← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 61

Sashe 37

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

su ka karaso wajen sannan Aleenah ta saki hannunta ta na cewa Inaya " ga ta momy " murmushi kawai Inaya ta yi kafin ta riko hannunta ta mikawa Prince ba musu ya riko hannunta ya juya ba tare da ya ce wa kowa komai ba ya fice parlourn sai da ya fita sannan RIANNA ta bushe da dariya ta na fadin " baby , gaskiya ba ku yi wa Prince adalci ba " dariya kawai Inaya ta yi kafin ta ce wa Aleenah " koma ki konta , sai da safe " gyada mata kai kawai Ta yi kafin ta juya ta koma cikin bedroom din su , Inaya kuma ta fice ta tafi wajen babynta bangaran su Prince kuma , kai tsaye part din su su ka nufa , su na tafe ta na matse mishi hannu , ya na ji amma bai tanka mata ba ko da su ka shiga part su ya wuce da ita bedroom din ta su na shiga ya saki hannunta ya juyo su na fuskantar juna ya ce mata " what's wrong with you ? " kamar za ta yi kuka ta ce mishi " Cikina ke yi min ciwo " " wani abu ki ka ci wanda bai da kyau ? " girgiza mishi kai ta yi a hankali slowly ya matso dab da ita , ya kai hannu saman cikinta dam ta ji zuciyarta ta buga har sai da ta dago kai ta kalle shi a hankali ya fara shafa mata cikinta , a sanyaye ya ce mata " don't worry zai daina , yanzu shiga ki yi wanka sai ki konta " ya na gama fadar haka ya janye hannunsa ya juya zai fita da sauri ta riko hannunshi ta na fadin " please kar ka tafi , ban iya barci ni kadai ba " ta fada ta na marairaice mishi fuska a hankali ya kwace hannunsa sannan ya tako a hankali ya zauna bakin gadonta, ya fara latsa wayarsa ta na ganin ya zauna ta saki wani dan karamin murmushi ta taka a hankali ta shiga toilet dan ta yi wanka ________________
Chapter 37 · 0% Book details