Sashe 46
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
THE BIGINING https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i _______________________________________________ _ PAID BOOK *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , 500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP [ FREE PAGE ___ 19 PRINCE bayan ya baro part din Malik da Inaya , nashi part din ya nufa , saman hanyarsa sai da ya tsaya ya daure gashin kansa a baya sannan , duk in da ya wuce sai dogarai sun dinga bin sa da ido kamar ba su san shi ba , ya na ganin su amma bai kula ba ya ci gaba da tafiyarsa a haka har ya iso part din sa da Sallama a bakinsa ya shigo parlourn , duk da ma sallamar ba ta fito fili sosai ba , kassa kassa ya yi ta a hankali ta dago kai ta na amsa mishi sallamarsa ta na ganin shi ta mike tsaye ta na fadin " Baby , me ya samu gashinka , kuma kayan jikinka ? " ta fada dan ta ga lokacin da ya bar part din , ba jallabiya ba ce a jikinsa ko sannu bai ce mata kawai ya nufi corridor ya shiga a hankali ta mike ta bi bayansa , har sai da ta ga bedroom din da ya shiga shiga bedroom din ta yi , ta na shirin yi mishi magana kawai ta ga ya cire jallabiyar jikinsa ya tilla saman gadon , dama short ne kadai a jikinsa , cak ta tsaya ta zuba mishi idanu ta na zaro su ta na tsaye a haka har ya juyo su ka yi ido hudu wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " lafiya ki ka biyo ni ? ko sai na fidda short din shi ma kin gani sannan za ki tafi ? " wani dan karamin tsaki ta ja ta na kauda kai gefe ta ce " to sai me in ka fidda , a ka ce maka ban san abun da ke ciki ba ne , ni kawai na zo na ga in ka na lafiya ne " ta na gama fadar haka ta juya za ta fita taku biyu kawai ya yi ya damko hannunta , ya janyo ta ya gama bayanta da bango , ya dafe bangon da hannayansa biyu ya saka ta tsakiya cikin wata siririyar murya ta ce mishi " yi a hankali mana , haka sai ka ji min ciwo " cikin tsare gida ya ce " me ki ka ce ? maimaita na ji " hararrar shi ta yi sama da kassa kafin ta ce " ni ba abun da na ce , sake ni na tafi " " babu in da za ki je , wai ke bakinki bai iya shiru ba ? a ka ce miki komai za ki iya fada kai tsaye ? " " to me na fada da ba dai'dai ba ? na ga a gaban mijina na ke " ta kai karshen ta na daga mishi gera ta dago hannu a hankali ta fara yi mishi tafiyar tsutsa da yatsarta saman kirjinsa har zuwa saman mararsa slowly ya lumshe idanunsa ya sake bude su saman face din ta , nan take duk sigar jikinsa ta mike tsaye wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya janye hannayansa ya nufi toilet ya shiga ya medo kofar ya rufe da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta bushe da dariya , ta yi tunanin dukan tsiya zai yi mata dan har wata bugawa zuciyarta ta ke , amma ta ga ba abun da ya yi mata har ta juya za ta fita wani abu ya ce mata kar ta tafi ai ko ta bi maganar zuciyarta ta koma ta Haye saman gadonsa ta zauna ta zubawa kofar toilet ido ta na jiran fitowarsa sai da ta yi wajen good 45 minutes zaune a haka sannan ya fito daure da towel a kugunshi , da wani dan karamin ya na goge gashinsa , sam bai lura da ita ba sai da ya karaso wajen dressing mirror sannan ya gan ta zaune ta zuba mishi ido kamar za ta cinye shi wani iska mai zafi ya furza da ga bakinsa ya na neman sanyaya zuciyarsa , ya san in ya biye mata gawarta ce kadai za ta bar Part din nan share ta kawai ya yi ya shafa lotion din sa , ya shiga dressing room , jim kadan ya fito sanye da wasu kananan kaya kamar kullum , wandon jeans da t-shirt , ya daure farin gashinsa a baya , da alamun ya fara dawowa dai'dai dan da ga kassa ya yi black kadan haka ya karaso wajen bedside drawer ya dauki wayoyinsa da sauri ta ce mishi " baby ina kuma za ka je ? yanzu fa ka dawo " ta fada a sanyaye ta na marairaice mishi fuska ba tare da ya kalle ta ba ya ce " zan je in da ba zan ga wannan face din taki ba " da sauri ta sauko da ga saman gadon ta sa hannayanta biyu ta tura shi har sai da ya yi baya kamar zai fadi a rude ya juyo ya na kallon ta ya ce " ba ki da hankali ? " " Eh , ba ni da hankali , wai me ka ke tunani ? kawai dan ina son ka za ka tsaya ka na fada min duk abun da ka ga dama , kar ka manta , da ga gidan sarauta na fito ni ma bare ka ce ina son ka dan dukiyarka , asali ma lokacin da na kamu da son ka ko sunanka ban sani ba bare na san da ga ina ka ke , ni fa matarka ce , ko ba ka so na ya kamata ka nuna min respect , in kai ba za ka iya fadawa momynka ba , ni zan fada mata a raba auren nan tun da har ba ka so na " ta fada ta na kuka hawaye na zubo mata bibiyu shi dai ya yi tsaye ya zuba mata ido sai balbale shi da fada ta ke ta na kuka sai da ya bari ta gama maganarta , sannan ya matso a hankali ya rungume ta ya na shafa bayan ta a hankali cikin sigar rarrashi neman kwatar kanta ta fara yi ta na fadin " ka kyale ni na tafi , ni gidan mu zan koma " a sanyaye ya ce mata " sorry , stop crying please " " why ba ka so na ? duk kokarin da na ke dan na faranta maka ba ka gani , ni gaskiya gidan mu zan koma " a hankali ya tako bakin gadon ya zauna , sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa , ya na kallon face din ta ya ce " ba za ki daina kukan nan ba ? na zata ke jaruma ce " " ai ko wani Jarumi ya na da rauni , ni kuma kai ne nawa raunin " ta fada ta na sa hannu ta fara goge hawayenta " shikenan , yanzu daina kukan nan " a hankali ta mike tsaye da sauri ya riko hannunta ya na fadin " ina za ki je ? " ba tare da ta juyo ba ta ce " zan je na wanke fuskata " sakin hannunta ya yi , ya zuba mata ido har ta fita bedroom din sai da ta fita sannan ya ja wani dan karamin tsaki , kassa kassa ya ce " ni dai na shiga uku " da ga haka ya mike tsaye ya dauki laptop din sa saman bedside drawer ya fito bedroom din IZZAT tsaye ta ke gaban dressing mirror din bedroom din ta , sai juyi ta ke yi gaban Queen kamar kullum inuwarta kawai ya fito cikin mirror din sai cen na ga ta koma ta zauna bakin gadon muryar Queen na jiyo ta na fadin " sai da na ce miki ki daina zuwa wajen nan , yanzu ga shi Prince ya gan ki " " momy , ni ma ban yi tunanin prince ya na wajen ba , na so na yi anfani da damar nan ne kawai na kashe Malik mu huta " da karfi Queen ta ce mata " no , ki daina shirme ki yi abun da na saka ki kawai , ko ma wani ki ke son kashewa Malikat Inas za ki fara kashewa " " why ? i think aikin zai fi sauki in Malik ya mutu ....... " katse ta Queen ta yi da fadin " Izzat , Izzat , idan har ba za ki iya abun da na ce miki ba zan dawo da ke na je na yi aikin da kaina " ta na gama fadar haka ta bace da ga cikin mirror din wata yar siririyar kara Izzat ta saki ta na fadin " ni gaskia na gaji da wannan aikin , abun haushin ma wannan sakarar matar da ta makale min " ai ko ta rufe bakinta ta jiyo Muryar Rianna ta na kiran Faaz wani dan siririn tsaki ta ja kafin ta mike tsaye ta fara takowa a hankali ta nufi kofar fita kafin ta iso wajen kofar ta koma Faaz , ya kai hannu a hankali ya bude kofar ya fito da dan gudu ya nufi Parlour ya na fadin " ga ni momy " ya na isowa parlourn idanunsa su ka sauka saman Princess konce gefen Rianna ta tada kai da laps din ta cak ya tsaya ya fara takawa a hankali sai da ya karaso gaban Rianna sannan ya saki kukan shagwaba ya na fadin " momy ta tashi da ga nan , wajena ne ta ke konce " wani dan karamin tsaki Princess ta ja kafin ta mike tsaye ta riko hannunshi ta na fadin " kai , momyna ce , ba taka ba , in ka ce za ka cika ni sai na sa an rataye min kai " da sauri Rianna ta mike ta na fadin " Princess , please ki kyale shi , yaro ne fa " " momy ki kyale ni na koya mishi zama , na ga alamun ya na neman ya wuce gona sa iri