← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 61

Sashe 11

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya kalli saitin hagunsa ta cikin Window din wani ginin nan ya gan ta tsaye rike da sword ta na sanye da wasu fararen Tracksuit , ta daure gashin kanta a baya , sai wassan takobi su ke yi da wani dogarin da ga gani ta kware tsayawa ya yi ya zuba mata ido ya na son tantance wani abu ya yi wajen two minutes tsaye a haka kafin ya ga sun tsaya sai haki ta ke ta na sakin murmushi a hankali ta juya dai-dai lokacin da ya ga ta biyun ta karaso wajen su na fuskantar juna tak wadda ya gani a libraryn cikin gari , har kayanta kenan in ya gane Twins ne ? shi ya sa su ke kasancewa waje daban daban lokaci guda wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ci gaba da tafiyarsa har su ka iso libraryn da ga nan dogarin ya juya ya kyale shi ya nemi abun da ya ke zo nema U.S.A ( WASHINGTON DC ) Yau Garin tun bayan sallar asubahi a ka fara ruwan sama cen zuwa yamma kuma ya koma snow , Malik Gaskiya ya so ya tafi Saudiya a yau amma a Airport sun kira sun ce jirgi ba zai iya tashi ba a irin wannan lokacin sai dai ya bari har gobe ba dan ya so ba ya hakura washe gari kuma a yin sallar Asubahi su ka nufi airport shi da Inaya da Princess su na isa ko Jirginsu ya daga ya nufi Saudiya MASARAUTAR SAUDIYA DAULAR SAUDIYA MALIKAT NESRINE A hankali ta ke takowa ta na rike da tray cike da fruits , duk yanayin ta a sanyaye kamar ba ta jin jikinta a haka har ta karaso cikin parlourn part din su ta na sallama kassa kassa a hankali Diya ya dago kai ya na amsa mata sallamar ta ya na zaune saman sofa ya na sanye da kayan barci , duk ya rame har wani dan duhu ya yi da ga gani ciwo ya ke tsantsar shi a haka har ta karaso gefensa ta zauna ta na fadin " bude baki na ba ka ! " ta fada ta na dauko barin apple guda ta kai mishi a baki murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce mata " na ji ciwo na ke amma ai ni ba baby na ne , zan ci da kaina " sannan ya kai hannu ya karbi apple din ya kai a baki ya ci abu ne dan sunkuyar da kai ta yi kafin ta dauki tray din ta ajiye mishi saman cinyoyinsa sannan ta mike za ta bar wajen da sauri ya riko hannunta ya na fadin " Nesi , wai me ya faru ne ? kwana biyun nan na ga duk yanayinki ya yi sanyi ko magana na yi miki ba ki ba ni amsa kamar a baya , ko wani laifi na yi miki ? " girgiza mishi kai ta yi a hankali ta na fadin " ba komai , kawai barci na ke ji " a hankali ya sa hannu ya janye tray din saman laps din sa , ya ajiye gefe , sannan ya dafe forehead din sofar , ya fara kokarin tashi a hankali ta na jin ya fara jan hannunta da karfi ta yi sauri ta juyo , ta taimaka mishi ya mike tsaye ta na yi mishi sannu mikewa tsaye ya yi ya riko kugunta a hankali ya janyo ta jikinsa , cikin sanyin murya ya ce mata " haba Sarauniyar zuciyata , haba uwar y'ay'a na , ke ki na tunanin za ki iya boye min damuwarki ? please fada min , me ke damun babyna ? ko sai na yi miki kuka ? " ya qarashe maganar ya na marairaice fuska murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta rungume shi , ta kontar da kanta saman chest din sa cikin sanyin murya ta ce mishi " kawai har yanzu ina tunanin halin da ka ke ciki ne , ba dan ikon Allah ba da yanzu shikenan na rasa ka har abada , ba zan iya rayuwa babu kai ba , don Allah ko tafiya ka ke son yi ka bari na riga ka , yadda ba zan ji zafin rashin ka ? " " ni kuma na ji zafin rashin ki ko ? ki daina jin tsoro , in sha Allah ba abun da zai raba ni da ke , mu na tare har abada " gyada mishi kai kawai ta yi kafin ta matse shi tsam a jikinta wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " ki na tune haduwar mu ta farko ? " " please wai me ya sa sai ka min wannan maganar kullum ? ya riga da ya wuce , ni ka daina ba na so " ta fada cike shagwaba ta na turo dan bakin nan nata wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce mata " to ai ranar ce na kassa mantawa , har yanzu ganin nake kamar jiya ne haduwarmu ta farko , ina tune lokacin kin sauko da ga school , ki na tafe ki na faman turo baki , da ga gani yunwa ce ki ke ji , a ranar na dawo da ga Abuja cikin mota , kawai na tsaya na ce miki ki shigo na rage miki hanya , amma ina , madam na bude baki ta balbale ni da fada , kai kuma malam da ga ina ? dan yankan kai ne ko ? da wasu idaninka kamar na mujiya , to wlh babu inda zan je da kai , kuma wlh in ka sake ka biyo ni sai na fadawa yayana ya yi maka dan banza duka , mai kanta kai kawai " ya fada ya na kwaikwayon Muryarta dariya sosai ta yi ta na bugun shi a kirji a hankali haka shi ma dariya kawai ya ke dan har ga Allah ba zai taba manta wannan ranar ba , ranar da ya kamu da son ta , ita ba ta san wannan tsiwar da ta yi mishi ne ya sa ya kamu da son ta a lokaci guda , ga shi yanzu tsawan shekaru 30 da yin aurensu har da yaransu biyu sai da ta gama dariyarta sannan ta dago kai ta ce mishi " na ji shikenan , yanzu mu je ka konta ka sha maganinka , ka huta " " baby , duk fa karfe 1 na rana , haba ku na neman ku saka ni a prison , duba fa har fada kun hana ni zuwa , at least ku bar ni na sarara " " please baby , mu shiga da ga ciki magana , zan yi maka tausa in mu ka je " ta fada mishi cike da shagwaba ta na kashe mishi ido wata yar karamar dariya ya yi , ya na shirin magana ya jiyo Muryar Malik kamar an koro shi ya na fadin " Diya , where are you ? " a tare shi da Nesrine su ka juya su na kallon kofar shigowa parlourn dai'dai lokacin da Malik ya shigo shi da Inaya wata yar karamar kara Nesrine ta yi kafin ta saki Diya ta nufi Inaya da gudu ta rungume ta ta na sakin kuka haka shi ma Malik da sauri ya nufi Diya ya rungume shi a tare su ka sauke wata nanauyar ajiyar zuciya , duk da su na ganin juna ko wacce shekara kuma su na waya amma a yanzu ji su ke yi kamar sun yi shekaru dubu ba su ga juna ba sai da su ka gaji da rungumar sannan Malik ya dago da ga jikin Diya , ya daura hannayansa biyu saman face din sa , a rude ya ke fadin " Ya jikinka ? How ? ta ya haka ta faru ? kuma a ce ba za ka iya kira na ka fada min ba ? yanzu da wani abu ya same ka fa ? shikenan na rasa dan uwana tilo da na ke da shi ? me ya sa za ka min haka ? at least da sai ka kira ni ka fada min tun kafin abun ya tsananta , amma sai da ka gama samun lafiya za a sanar da ni , ko ka na tunanin ba ka da mahimanci ba ne a waje na ? haba Diya ? " " za ka yi shiru ko sai ka saka ni kuka ? " Diya ya fada cikin sanyin murya idanunsa na cikowa da hawaye da sauri Malik ya kara rungume shi ya matse shi tsam , a kunne ya ke ce mishi " I'm sorry , na so na kasance a tare da kai lokacin da ka fi bukata ta , i'm so sorry , I promise ba zan sake rabuwa da kai ba , ko da kuwa mutuwa ce ta zo shiga tsakanina da kai ba zan bari ta raba ni da kai ba , i'm back my bro , i'm back " wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya rungume shi tsam , kamar zai yi kuka kar ku tambaye ni ina su Inaya , tun lokacin da Nesrine ta rungume ta ba su saki juna ba sai kuka su ke yi kamar za su hadiye juna , musaman Nesrine dan sai da Inaya ta dinga rarrashin ta kamar wata baby a hankali Diya ya raba jikinsa da na Malik ya na fadin " now je ka huta , na san kun gaji , zuwa yamma na tarda ka " " no , mu je na raka ka ka konta kafin nan " Malik ya fada ya na riko hannunsa , ya fara jan sa a hankali su ka nufi corridor " zan iya tafiya da kaina , ka tafi kawai " ko sannu Malik bai ce mishi ba su ka ci gaba da takawa har ya kai shi bedroom din shi , ya kontar da shi saman gadonsa , ya rufe shi da duvet sannan ya juya ya fito ________________
Chapter 11 · 0% Book details