Sashe 17
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
mu ba " " amma uncle ka na gani fa da kyair ma ya ke iya tashi " " na sani , kai dai kawai ka yi abun da na ce maka , ka kyale shi ya kula da kansa zai fi jin dadin hakan da wannan matsawar da mu ke yi mishi " " shikenan uncle , zan yi y...... " bai karashe maganarsa ba sakamakon ringing din da wayarsa ta yi kallon screen din wayar ya yi kafin ya saki wani dan karamin murmushi ya ce " uncle , prince ne ya ke kira " dan zaro idanu Malik ya yi kadan , cikin rudu ya ce mishi " Prince kuma ? dama ku na waya da shi ? " cikin rudu Junior ya ce mishi " ban gane ba uncle , ba ku waya ne da shi ? " " na ga wayar " Fadin Malik ya na mika mishi hannu ba musu Junior ya ba shi wayarsa daukar kiran Malik ya yi ya kai wayar a kunne ba tare da ya ce komai ba babu ko sallama Prince ya ce mishi " kai don Allah ina ka saka wayarka , tun dazu ina kiran ka sai yanzu za ka dauka ? " ya fada cikin tsare gida matse fuska Malik ya yi kamar ya na gabansa ya ce " ba shi ba ne , Ubanka ne ke magana " ________________