Sashe 4
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GASKIYA SAI NA JE NA SHA MALTINA , Cikin rudu Diya ya ce mata " Mama , ya kamata mu koma mu fadawa Malik , ya sa a fara cigiyar Nayab , in har ya fadi hannun mugayen mutane to tabbas mu na cikin tsaka mai wuya " gyada mishi kai kawai ta yi kafin su juya , a tare su ka bar wajen da gudu a tare kai tsaye motarsa su ka koma , su ka shiga su ka bar wajen da gudu kai tsaye Daular Saudiya su ka koma , ko da su ka koma part din Malik su ka wuce a nan floor na uku su ka tardo shi zaune saman Royal chair din sa , ya na rike da hannayansa , kamar dai jiran su ya ke yi da sallama a bakinsu su ka shigo parlourn , a hankali ya motsa lips din sa ya na amsa musu sallamar da sauri Diya ya ce mishi " Malik , akwai matsala , Bab...... " cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " Get out ! " ya fada a sanyaye da sauri Mama ta ce " don Allah ka tsaya ka saurari abun da za mu fada maka , wlh Nayab bai mutu ba , kuma da Aswad a jikinsa , in a ka je wani makiyinka na kusa ya tsintse shi wlh akwai matsala " a hankali ya mike tsaye , ya riko hannayansa a baya ya ce " shikenan , ku je neman sa , amma ba da yawuna ba , da hannuna na dauke shi kuma ban ji rai a tare da shi ba , mama kin san halin yarinyarki , na riga da na ce mata Twins ne , yanzu in ta ji labarin babu na ukun ya za ta ji ? ke ma kin san da ga ni har ku ba za ku ji da sauki ba , shi ya sa na binne wannan maganar , don Allah na roke ku ku bar maganar nan , tun wani bai jiyo ba , please " " amma Nayab ya na raye , Ya ke ko so mu yi da hakan ? " Fadin Diya " za ka iya tafiya neman sa in ka na so , amma ni dai na san Nayab ya koma ga mahallacinsa , kuma cikinku wani ya yi wa Cutie wannan maganar ban yahe masa ba " ya na gama fadar haka ya juya ya nufi corridor ya shige da kallo su ka raka shi har sai da ya shiga , sannan mama ta juya ta kalli Diya ga na marairaice fuska tun kafin ta ce wani abu ya riga ta cewa " ya ce za mu iya tafiya neman sa , dan haka ni zan je neman sa in shi ba zai iya ba , mu tafi mam " ya fada ya na juyawa zai bar wajen ba musu mama ta bi bayansa su ka bar part din baki daya _______________________________________________ AFTER SOME YEARS UNITED STATE OF AMERICA ( U.S.A ) WASHINGTON DISTRICT OF COLOMBIA a hankali ta ke sauko stair din gidan , ta na sanye da wata gown pink color mai wani belt fari da ga tsakiya , rigar mai kananan hannu ce , amma gaskiya ta hadu , babu veil a kanta , ta saki wani smooth hair baki kirin , ya zubo mata a shoulder har tsakiyar baya kai da ga gani ka san ba kananan kudi a ke kashe mishi ba budurwar kyakyawa ce gaskiya kai ka rantse sarauniyar kyau ce , a shekaru za ta kai 30 haka , amma yanayin jikinta ka ce yar 18 ce , breast din ta ya na tsatsaye kamar an hira balan-balan , shape din ta kamar na coca cola abun dai Masha Allah , fara ce kal kamar ka taba jini ya fito , jinin larabawa , tak tak Malik a jinsin mata har shape din lips din shi kamar heart , da Hazel eyes din sa , ba dan kar ku ce na yi karya ba da sai na ce wannan har ta fi Malik kyau , bare kuma rainon Ice cream da Madara , ga kuma yanayin garin US kai ka san abun sai Masha Allah kawai a haka ta ke sauko stair din cike da nitsuwa , kai tsaye parlourn gidan ta nufa ta zauna saman sofa , ta kai hannu saman center table ta dauki wayarta , ta fara latsawa ta yi wajen two minutes zaune a haka kafin ta juya ta kalli kofar kitchen , ta na turo dan bakin nan nata kamar pen , cike da shagwaba ta fara fadin " Cutie ! ! , please yunwa na ke ji , tun dazu kin kyale ni a nan , sai yunwa ta kashe ni sannan ki rasa mai yi miki tausa " yanayin da ta yi maganar kai ka ce yar shekara 8 ce ta yi maganar shiru na ji ba a amsa mata ba , kukan shagwaba ta saki ta na fadin " Cutie ! Cutie ! yunwa na ke ji pleaseeeee " ta na gama rufe bakinta ba ga Inaya ta fito da ga kitchen , ta na rike da plate a hannu guda , da wani dan bowl a dayan gaskiya US ta zauna mata sosai , ita da Princess ka ce yaya da kanwa ne ba diya da uwa ba , dama hakan na faruwa in mace ta haifu da karancin shekaru , specially in ta haifi mace dan ta fi namiji saurin girma , kuma lokacin da ta haife su ba ta wuce 15 years na dole a yi musu kallon yaya da kanwa yanayin jikinta tak irin na Princess , ita ba rama ba kuma ita ba kiba ba , dai-dai tsakiya , ta yi wani uban Haske masha Allah , in ba kare mata kallo da kyau ba ka yi ba za ka iya karance yanayin shekarunta ta na sanye da wata Abaya white color mai kyau , sai wani dan veil da ta yafa a kanta ta na taku cike da nitsuwa a haka har ta karaso cikin parlourn , ta ajiye wa Princess plate din hannunta , kafin ta kai hannu ta dunguri kanta ta na fadin " ki mutu da yunwa tun da ke ba za ki iya shiga ki girka wa kanki abinci ba " " ni da na ke da Cutie na san ba za ta taba bari na mutu da yunwa ba , amma Cutie kin manta da Juice , ko shi ne cikin bowl din " ta fada ta na neman karbe bowl din dayan hannunta da sauri Inaya ta janye Bowl din ta na fadin " ke Princess ? kin san Allah ki fita da ga idona , in shirme ki ke so na fi ki iya wa , je ki tambayi Daddynki , dan haka ki bi ni a hankali ko kuma gidan ya mana kadan " wata yar karamar dariya Princess ta yi kafin ta ce " momy ni wassa na ke miki fa " ta fada cikin sanyin murya dan ta san halin mahaifiyarta , yanzu za su fara rigima cikin gidan sai Malik ya shiga tsakaninsu wani dan karamin murmushi Inaya ta yi kafin ta juya ta nufi stair ta Haye Ta na hawa Princess ta kai hannu ta dauki spoon ta fara cin abincin , Inaya kuma kai tsaye bedroom din su ta koma , da sallama a bakinta ta shigo bedroom din babu kowa a ciki , kawai sai ta nufi bedside drawer ta ajiye bowl din hannunta kafin ta mike Dai-dai lokacin da ya bude kofar toilet ya fito ya na daure da towel a kugunsa , da alamun wanka ya yi wani cool murmushi ta saki ta na kallon shi , ya na nan yadda ya ke sam bai sauya ba , har wannan murdaden jiki nasa , ni ganin na yi kamar ya ma kara murdewa , wannan smooth hair din nasa ya na jike da alamun wanke sa ya yi daga mata gera guda ya yi ya na fadin " lafiya ki ke min irin wannan kallon ? " ya fada murya cen kassan makoshi har yanzu dai na miskilancin su na nan a hankali ta fara takowa , sai da ta zo dab da shi sannan ta ce " me ya sa za ka cire gashinka ? dama kullum Princess na cewa ta fi ka gashi , yanzu ga shi kuma ka cire shi " murmushi mai dan sauti ya yi ba tare da ya ce mata komai ba , ya juya ta gefe ya nufi dressing mirror ya janyo chair ya zauna , ya kai hannu ya bude box , ya na shirin fiddo air dryer kawai ya ga hannunta , ta riga shi dauka cike da so ta ce mishi " bari na yi maka " ba musu ya janye hannunsa , ya zuba mata ido ta cikin mirror cikin nitsuwa ta fara busar mishi gashin sa , sai da ta kammala ta sa hairbrush , ta gyara mishi shi , ta sa pin ta nade shi a baya bayan ta kammala ta sauko ta manna mishi kiss saman shoulder ta na fadin " ka san wani abu ? a kullum ganin na ke kara kyau ka ke yi babyna " murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya kai hannu ya zagayo da ita gabansa ya zaunar da ita saman laps din sa a hankali ya kai hannu ya zare veil din ta , ya ajiye saman dressing mirror kawai ya tsaya ya zuba mata ido kamar bakuwarsa daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " ya ? lafiya ka na min irin wannan kallon ? sai ka ce za ka cinye ni " girgiza mata kai ya yi ya na murmushi ya ce " ya kamata mu tafi Honey Moon my Cutie " wata yar karamar dariya ta yi ta na fadin " kai baby , wace Honey Moon kuma , mu ai yanzu mun tsuha sai dai mu tura Prince da Princess honey moon , ba dai mu je ba " " and so what dan mun tsufa ? kin taba ganin in da soyayya