Sashe 26
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" da to kawai Al-Sayid ya amsa mishi ya na kallon kofar fadar ya na jiran ya ga wanene zai shigo dan shi fa ko Malik din a Tv kawai ya taba ganin sa bare yaronsa da bayan familynsa ba wanda ya san sunansa sun yi wajen two minutes zaune a haka ba wanda ya ce wa kowa ufan , Har Al-Sayid ya bude baki zai yi magana su ka jiyo Muryar Prince ya na sallama cike da nitsuwa dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga har sai da ta wani lumshe idanu amma sam ba ta yi kokarin dago kai ba bare ta ga in da gaske shi ne ko ba shi ba ne cikin rudu Al-Sayid ya kare mishi kallo dan ya gane fuskarsa sarai , amma bai kawo komai a ransa ba kawai ya yi tunanin ko wani littafin ya zo nema a libraryn masarautar ya na sanye da wasu suit white color shi kuma , ma su bala'in kyau kamar dai irin na Junior sai da ya karaso wajen Chair din da Junior ke zaune ya tsaya ya na fadin " ina mika gaisuwata ga shugaban wannan kassar mai Albarka " da murmushi a face din sa Al-Sayid ya ce " ina amsawa , yau kuma me ya kawo Prince wannan fadar ? ko dai wani littafin ka zo nema ? " da sauri Junior ya kalli Prince ya na zaro idanu , ya na tambayar kansa ya a ka yi Al-Sayid ya san sunansa Prince kenan dama ya taba zuwa fadar Yemen girgiza mishi kai Prince ya yi kafin ya ce " zan so na fara gabatar da kaina , sunana Prince Nayel Hicam Bin Jaabar , d'a ga Malik Nawfel Hicham bin Jaabar , zan so na mika sakon godiyata kai tsaye ga Al-Sayid da wannan gayatar " ya fada cike da izza baki sake Al-Sayid da sauran mutanan fadarsa biyu ke kallon Prince , kenan dama ya zo fadar ba su da labari Junior kuma sai tabe baki ya ke jin kalaman Prince ya na fadin " sannu Prince , izzar taka a nan ma sai ka nuna ta ? zan yi maganin ka in ka koma " cike da kula Al-Sayid ya ce mishi ya zauna ba musu Prince ya zauna gefen Junior ita dai Aleesherh ta na jin duk abun da ke faruwa amma ta kassa dago kai , ta na gudun ta dago kai ta ga ba abun da ta yi zato ba ne ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Aleenah ta na bubuga cinyarta ta na fadin " Alee , Daddy na mike magana " a razane ta dago kai dan ita sam ba ta ji abun da ya ke cewa ba ta na dagowa ko idanunta su ka sauka saman Prince da ke zaune ya tsare ta da ido shi ma tun zamansa ya ke jiran ta dago kai amma ta ki dama Aleenah karya ta ke mata dan ta lura da irin kallon da Prince ke yi wa Aleesherh , shi ya sa ta ce ta dago kai su ga juna cikin nitsuwa Al-Sayid ya ce wa Prince " ya kamata ku tafi part din da a ka gyara muku ku huta , zan sa a kai muku abinci " Junior ya amsa mishi da cewa " a'a Uncle , taf....... " bai karasa maganarsa ba Prince ya katse shi da cewa " mun gode ranka shi dade , amma mun riga da mun kama bedrooms a hotel , so a cen za mu sauka " wannan karan Sayida Ahlame ce ta karbi zancen da cewa " a'a , gaskiya ba za ku kwana a hotel ba , mun riga da mun shirya muku part , dan haka sai ku tashi ku tafi , Aleesherh ko za ki kai su part din ? " gyada mata kai Aleesherh ta yi kafin ta mike tsaye a hankali ta na fadin " bismillah " ba musu Junior da Prince su ka mike su ka yi wa Al-Sayid sallama sannan su ka bi bayanta su ka baro fadar sai da su ka yi dan nisa da Fadar sannan Junior ya cewa Prince " lafiya ka ce za mu zauna ? Daddy fa ya ce da mun zo mu koma , ni gaskiya ba Niyyar zama " wani dan karamin tsaki Prince ya ja kafin ya ce " kai don Allah yi min shiru , ba duk kai ne ka janyo min ba , da ba ka bawa Daddy wayar a lokacin da na kira ka ba da ba zai ce na dawo ba , dan haka malam sai dai ka yi hakuri har na yi sign din contract din da ya kawo ni Yemen , in ya kira ka ce mishi Al-Sayid ne ya matsa mu zauna " " no , ni gaskiya ba zan yi wannan karyar ba , ka san halin Daddy " " Junior ka san Allah na fi ka duk shirmen da ka ke ji , in har na rasa wannan contract a karo na biyu saboda kai , Allah sai na hana ka samun sukuni a rayuwarka " bushewa da dariya Junior ya yi har da tapi , kafin ya ce " ba dan Daddy ya yi maka auren dole ba za ka sauke haushin sama na , da ga na fadi gaskiya " wani dan karamin tsaki Prince ya ja kafin ya juya ya na kallon gabansa nan ya tuno ashe ta na a wajen shi ko bai san duk maganarsu ta jiyo ta , kuma sun yi mugun tuno mata ita da Aleenah , haka su ke wannan jayayar in ta ce za ta yi wani abu sai da su karaso bakin kofar part din ta sa hannu ta tura kofar sannan ta koma gefe ta tsaya kai a sunkuye ta ce musu " bismillah " godiya Junior ya yi mata kafin ya shiga part din kai tsaye , shi kuwa Prince ya tsaya ya zuba mata ido ganin har yanzu ya na tsaye a gabanta ya sa ta dago kai slowly , kai tsaye idanunta cikin nashi su ka sauka kauda kai ta yi a hankali kafin ta juya za ta bar wajen cikin nitsuwa ya taro ta da fadin " wa ya ba ki izinin tafiya ? " ba tare da ta juyo ba ta ce " na ga wanda ya ba ni umarnin kawo ku wajen nan ba ya nan bare ya ce min kar na tafi " " All right , za ki iya tafiya za mu hadu a gaba " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya shiga cikin part din ta na jin ya fara takawa ita ma ta ci gaba da tafiyarta , kai tsaye part din su ta koma ko da ta shiga ta tardo Aleenah zaune bakin gadonsu ba ta ce mata komai ba ta fiddo wayarta , ta sa music ta kai karar karshe sannan ta tilla wayar saman gadon ta kai hannu ta cire Alkyabarta ta tilla gefen wayar cikin rudu Aleenah ta tsaya ta na kallon ta ta na jiran ta ga abun da za ta yi ba zato ba tsanmani kawai ta ga Aleesherh ta fara rawa har da kama sautin wakar ta na girgije wa da kyau ita dai Aleenah ta yi zaune ta na kallon ikon God su na a haka Sayida Ahlame ta shigo wajen cak ta tsaya ta na kallon Aleesherh sai rawarta ta ke cikin konciyar hankali ta na murmushi cikin rudu ta karaso wajen ta na fadin " Alee , lafiya ki ke rawa haka ? " Aleenah ce ta ba ta amsa da cewa " momy , saurayin da ta ce muku ta na son shi , to shi ne Prince " dan zaro idanu Sayida Ahlame ta yi ta na kallon Aleesherh sai rawa ta ke wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta riko hannunta ta na fadin " rawar ta isa haka madam , zo zauna na yi miki magana " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " momy i'm so happy , i can't imagine , don Allah ko mafarki na ke kar ku tashe ni " hannu Sayida Ahlame ta daga za ta marin ta ta na fadin " ni zan tashe ki to yar rainin hankali kawai " dariya kawai Aleesherh ta yi kafin ta zauna bakin gadon ta na kallon Sayida Ahlame sai da ta zauna sannan Sayida Ahlame ta ce mata " yanzu an kawo miki scrub ki yi kafin ki shiga wanka , kuma Ammie ta ce ta turo miki perfume da wasu abubuwa ban San ko minene ba dan ba ta fada min ba , Al-Sayid ya ce next Friday za a yi auren in da rai da lafiya " ta na gama fadar haka ta juya ta fice hannu Aleesherh ta kai ta boye fuskarta ta na murmushi kafin ta yi baya ta konta saman gadon zuciyarta cike da farinciki kamar ta tashi sama ta ke ji Aleenah dai duk ta yi sanyi , sai latsa wayarta ta ke cikin konciyar hankali , ta ma rasa me ke yi mata dadi a duniyar nan ba ki daya , kuma ta kasa tantance abun da ke damun ta , ko dai kishi ta ke ? TO FA ALEENAH ZA TA FARA KISHI DA ALEESHERH KO YA ? ________________