← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 61

Sashe 25

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

THE BIGINING ( TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK _______________________________________________ PAID BOOK N500 [ FREE PAGE ___ 10 da to kawai Aleesherh ta amsa mata , da ga haka Sayida Ahlame ta sa kafa ta fice part din ta na fita Aleesherh ta mike ta shiga toilet ta zauna bakin bath din ta na kuka kassa kassa ita dai Aleenah ba ta ma san duniyar da ke faruwa ba sai barcinta ta ke cikin konciyar hankali har da wani dan karamin murmushi a face din ta bari na koma Saudiya kafin su kammala to MASARAUTAR SAUDIYA MALIK zaune ya ke cikin parlourn part din sa a floor na uku , Prince da Junior su na zaune su ma kowane ya na rike da wayarsa sai saman latsawa ya ke cikin nitsuwa Malik ya fara magana ya na fadin " Prince , ina fatan Junior ya fada maka sakon da ya iso mana da ga Daular Yemen ? " ya fadi hakan dan a lokacin da letter din ta iso gare shi Junior ya na wajen nan take yanayin face din Prince ta ida sauyawa duk da ba wani murmushi ne a kai ba , kamar zai yi kuka ya ce " Daddy i'm sorry in hukuncin tafiyar da na yi ne ka yi hakuri ba zan sake tafiya ba , amma gaskiya ban shirya yin aure ba " " okay , ka ba ni hujja uku da za ta hana ka yin aure a yanzu , in har sun gamsar da ni to zan janye maganar auren " Malik ya fada cikin tsare gida ya na matse gera alamun ba wassa wani dan karamin tsaki Prince ya ja ya na kauda kai , shi gaskiya ba ya son auren nan specially ma da ya ji wacece a ka ce zai aura ya na a haka ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " Nayel , da kai na ke magana , ka ba ni hujjojin na ce " murya cen kassan makoshi ya ce " babu " da kyair ma sautin ya fito , tun da ya ji Malik ya kira sunan shi kai tsaye to duk abun da zai ce ba zai iya kare kansa ba , maganar auren ta zauna kenan ba mai kwatar sa sai Cutie , ita kadai za ta iya shayo kan Malik ya janye maganar auren nan shi ko bai san Cutien da ya ke cewa ita ta kawo shawarar auren ma wani dan karamin murmushin gefen fuska Malik ya saki kafin ya ce " okay , ku shirya gobe za ku tafi Yemen kai da Junior , nan da one week za a yi auren kuma za a yi shi ne bisa tsarin al'adun masarautar Yemen " da sauri Junior ya ce " Uncle ina da magana please " " wace magana ? " Malik ya fada ya na tsare shi da ido sunkuyar da kai ya yi ya na fadin " umm Uncle , ni dai ba zan iya karbar auren nan ba , saboda akwai wadda na ke so " dan tabe baki Malik ya yi ya na kallon shi ya ce " really ? wacece ? zan je da kaina neman maka aurenta sai a yi auren rana guda da na Prince " sunkuyar da kai Junior ya yi ya fara wasu dan kame kame ya kassa fadawa Malik Abun da ke cikin zuciyarsa , ya na jin kunyarsa gaskiya su na a haka Inaya ta shigo cikin parlourn ta na sallama da murmushi a face din ta kai tsaye ta nufi gefen Malik ta zauna ta na fadin " hirar me ku ke yi haka ? " Malik ne ya ba ta amsa da cewa " hirar auren yaranki , Junior ya ce akwai wadda ya ke so ba zai karbi kyautar Al-Sayid ba " " Masha Allah , Junior ka fada mana wacece sai mu fara shirye shiryen auren a yi shi tare da na Prince " ta fada ta na kallon Junior Prince kuwa ya na jin ta kira sunansa ya dago kai a dubu dari ya na kallon ta kenan ta na sane da maganar auren ya , ke tambayar kansa shi dai Junior sai sosa bayan keya ya ke da hannu ya kassa fadin maganarsa kamar an rufe mishi baki ya ke ji wani dogon tsaki Prince ya ja kafin ya ce " Cutie , Princess ce ya ke so " a tare duk su ka juya su ka kalli Prince har shi kansa Junior pillow ya dauka ya kai mishi bugu a baya ya na fadin " me a ba ka gane ba cikin sirri ? " " wait ! Junior da gaske Princess ka ke so ? " Malik ya jefo mishi tambayar wasu yawu Junior ya hadiye kafin ya ce " um , um uncle , dama da..... " " ban ce ka yi min wani kame kame ba , Eh ko A'a za ka ce " gyada mishi kai kawai Junior ya yi dan ba zai iya bude baki ba wani cool murmushi Malik da Inaya su ka saki a tare , Malik har da wata yar karamar dariya ya na fadin " to ai faduwa ta zo dai'dai da zama , ta na dawowa za a daura auren " marairaice fuska Junior ya yi ya na fadin " Uncle , it's not sure ita ma ta na so na " Inaya ce ta amsa mishi da cewa " Kar ka damu , ba za mu fada mata an yi auren ba sai ka shawo kanta , kuma kai ma ka san halin Princess ta na da saukin kai , cikin sauki za ka shayo kanta " wata yar karamar dariya Junior ya yi ya na sunkuyar da kai Prince kuwa tsaki ya ja ya na fadin " Fine , da alamun hade min kai ku ke son yi yau " " Kai malam aure ne dai sai ka yi shi sai dai ka mutu " " yanzu Cutie ba za ki ce wani abu ba ? " ya fada ya na kallon Inaya daga mishi kafadu ta yi alamun ba ta sani ba bushewa da dariya Junior ya yi har da tapi hararrar shi Prince ya yi ya na fadin " yi min shiru kai kuma ko na shake ka wajen nan " " Ba ni na karto man ba , rataya a ka ba ni " ya fada ya na mikewa tsaye ya nufi lift da gudu ya na dariya da sauri Prince ya mike ya bi bayansa sai dai kafin ya riko sa har kofar lift din ta rufe wani tsaki ya ja kafin ya juya ya koma cikin parlourn ya na dawo da kallonsa kan Malik da Inaya kawai ya gan su rungume da juna ya na yi mata magana cikin rada " Daddy , da mutum fa a wajen " ya fada ya na dan zaro musu idanu hararrar Malik ya yi kafin ya ce " in ka ji haushi sai ka yi aure kai ma , My Cutie , tashi mu tafi na yi miki tausa " cike da shagwaba Inaya ta ce mishi " Baby ni gaskiya yunwa na ke ji " kiss ya yi mata a forehead ya na fadin " don't worry , tashi mu tafi " ba musu ta tashi shi ma ya mike tsaye ya riko hannunta su ka nufi lift su ka shiga, su ka bar Prince zaune a nan ya na kallon ikon Allah su na sane sarai da shi amma su ke zuba soyayyarsu ko kunyar sa ba su ji ( hmmmm in dai Malik ne ba ka ga komai ba WASHE GARI MASARAUTAR YEMEN Zaune Aleesherh ta ke cikin parlourn su , sanye da wata tsadadiyar gown blue ta daura wata farar Alkyaba da ga sama , ta yi mata kyau Over duk da ba ta yi make up ko kadan ba , amma fuskar ta na a daure kamar wadda uwarta da ubanta su ka rasu ta na zaune a haka Aleenah ta fito da ga cikin wardrobe sanye da kaya tak tak irin nata sai dai ita gown din ta white color ce , fuskarta babu yabo ba fallasa sai sha-aninta ta ke su na a haka Sayida Ahlame ta shigo ta na yi musu waya da murmushi a face din ta ta ce " ku tasso mu tafi su na fadar Al-Sayid " ba musu Aleesherh da Aleenah su ka mike su ka bi bayanta a cen kuma Fadar Al-Sayid zaune Junior ya ke cikin fadar ya na Sanye da wasu suit blue ma su mugun kyau kuma gaskiya sun kama shi sai jan sa da hira Al-Sayid ya ke su na a haka har Sayida Ahlame ta shigo rike da hannayan Aleenah da Aleesherh ta karaso cikin fadar ta zaunar da su saman chair din da ke fuskantar wadda Junior ke zaune , dama yau fadar ba mutane dayawa a ciki da ga Al-Sayid sai Sayida Fadwah da Sayida Ahlame sai kuma wasu biyun na hannun daman Al-Sayid wanda su ka kawo shawarar auren ma bayan ta zaunar da su Sayida Ahlame ta koma saman chair din ta da ke gefen damar kujerar ta Al-Sayid ta zauna , Sayida Fadwah kuma ta na a gefen hagu sai da ta zauna sannan Al-Sayid ya ce wa Junior " wadanan su ne yaran nawa , mai blue din riga ita ce babbar Aleesherh , dayar kuma sunanta Aleenah " wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " Amma ranka shi dade ba ni ne a ka aiko ya gan su ba " ya fada dan kar ma Al-Sayid ya yi mishi maganar ya zaba ya rasa amsar da zai ba shi cikin rudu Al-Sayid ya ce " kamar ya ? ba kai ne Yaron Malik Nawfel ba ? " girgiza mishi kai Junior ya yi ya na fadin " no , ni cousin din sa ne , amma wajen Malik na ke zaune , shi ya sa ma ya ce mu taho tare " " to ina dan uwan naka ya yi ? " " sorry uncle , ya na wani kira ne mai mahimanci amma yanzu zai shigo
Chapter 25 · 0% Book details