na jan sa ba yadda ya iya ya bi bayanta su ka bi bayan Faaz dan ya na tsoron ya bar ta haka wani abu ya same ta duk abun da ya faru Malik na tsaye ya na kallon su cikin part din sa , ba karamin sanyi ba ya ji cikin zuciyarsa ganin su haka musaman lokacin da Junior ya zube saman guyiwowinsa , kawai ya tsaya ya na jiran ta daura hannunta saman nashi , amma sai ya ga ta ja shi su ka bar wajen , bai kawo komai a ransa ba dan a tunaninsa wani abu ne su ka gani bangaran su kuwa , cikin sand'a su ke biye da bayan Faaz , duk da akwai mutane cikin masarautar dan lokacin bai wuce karfe 10 na dare ba haka su ka fara bin bayansa ya na tafiya in ya gaji ya yi gudu , ya na tsalle kamar ya na wassa sai rokonta Junior ya ke su koma amma ba ta jin sa , ba abun da ta ke so kamar ta ga ta kama Faaz , tun lokacin da ta sauke ido saman shi ta ji bai konta mata ba , in har wani abu ya ke shirya musu ya kamata ta sani sai da su ka yi wajen 30 minutes su na biye da bayansa , kafin su ga ya sha wata kwana da sauri Ta janyo Junior su ka yi kwanar amma kawai sai ta ga mutum ya bace , babu shi sama da kassa , ga shi kuma hanyar doguwa ce babu kwana dan ita ce hanyar da za ta kai Prison din masarautar cikin rudu ta ce " Ina kuma ya shiga ? " riko hannunta Junior ya yi da karfi ya janyo ta su ka bar wajen ya na fadin " ya isa haka , mu koma gida yanzu " " Junior please , a ka je wani mugun abu ya ke shirya mana kuma fa ? " ko sauraron ta bai yi ba ya ci gaba da jan ta har su ka dawo kan titi nan ya tsayar musu da wani mai mota dan ya meda su Daular , cikin sa'a ko ya amince dan sarai ya gane su , ya meda su har cikin Daular , sannan su ka sauka Junior na yi mishi godiya Princess kuma ta na saukowa ta nufi part din MALIKAT INAS da gudu da Sauri Junior ya bi bayanta ya na kiran sunanta amma ta ki jiransa babu ko sallama ta fado parlourn kamar an tillo ta da ga sama nan ta tardo Rianna da Aleenah zaune a parlourn da alamun hira su ke kamar wata zarrara ta ke fadin " momy ina Faaz ya ke ? " cikin rudu Rianna ta ce mata " Faaz kuma ? ya na barci , me ya faru ? " " no momy , Faaz ba ya cikin Daular nan , mu na zaune a garden na gan shi ya fita , na bi bayansa amma ya bace min , momy sai da na ce miki zuciyata ba ta konta da yaron nan ba , amma kin ki yarda , in ba munafikanci ba me zai fitar da shi Daular a wannan lokacin ? ina kuma ya je ? " ta na gama rufe bakinta Junior ya shigo Parlourn ya na kiran sunanta a dai-dai lokacin ko Faaz ya fito da ga cikin corridor sanye da kayan barcinsa , ya na murza ido da hannunsa guda , cike da shagwaba ya ke fadin " momy , na kassa yin barci " Dam Princess ta ji zuciyarta ta buga , ta na kallon shi ta na zaro idanu kafin ta juya ta kalli Junior da ke tsaye gefenta Rianna kuma kare mata kallo da kyau ta yi kafin ta ce " me ya sa ki ke haka ? ga shi nan to , in shi ba ki yarda da shi ba ni kin yarda da ni , tun da na ce miki ya na barci , ga shi yanzu kin tashe shi " girgiza kai ta shiga yi ta na fadin " no , no , no , Momy , ki yarda da ni , wlh na gan shi da idona , Junior , ka fada mata , ba tare mu ka bi bayansa ba ? " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya riko hannunta ya na fadin " ya isa haka Baby , m u tafi " ya fada ya na juyawa ya na janye da ita sai ce mishi ta ke ya ke sake ta amma ya ki sauraron ta su na fita na ji Faaz ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya , ya nufi Rianna ya rungume ta ya lumshe idanunsa kamar mai jin barci bangaran Junior kuwa , kai tsaye part din Diya ya nufa da ita a bangaransa , in ba ku manta ba dama part biyu a wajen , to Junior shi ya shiga gudan sai da su ka shigo parlourn sannan ta kwace hannunta da karfi ta na ce mishi " me ya sa za ka janyo ni ? na ga a gabanka ya fita , tare mu ka bi bayansa , ta ya za a ce ka riga mu dawowa ? " hannayansa dukka biyu ya daura saman face din ta cikin sanyin murya ya ce " baby , please calm down , may be gizo ne kawai ki ka gani " " gizo ? kenan kai ma gizo ne ka ga ni dan tare mu ka gan shi , please in kowa bai yarda da ni ba , at least kai ka iya sauraron abun da na ke fada , wlh yaron nan da mumunar manufa ya shigo Daular nan , ban san me ya ke shirin
Chapter 51 · 0% Book details