← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 61

Sashe 36

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hankali Malik ya mike tsaye ya karaso gabansu ya tsaya na dan lokaci sannan ya juya ya kalli Diya ya ce " Diya ka sa a fitar da one hundred million a yi wa mutanan gari sadaka " da sauri Diya ya ce " ina ga sai dai two hundred million " wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " Aleesherh , wannan shi ne mahaifinki , ina fatan za ki girmama shi tamkar shi ya haife ki " gyada mata kai Aleesherh ta yi a hankali ba tare da ta ce komai , ta na so ta dago kai ta kalle shi amma ta na kunya ta ji Muryarsa tak irin ta Prince ta na so ta ga in ya na kama da shi kamar yadda Muryarsu ta yi kama ta na a haka ta jiyo Muryar Malik ya na fadin " Cutie , ki kai ta part din Ammie ta huta mana na ga alamun kamar ta gaji " " na sani , kawai na kawo ta ne ku gan ta kafin na kai ta part din MALIKAT INAS " " shikenan , za ku iya tafiya " ya fada ya na komawa ya zauna ba musu ta ja Aleesherh su ka koma cikin lift kafin kofar ta rufe ta yi sauri ta dago kai ta saci kallon Malik , kuma gaskiya ya na kama Tak da Prince har Hazel eyes din su , ba dan shekarunsa da sai a yi musu kallon Twins da ga haka su ka baro part din su ka nufi part din MALIKAT INAS lokacin da Aleenah ta shiga part din duk sun dauka ita ce matar Prince sai tambayar ta su ke in ta zo lafiya , ya sunanta da sauran su sai da Junior ya ce musu ba ita ba ce , matar Prince ta na tare da Inaya sun tafi wajen Malik , wannan Twins din ta ce duk da hakan ba su hakura ba sai tarerayar ta su ke Tesnim har da fadin ta yi wa Autanta kamu , ita dai Aleenah ga na zaune ta na kallon ikon Allah a haka har Inaya ta shigo parlourn ta na sallama ta na rike da hannun Aleesherh nan ma duk su ka ga tarerayar Aleesherh har gift MALIKAT INAS ta ba ta , wasu bracelet na Gold da duwatsun diamond a sama ta saka mata su a hannu da kanta sai da kyair Inaya ta kwace ta da ga hannunsu sannan ta ce wa Aleenah su tashi su tafi ba musu ta taso ta na sunkuyar da kai ta bi bayan Inaya su ka shiga corridor din cikin dayan bedroom ta kai su sannan ta ce " ku shiga ku yi wanka , za sa a kawo kayanku a nan , zan je na shirya muku abinci na San ku na jin yunwa " ta na gama fadar haka ba ta jira amsar su ba ta juya ta fice sai da ta fita sannan Su ka fara bin dakin da kallo Aleesherh ta karaso bakin gadon ta zauna ta na kallon bracelet din da MALIKAT INAS ta saka mata , gaskiya sun yi kyau over karasowa ita ma Aleenah ta yi ta zauna gefenta ta na fadin " gaskiya sun yi kyau sosai " murmushi mai dan sauti Aleesherh ta yi kafin ta fiddo gudan na hannun hagunta ta mika mata ta na fadin " karbi ki saka ke ma " dan zaro idanu Aleenah ta yi ta na girgiza mata kai ta ce " no , ke a ka bawa , ya ki ke tunanin kakarsa za ta ce in ta ga bracelet din a hannuna ? please kar ki janyo mana magana , na ga mutanan wajen duk su na kirki , ya kamata mu yi komai cikin tunani " " na sani , kuma ba za ta ji zafi ba , please karbi ki saka " girgiza mata kai Aleenah ta yi kafin ta tashi ta nufi kofar da ta ke tunanin toilet ce ta na shiga ko wasu maids su ka shigo janye da trolley din su ta nufi dressing room su ka gyara musu kayan cikin closet su ka fito su na tambayar Aleesherh in ta na bukatar wani abu girgiza musu kai kawai ta yi ta na murmushi haka ta zauna jiran Aleenah sai da ta yi wankanta da kyau sannan ta fito , ita ma Aleesherh ta tashi ta shiga toilet din ta yi wanka , sannan ta fito ta shiga dressing room ta shirya cikin wata Abaya white color ta fito , ta dauki wayarta ta haye saman gadon ta fara latsawa , ita kuwa Aleenah tuni barci ya yi gaba da ita AFTER SOME HOURS a takaice dai inin ranar Aleesherh da Aleenah duk cikin bedroom din su ka share shi , sai dai Inaya ta shigo ta na tambayar su in su na bukatar wani abu , ko kuma ta kawo abinci da kanta Prince kuwa, kamar yadda ya yi alkawari 10 na dare ya shigo cikin garin , ba karamin fada ya sha hannun Malik sai da Inaya ta kwace shi , da ga haka kuma ya koma part din da Malik ya shirya mishi MISALIN KARFE 11 NA DARE a hankali ya ke fitowa da ga cikin corridor din part din sa , ya na sanye da wasu pajama white color , ya daura gashin kansa a baya , ya na rike da waya kamar kullum sai aikin latsawa ya ke a haka har ya karaso cikin parlourn ya zauna ya ci gaba da aikinsa ya na a haka Inaya ta shigo parlourn ta na sallama ita kadai ba tare da ya dago kansa ba ya amsa sallamar karasowa gefensa ta yi ta zauna , da murmushi a face din ta ce mishi " sannu agogo Sarkin aiki , kai kullum ka na rike da waya ? ba ka gajiya ? " " to Cutie in ban yi aiki ba me za ni yi ? kuma na ga ba na takurawa kowa " " haka ne , amma yanzu ya kamata ka rage tun da ba kai kadai ba ne , ya kamata ita ma ka ba ta ko da rabin lokacinka ne " " wa kenan ? " hannu ta kai ta kwace wayarsa ta na matse fuska ta ce " ba na son shirme ka san sarai a kan wa na ke magana " marairaice fuska ya yi ya na fadin " i'm serious momy , ban san a kan me ki ke magana ba " " a kan matarka na ke magana , ka san Allah Prince ? kar ka ce za ka yi wannan wassan da ni dan ni na haife ka , dan haka tashi ka je ka dauko matarka ta dawo part din ka " ta fada ta na matse gera alamun ba wassa cikin nitsuwa ya kai hannu ya karbi wayarsa sannan ya ce mata " me ya sa ba ki taho da ita ba ? " " ce min ta yi wai su wajen su mijin da kansa ya ke tafiya dauko matarsa, dan haka tashi mu tafi " wani dan karamin tsaki ya yi kafin ya ce " Cutie , wai............. " katse shi ta yi da cewa " so ka ke sai Daddynka ya shiga maganar ? kai ma ka sani ba za ka ji dadi ba in har ya sa baki " " shikenan let's go " ya fada ya na mikewa tsaye wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta mike tsaye ita ma ta riko hannunsa su ka baro part din a tare kai tsaye part din MALIKAT INAS su ka nufa da sallama su ka shigo part din , babu kowa sai RIANNA da MALIKAT INAS sai da su ka shigo cikin parlourn sannan ta saki hannunsa ta ce ya jira ta ba musu ya tsaya sai tsuke fuska ya ke , MALIKAT INAS da RIANNA su na yi mishi dariya kassa kassa dan da ga gani bai ji dadin abun da a ka yi mishi ba ya na a haka tsaye Inaya ta fito rike da hannun Aleenah , ita a tunaninta Aleesherh ce dan ta ga kaya iri daya su ke sanye da kuma da ta shiga ta tarda dayar konce , kawai sai ta yi tunanin ko Aleenah ce barci ya dauke sai da ta karaso wajen shi sannan ta mika mishi hannunta ta ce " za ku iya tafiya " shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na kallon Aleenah da ga kassa har sama sannan ya kalli Inaya ya ce " to ai wannan Twins din ta ce " cikin rudu Inaya ta kalli Aleenah irin kallon nan na rudu sai a lokacin Aleenah ta samu ta yi magana ta ce " shi ne na ke son na fada muku amma ba ku saurare ni ba , Aleesherh ce ke konce " wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta saki hannunta ta ce " to ni ta ya zan sani , duk ku na kama " " no , ba su kama , wacen ta fi wannan manyan idanu " Fadin Prince kare mishi kallo da kyau Inaya ta yi , kenan har ma ya san manyan idanu ne da ita ? " shikenan , Aleenah , je ki kira ta please " Inaya ta fada ba musu Aleenah ta juya ta koma bedroom din su saman gadon ta Haye ta na fadin " Alee , tashi mijinki ya zo neman ki " murya a sanyaye ta ce " Aleen , cikina ke yi min ciwo wlh , ba zan iya tashi ba " " don Allah tashi , kin ga in ku ka tafi cen shi zai kula da ke , yanzu dai tashi " wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta mike zaune ta sauko da kafafunta kassa sannan ta sauko da ga saman gadon ta fara takawa a hankali kanta na sunkuye riko hannunta Aleenah ta yi su ka fito bedroom din tun da su ka fito corridor din Prince ya tsare ta da ido , da ga ganin tafiyarta ya san ba lafiya ba a haka har
Chapter 36 · 0% Book details