← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 61

Sashe 32

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

in ta koma Saudiya da sauri ta matso ta rungume ta dan ba ta da abun da za ta ce mata ta ji sanyi cikin zuciyata , ita kanta zafin rabuwarsu ta ke ji cikin zuciyarta sannu sannu har barci ya yi gaba da su a haka ____________________________________________________________ WASHE GARI Tsaye ta bakin kofar part din su Prince , ta na rike da tray din breakfast din su sai knocking ta ke amma ba su bude mata ba har ta fidda rai kawai ta ga an bude mata kofar sai ta ga Junior ne tsaye ya shirya cikin suit black color wani dan karamin murmushi ya sakin mata kafin ya ce " Sorry , ina saka kaya ne , barka da safya " " Good morning , na kawo muku breakfast ne " ta fada ta na mika musu tray din hannu ya kai karba ya na mata godiya ya juya ya koma cikin dakin a hankali ta biyo bayansa ta na fadin " ya jikinsa ? " " tun da har kin zo nan , me zai hana ki duba shi da kanki ? kin ga ni yanzu fita zan yi , na bar miki amanarsa , ki kula da shi please , amma sai kin yi hakuri wlh kamar baby ya ke in ba ya jin jikinsa " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " zan gwada " dariya shi ma ya yi kafin ya fice part din sai da ya fita sannan ta tako a hankali ta tsaya bakin gadon , ta kai hannu a hankali ta janye duvet din jikinsa, har yanzu ya na sanye da jacket din sa ta jiya wata doguwar mika ya yi ya na daga hannayansa, kafin ya juya, murya a disashe ya ce " Cutie , ki kyale ni barci na ke ji " wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon shi gaskiya ba karamin tafiya da ita ya yi ba , specially ma sunan Cutien da ya ce , ga wata sanyayar Muryarsa cen kassan makoshi , yanzu kenan haka kullum za ta dinga tashi da wannan zazzakar Muryarsa ? gaskiya ya kamata ta shawo kansa kafin a yi auren hannu ta kai a hankali ta dan bubuga shoulder din sa ta na fadin " wake up safiya ta yi " wani dan karamin kukan kura ya yi kafin ya zabura ya mike tsaye saman gadon lokaci guda har sai da ta firgita ta na ja da baya sai da ya dauki lokaci a tsaye kafin ya diro da ga saman gadon ya na kallon ta ya ce " coffee " da hannu ta nuna mishi table dan ba ta da bakin magana a hankali ya juya ya fara takawa ya nufi sofa , ya zauna ya janyo table din gabansa ya dauki mug din coffee ya fara sha ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara takawa ta fice part din ta bar shi nan ya na shan coffeen sai da ya shanye coffeen nan sannan ya tashi ya shiga toilet jim kadan ya fito sanye da bathrobe ya wuce dressing room ya shirya cikin suit white color , ya dauki wayoyinsa da laptop din sa ya fice , kai tsaye Daular ya baro baki daya MASARAUTAR SAUDIYA INAYA kamar dai kullum yau ma ta na a parlourn MALIKAT INAS , yau dai Malik ya raka Diya Fada Faaz da RIANNA kuma su na zaune a kassa saman carpet ta na rike da book ta na koya mishi karatu dan jiya ma sai da ta kira wata prof din ta koya mishi amma ta tsere ba ta ma ce m usu komai ba MALIKAT INAS kuma ta na zaune ta na kallon su su na a haka su ka jiyo Muryar Princess da karfi ta na kwallawa MALIKAT INAS kira a tare duk su ka juya su na kallon kofar shigowa parlourn Inaya har sai da ta ji zuciyarta ta buga shikenan jaraba ta zo kowa ya yi zugum ya na jiran shigowarta da sallama a bakinta ta shigo parlourn ta na fadin " I'm here " da sauri RIANNA ta mike ta nufe ta ta rungume ta tsam ta na dariya mikewa ita ma MALIKAT INAS ta yi ta nufo su ta rungume su dukka biyu dariya Princess ta yi ta na fadin " Ammie , momy , na yi kewar ku sosai " RIANNA ce ta amsa mata da cewa " Mu haka our Princess , mun yi kewar ki over " " to a sake ni " ta fada cikin shagwaba ba musu su ka sake ta , MALIKAT INAS ta riko hannunta ta na fadin " gaskiya wannan karan a part di na za ki zauna " har ta bude baki za ta yi magana ta jiyo Muryar Faaz ya na fadin " momy , ki kyale ta ki zo ki koya min ni " ya fada cike da shagwaba kare mishi kallo da kyau Princess ta yi kafin ta kwace hannunta da ga cikin na MALIKAT INAS ta karaso gabansa ta tsugunna ta na kallon shi da kyau sai da ta kare mishi kallo sannan ta ce wa RIANNA " momy , wanene wannan kuma ? " sai da ta yi wata yar karamar dariya sannan ta ce " kar ki damu zan fada miki da ga baya " " okay " ta fada a takaice kafin ta kai hannu ta murde mishi kunne ta na fadin " saurare ni da kyau , a nan gidan ni ce baby , in har na kama ka ka na yi wa momyna shirme da shagwaba , sai na sa an cire maka kai , ka ji ni ko ? " kuka ya sakin mata ya na fadin " sake min kunnena , momy ta sake min kunne " da karfi Princess ta ce " yi min shiru ko na mare ka a wajen nan ! " ta fada ta na matse gera alamun ba wassa ai ba shiri ya shanye kukansa ya na kallon ta " Princess , na san halinki ba ki da kirki , please kyale shi , me kuma ya yi miki ? " RIANNA ta fada ta na karasowa wajen su , ta kwace kunnen Faaz da ga cikin hannun Princess , da sauri Faaz ya mike ya fada jikinta ya na kuka mikewa tsaye Princess ta yi ta na fadin " ki kyale ni momy na koya mishi zama , tun da na zo yanzu , zan gyara wa kowa zaman sa a masarautar nan " " sannu to , ke kuma a wa , za ki wuce ciki ko sai na tashi gare ki ? " Inaya ta fada ta na tsare da ta idanu turo dan karamin bakinta ta yi ta na fadin " ni ai ba wajen ki na zo ba , ki kyale ni , kuma ina Daddyna ya ke , ina son ganin sa " " Daddynki ya na fada , ki yi hakuri zai zo har nan ya gan ki , yanzu shiga ki yi wanka " Fadin MALIKAT INAS gyada mata kai kawai ta yi kafin ta juya da sauri ta fice dan kar ma MALIKAT INAS ta taro ta dan ita a part din Daddynta za ta zauna sai da ta fita sannan Inaya ta ce " Allah ya shirya ki , wlh Ammie yarinyar nan sai kun dinga saka ta a addu'a , ni ban ma san ya zan yi da ita " dariya Malikat Inas ta yi kafin ta ce " kar ki damu , Junior zai yi maganin ta " dariya kawai Inaya ta yi ba tare da ta ce komai ba ita dai RIANNA sai rarrashin Faaz ta ke yi , sa va gani ta na mugun son shi tsakanin ta da Allah , da ta san wanene ainahin Faaz na san zuciyarta za ta karaya ba kadan ba sai da ya daina kukunsa sannan ya dago da ga jikinta ya na fadin " momy zan je toilet " da to kawai ta amsa mishi kafin ta sake shi ta koma ta zauna saman sofa shi kuma ya nufi corridor kai tsaye bedroom din sa ya shiga , ya turo kofar ya saka mata security wani dogon tsaki ya ja ya na fadin " kaiii wannan wace yar iska ce kuma ta shigo gidan ? , ba komai zan yi maganin ku daya bayan daya " ya na gama fadar haka ya karaso tsakiyar dakin ya tsaya ya lumshe idanunsa ya fara motsa lips din sa ya na wani karatu mara dadin ji ni kaina ban san abun da ya je fada ba a hankali na ga kawai ya kara tsawo yanayin jikinsa ya sauya baki daya ya koma mace ban gane ba ? ni fa abun ya fara ba ni tsoro, na gudu ko na tsaya ? in na gudu na za mu san ko wacece ba , in kuma na tsaya na san ba yi kwana ba yau dan ganin abun nan ya fara fin karfina amma bari na tsaya mu ga ) slowly na ga ta ware idanunta farare kal kamar madara kwayar cikinsu Blue mai kyau , ta na da dogon hanci kamar pencil da dan karamin bakinta gashinta baki kirin har tsakiyar bayanta , ta na sanye da wando da riga kamar dai wanda su je jikin Faaz da farko kafin ta komo haka , ta hadu gaskiya ba laifi cikakiyar balarabiya, a shekaru na san za ta yi 28 to 29 years haka wani dogon nunfashi ta ja kafin ta bude baki da wata zazzakar muryarta ta ce " Haba , har na ji dadi " ta na gama fadar haka ta shiga fadin " Queen , ina son magana da ke ? Queen ? " ta fada cikin sanyin murya a hankali na ga wutar dakin ta fara kunnuwa ta na mutuwa , a hankali ta tako ta nufi dressing mirror ta tsaya dai'dai lokacin duk lamps din dakin su ka mutu Mirror din ya fara wani haske kadan kawai na ga inuwar wata kujera kamar ta Royal chair haka , na ga sahun mutum zaune a kai amma na kassa gane macece ko namiji , amma da
Chapter 32 · 0% Book details