Sashe 33
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga jin sunan da budurwar nan ta fada na Queen tabbas mace ce a haka na jiyo Muryarta mara dadin ji ta na fadin " ba na ce ki daina min irin wannan kiran ba ? " wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta ce " sorry momy , to ba ke ce ba mutum na son magana da ke sai ya shiga wani rite , ni ban da wannan lokacin " " Izzat , ba na son shirme , kiran me ki ke min ? " ta fada da dan karfi " Queen , yarinyar Malik ta zo yau , ya ki ke so na yi da ita ? kuma yanayin ta ya nuna sam ba ta da kirki , kar ta gana min azaba , kuma kin sani ba na bari a taka ni " " No , ki kyale ta , ki bi tsarin mu kawai , yanzu ki tabbatar kin zubawa MALIKAT INAS poison ta mutu kafin a shiga watan azumi " " MALIKAT INAS kuma ? why zan kashe ta ? " wani dan karamin tsaki Queen ta ja kafin ta ce " MALIKAT AL'UMU ta riga da ta mutu MALIKAT INAS kadai ta yi wa Malik saura , in ta Mutu kin ga sai birkice , ba zai iya tantance abun da ke gabansa ba , a nan ne plan din mu na gaba zai fara ? " janyo chair Izzat ta yi ta zauna ta na kallon mirror din ta ce " Big bro kuma fa ? har yanzu fa ban jin kin ce zai shigo plan din ba , ga kuma Izyan da ke prison , matsalar ma yanzu Prison din sun meda ta cen karshen masarautar , da ta na cikin Daular da na fito da shi " " kar ki damu , Big bro din ku zai fito da shi idan ya zo " da sauri ta mike ta na fadin " momy, big bro zai zo ? how ? " wani dan karamin tsaki Queen ta ja kafin ta ce " Izzat , Izzat , ki maida hankali kan abun da ya kawo ki , in har ta dalilin ki plan di na ya baci ba abun da zai hana ni kashe ki duk da ni na haife ki " wani dogon tsaki Izzat ta je kafin ta koma ta zauna ta na kauda kai ta ce " an gama ya shugaba " komai Queen ba ta ce mata ba ta bace bat da ga cikin mirror din nan take duk lamps din dakin su ka kunnu wani dan karamin tsaki Izzat ta ja kafin ta mike tsaye ta na fadin " ni gaskia na gaji da wannan aikin , ga shi duk lokacin da na tambaye ta minene manufarta amma ba ta fada min " ta na gama fadar haka ta nufi toilet ta shiga QUEEN ! TO FA AIKI SABO , KO WACECE WANAN QUEEN , KENAN IZZAT DIYAR TA CE , TO MICECE MANUFARSU , NA JI TA CE A KASHE MALIKAT INAS, KENAN ENEMYN MALIK CE ? WANENE WANNAN IZYAN DIN DA TA CE YA NA PRISON ? GASKIYA TAMBAYOYIN SU NA DA YAWA , NAN GABA KADAN MUN SAMJ AMSA _______________________________________________ [ FREE PAGE ___ 14 AFTER SOME DAYS MASARAUTAR YEMEN yau dai ta kama ranar Friday , a yau a ka daura auren Prince da Aleesherh , dan farinciki sai da ta zuba ruwa a kassa ta sha , Prince kuwa bai ma san abun da ke faruwa ba dan tun safe da ya tafi wajen aikinsa har zuwa yanzu da na ke ba ku labarin , ba karamin taro su ka sha ma cikin Daular , dan musaman Al-Sayid sai da ya shirya walima , ya kuma ba da makudan kudade a yi sadaka , yau dai babbar yarinyarsa ta yi aure , auren ma a cikin familyn Malik din Saudiya , gaskiya ba karamin farinciki ya ke ba , amaryar kuma tun safe da Sayida Ahlame ta janyo ta part din ta ba wanda ya sake ganin ta , sai scrub ta ke mata a jiki ta na dura mata tsumi sai da Aleesherh ta dinga yi mata kuka ta kyale ta , Aleenah kuma tun lokacin da Sayida Ahlame ta dauke Aleesherh ta yi zaune ta aza kuka kamar baby MISALIN KARFE 9 NA DARE PRINCE a hankali ya turo kofar part din su ya shigo , duk da ba wani sake fuska ya ke ba amma yau da ga gani ya na cikin farinciki , contract din da ya dade ya na aiki a kai yau ya same shi , gaskiya yau ya na farinciki ba kadan ba , amma duk a gajiye ya ke dan ya sha aiki ya na shigowa part din ya ga wajen a gyare sai tashin qamshi ya ke , har sai da ya sauke ajiyar zuciya dan sanyin ba karamin sanyaya mishi zuciya ya yi ba a hankali ya karaso cikin dakin ya nufi bedside drawer ya ajiye wayarsa da laptop din sa , sannan ya nufi toilet ya shiga wanka ya yi sannan ya fito cikin bathrobe , ya nufi wardrobe ya shirya cikin kayan barcinsa white color , ya saki wannan smooth hair din nashi , sai tashin qamshi ya ke kai tsaye gadonsa ya nufa ya zauna sannan ya dauki wayarsa ya fara latsawa , bai wani nemi Junior ba dan ya san ya na cen yawon da ya saba dan wannan shi ne first time da ya zo Yemen , ya na son ya zagaye ta , Allah kadai ya san yaushe zai dawo ya na a haka ya ji a na yi mishi knocking ba tare da ya dago kai ba ya ba da izinin shigowa dan a tunanin sa diner ne maid su ka kawo mishi ya na a haka kawai ya jiyo wani dadaden qamshi ya kai mishi karo a hanci slowly ya dago kai ya kalli saitin da ya ke jiyo qamshin tsaye ta ke gaban center table ta sunkuya ta ajiye wani tray din fruits ta na sanye da wata gown white color mai mugun kyau da tsada , tsaya wa fada muku yadda rigar ta ke ma bata lokaci ne dan haka kowa ya yi anfani da brain din sa , ta daure gashin kanta a baya , babu wata kwalliya a face din ta amma ta yi kyau over a hankali ta mike ta dauki glass din milk da ke saman tray din , ta nufo shi kai a sunkuye tsare ta da ido ya yi babu ko kiftawa , kamar ya cinye ta dan ba karamin kyau ta yi mishi ba sai da ta zo gabansa sannan ta tsaya ta mika mishi glass din hannunta ba tare da ta ce komai ba a hankali ya kai hannu ya karbi glass din ya na yi mata godiya ya na karba ta dawo gefensa ta zauna kanta a sunkuye shan Milk din ya fara yi cikin konciyar hankali ba wanda ya ce ma wani ufan har sai da ya shanye milk din ya ajiye glass din saman bedside drawer wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta bude baki a hankali murya a sanyaye ta ce " ina son na roki wata Alfarma a wajen ka idan ba damuwa " " yeah , in har za ni iya za na yi miki " ya fada ya na latsa wayarsa wasu yawu ta hadiye kafin ta ce " ban san ya mutane za su kalli hakan ba kuma ban damu ba , Aleenah yar uwata ce kuma friend di ta , ita kadai gare ni a duniya wadda zan iya fadawa abun da ke damu na kuma ta saurare ni , ina rokon ka , ka yi hakuri ka bari ta taho tare da mu a Saudiya , ba na tunanin rayuwata ba tare da ita ba , don Allah " " okay , in har Al-Sayid ba shi da matsala da hakan , sai ku tafi ke da ita " ya fada ya na ci gaba da latsa wayarsa wata yar karamar kara ta saki kafin ta zagayo da hannayanta a kugunsa ta rungume shi ta na fadin " na gode , na gode " ba shiri ya saki wayarsa bawan Allah dama sanyi ya ke ji ta zo ta na neman tada tsohon tsumi sai da ya saisaita nitsuwarsa sannan ya ce " amma ina da sharadi " slowly ta dago da ga jikinsa ta na kallon shi cike da rudu ta ce " sharadi ? wane sharadi ? " slowly ya matso da face din ta dab da face din ta , har su na iya jiyo nunfashin juna murya kassa kassa ya ce mata " sai kin fada min wanene wannan wanda ki ka kamu son shi , ina so na san wanene wanda ke cikin zuciyar wadda ke matsayin matata " wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " ba ga shi nan a gabana ba " baki sake ya ke kallon ta kenan shi ne wanda ta ke so cikin nitsuwa ta ce mishi " me ka ke tunani ? tun ranar da ka taro ni cikin kasuwa zuciyata ta kamu da son ka , na so na cire abun da ke cikin zuciyata amma na kassa , da taimakon ka ne na ganin walkiya cikin duhu , da a ce za ka ga kanka a yadda na ke ganin ka da za ka fahimci ina ganin haskenka fiye da haske rana mai matukar kyau , a kullum dare ko rana tunanin ka kawai na ke , a kowane lokaci mararin ka na ke yi , duk wani motsi da bugawar zuciyata da kaunar ka ya ke harbawa , kai ne na ke fara gani a farkon mafarkina kuma kai ne tunani na farko da ke zuwa min a duk lokacin da na ke cikin nitsuwa , kai ne farincikin da na jima ina jira Prince " shi dai bawan Allah ya tsaya ya zuba mata ido sai zuba ta ke mishi ya na kallon cikin idanunta ba karya ya na ganin wannan soyayyar da ta je magana a kai sai da ta gama